Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU), reshen Jami’ar Jihar Kaduna (KASU), ta fara yajin aikin gargaɗi na tsawon makonni biyu, lamarin da ya haifar da dakatar da harkokin karatu a jami’ar. Ƙungiyar ta ce ta ɗauki matakin ne domin neman cikakken aiwatar da buƙatunta da suka shafi jin daɗin malamai da sauran batutuwan da suka daɗe ba a warware su ba.
ASUU-KASU ta sanar da fara yajin aikin ne bayan wani taro da jami’ai da mambobin ƙungiyar suka gudanar a ranar Alhamis, inda suka tattauna kan matsalolin da ke tsakaninsu da jami’ar da gwamnatin jihar.
Daga cikin batutuwan da ƙungiyar ta ce har yanzu ba a warware su ba akwai yarjejeniyar ƙarin albashin kashi 25 zuwa 35, batun cin gashin kai da kuma bashin haƙƙin ƙarin girma da matsayi na malamai.
Ƙungiyar ta ce rashin warware waɗannan batutuwa ya tilasta mata fara yajin aikin gargaɗi domin matsa wa hukumomin da abin ya shafa lamba su ɗauki matakan da suka dace. Matakin ya jefa harkokin karatu a jami’ar cikin tsaiko, yayin da ɗalibai da iyayensu ke fatan samun mafita cikin gaggawa.
Sai dai mahukuntan KASU sun roƙi ASUU da ta dakatar da yajin aikin, suna mai cewa ana ci gaba da tattaunawa domin warware matsalolin. Mataimakin Shugaban Jami’ar, Farfesa Abdullahi Ibrahim Musa, ya ce mahukunta sun fahimci damuwar malaman da kuma fargabar ɗalibai da iyayensu kan yiwuwar tsawaitar matsalar.
Farfesa Musa ya roƙi ASUU da ta bai wa tattaunawar da ake yi damar yin nasara tare da sake duba matakin fara yajin aikin gargaɗin, musamman ganin irin matakan da gwamnatin Jihar Kaduna ke ɗauka wajen magance batutuwan da ake tattaunawa a kansu. Ya ce dakatar da yajin aikin zai ba da damar ci gaba da tattaunawa har a cimma matsaya da za ta kawo ƙarshen rikicin.














