ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Jam’iyyar APC Ta Bukaci Matasa Su Jagoranci Kare Dimokuraɗiyyar Nijeriya

by Muhammad
4 months ago

Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Nentawe Yilwatda, ya buƙaci matasan Nijeriya da su taka muhimmiyar rawa a gaba wajen kare wa da kuma ƙarfafa dimokuraɗiyyar ƙasar, yana mai bayyana su a matsayin ginshiƙi da tasiri ga zaman lafiya da makomar ƙasa.

Da yake jawabi a kan sauye-sauyen da ake yi a ƙasa a halin yanzu, Yilwatda ya ƙarfafa matasa musamman masu shekaru tsakanin 25 zuwa 55 da su ɗauki alhakin kare tsarin dimokuraɗiyya, tare da ƙin amincewa da yunƙurin wasu ’yan siyasa masu son zuciya da ke ƙoƙarin kawo cikas ga ci gaban ƙasa.

Ya ce wannan kira ya zama dole duba da yadda wasu ɓangarorin siyasa ke yunƙurin yaɗa manufofi na son rai, tare da ruɗar da jama’a game da manufar da sakamakon sauye-sauyen da gwamnatin yanzu ke aiwatarwa.

ADVERTISEMENT

A cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan yaɗa labarai, Abimbola Tooki, ya rattaba wa hannu, ya ce: “Dimokuraɗiyyar Nijeriya na cikin wani muhimmin mataki. Nauyin kare ta da kuma tabbatar da dorewarta yana kan matasa, waɗanda ke da ƙarfi, ƙirƙira da kishin ƙasa da ake buƙata domin ciyar da ƙasa gaba. Bai kamata mu bari waɗanda ba su da sahihan mafita su ruɗi jama’a ko su dakile nasarorin da aka samu ba.”

Yilwatda ya bayyana cewa APC ta zama jam’iyya mai dogaro da matasa, inda fiye da rabin mambobinta matasa ne, abin da ya ce ya nuna tsari na musamman na haɗa kowa da kowa, sabunta shugabanci da kuma bunƙasa matasa.

LABARAI MASU NASABA

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi

Ya ƙara da cewa fitowar matashi a matsayin shugaban jam’iyyar na ƙasa a karon farko tun bayan kafuwarta alama ce ta ƙudirin bai wa matasa dama da kuma daidaita tsarin jam’iyyar da yanayin yawan al’ummar Nijeriya.

A cewarsa, bai wa matashi wannan matsayi na nuna amincewa da ƙwarewa da hangen nesa na matasa, tare da ƙarfafa ra’ayin cewa dorewar dimokuraɗiyya da ci gaban ƙasa na rataye ne a kan shigar su a harkokin mulki da sauye-sauye.

Shugaban APC ya kuma yi gargaɗi game da bai wa mutanen da ke bin son rai makomar ƙasa, musamman waɗanda ya zarga da neman shugabanci “ko ta halin kaka,” yana mai cewa hakan na iya jefa ƙasa cikin rashin tabbas.

Ya amince cewa sauye-sauyen da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ke aiwatarwa na tattare da ƙalubale, amma ya jaddada cewa suna da muhimmanci domin samar da daidaiton tattalin arziki da ci gaba mai ɗorewa.

Yilwatda ya ce alamun farko sun nuna cewa sauye-sauyen na taimakawa wajen sake fasalin Nijeriya zuwa tafarkin ci gaba mai ɗorewa, ladabtar da harkokin kuɗi da kuma ƙara ƙwarewa a kasuwannin duniya.

Muhammad
+ postsBio
  • Muhammad
    Yadda Na Tsira Daga Cutar Mashaƙo A Katsina: “Na Fara Da Tsartuwar Jini Tare Da Yawu”
  • Muhammad
    An Naɗa Yusuf Nasidi Nasir A Matsayin Talban Barayan Kano
  • Muhammad
    Wani Kamfani Ya Tallafa Wa Masu Sana’ar Shayi A Kano
  • Muhammad
    Kosan Waka Ya Rasu, Gwamnan Kano Ya Jajanta Wa Iyalansa

MASU ALAKA

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027
Siyasa

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi
Manyan Labarai

2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi

September 8, 2026
Siyasa

Muna Da Yan Takarar Gwamna A Jihohi 28 Don Shiga Zaben 2027

September 6, 2026
Next Post
An Nuna Al’Adun Gargajiyar Kasar Sin A Karon Farko Yayin Bikin Murnar Samun ’Yancin Kan Kasar Togo

An Nuna Al’Adun Gargajiyar Kasar Sin A Karon Farko Yayin Bikin Murnar Samun ’Yancin Kan Kasar Togo

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.