ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Jihar Oyo Za Ta Sayo Laftof 60,000 Saboda Sabon Tsarin Jarrabawa

by Idris Aliyu Daudawa and Sulaiman
7 months ago
Oyo

Jihar Oyo ta kara jaddada aniyarta ta shiryawa fara anfani da sabon tsarin jarrabawar hukumar shirya jarrabawa ta Afirka ta yamma wadda aka fi sani da WAEC amma irin tsarin CBT wato yadda ake jarrabawar shiga manyan makarantu wato JAMB.

Yin hakan ya yi daidai da umarnin gwamnatin tarayya na bin tsarin yadda za’a bar ko daina amfani da biro da takarda, zuwa jarrabawar kafar sadarwa ta zamani ko kuma irin tsarin yadda ake yi lokacin jarrabawar shiga manyan makarantu.

  • An Gabatar Da Bikin Share Fagen Shirin Talibijin Na Murnar Sabuwar Shekarar Sinawa A Masar 
  • Abin Da Ya Sa Ta’addanci Ya Samu Gindin Zama A Arewa – Tsofaffin Janarori

Kwamishinan ilimi, kimiyya da fasaha, Olusegun Olayiwola, shi ne wanda ya bayyana hakan lokacin daya amshi bakuncin jagora kuma mataimakin Rajistara na hukumar WAEC,Mista. Waheed Amode,da shi da ‘yan tawagarsa lokacin da suka kai ma shi ziyara bangirma a ofishinsa da ke Ibadan.

ADVERTISEMENT

Olayiwola ya bayyana cewa Gwamna Seyi Makinde ya bada umarni na a gano ko nawa ake bukata wajen sayen fiye sa Laptops 60,000 saboda amfani da su a manyan makarantun Sakandare a fadin Jihar,inda ya ce manufar hakan ita ce Jihar ta shirya wa fara amfani da tsarin jarrbawa na CBT da za a rika amfani da tsarin wajen rubuta jarrabawar WAEC.

Ya jinjinawa hukumar ta WAEC akan matakin data dauka domin ta yi maganin matsalolin da aka fuskanta lokacin da aka yi jarrabawa daban daban a shekarar 2025,yayin da ya byi alkawari na ma’aikatar zata ci gaba da taimakawa wajen maganin magudin jarrabawa, da kuma lalata kayan makaranta.

LABARAI MASU NASABA

An Tantance Masu Neman Aikin Koyarwa 500 A Jigawa

JAMB Ta Ƙara Wa’adin Amincewar Guraben Karatu Zuwa 30 Satumba

A na shi bayanin, Amode cewa ya yi ziyarar tasu zuwa ma’aikatar ilimi ta Jihar Oyo domin su nuna jin dadinsu kan irin taimakon da ta bada lokacin da aka yi jarrabawar shekarar 2025, da kuma yadda ta ke ci gaba da hadin gwiwa da hukumar a shekarun da suka gabata,inda yace ma’aikatar tana daga cikin masu ruwa da tsaki dangane da nasaraorin da ta samu wajen aiwatar da ayyukanta.

Ya bayyana cewa za’a rufe yin rajistar jarrabawar watan WAEC Mayu/Yuni 2026 ranar 2 ga Fabrairu 2026,ya kuma kara da cewa,jarrabawar da za’a yi nan gaba za’ayi amfani ne da CBT da kuma alkalami da takarda,wannan kuma kamar yadda yace ya danganta ne da irin shirin da makarantun suka yi,yayin da makarantun da suke bukatar su yi jarrabawar gaba dayansu ta hanyar CBT ana bukatar da su nuna bukatarsu ta yin hakan ta rubuta neman yin hakan ta ma’aikatar ilimin.

Amode bugu da kari ya ce da akwai tsauraran matakan da za’a dauka da basu da dadi suke jiran daliban da aka kama su da lafin kasancewa da waya a dakin jarrabawa.

Ya ce irin wannan halin na satar jarrabawa ko aikata wani abnda bai dace ba yana iaya sa a soke sakamakon jarrabawar makarantar gaba daya,wannan kuma ya danganta ne kan irin yadda aka aikata laifin,don haka ya yi kira da Shugabannin makaranta da Malamai dasu maida hankalinsu kan aikata ayyukansu da gaskiya wanda hakan zai sa a kara bunkasa darajar ilimi.

Olayiwola ya yi kira da Iyaye, masu kula da karatun yara da kuma Malamai da su kara kyautata hadin kansu domin su samu damar yadda za su yi maganin rashin halaye masu kyau na dalibai,yace domin kuwa idan aka samu hadin kan makaranta da gida sune abubuwan da zasu taimaka wajen inganta tarbiyya,ta hanyar samar da wata dama da dalibai za su tashi da halaye masu nagari abin koyi ga kowa.

Kwamishinan ya ya yi wannan kiran ne lokacin da ya karbar bakuncin wata kungiya ta kawo gyara kan harkar ilimi ta kasa (NERM),inda ya yi kiuran masu ruwa da tsaki su maida hankalin kan tabbatar da ana aiwatar da koyar da tarbiyya da kuma ingantaccen ilimi, ya yin da shi kuma jagoran kungiyar,Mista.Adewumi Abass,ya ja kunne da kuma yin gargadin babu cikakken hadin kan Iyaye da Malamai da samun karuwar magudin jarrabawawa, lamarin da yake kara zama wata wani babban kalubale kan irin tsarin yadda ake tafiyar da ilimi a Nijeriya,don haka ya bada shawarar a rika yin amfani da wani littafi, mai suna“Yadda Iyaye ya dace su kasance domin ci gaban’ya’yansu,”amatsayin wata manuniya ce.

Oyo
Idris Aliyu Daudawa
+ posts Bio
  • Idris Aliyu Daudawa
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-aliyu-daudawa/
    Tarihin Rayuwar Galadiman Kano Alhaji Tijjani Hashim (2)
  • Idris Aliyu Daudawa
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-aliyu-daudawa/
    Kyamar Baƙi: An Sake Kwaso Ƴan Nijeriya 83 Daga Afirka Ta Kudu
  • Idris Aliyu Daudawa
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-aliyu-daudawa/
    Kamfanin Simintin Dangote Ya Tallafa Wa Manoma 60 Da Kayan Aiki A Edo
  • Idris Aliyu Daudawa
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-aliyu-daudawa/
    Tsohon Shugaban Ƙasa Jonathan Ya Ƙaddamar Da Ayyukan Raya Ƙasa 18 A Jihar Bauchi
Oyo
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • Sulaiman
    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

MASU ALAKA

Oyo
Ilimi

An Tantance Masu Neman Aikin Koyarwa 500 A Jigawa

August 31, 2026
Oyo
Ilimi

JAMB Ta Ƙara Wa’adin Amincewar Guraben Karatu Zuwa 30 Satumba

August 29, 2026
Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya
Ilimi

Kano Ta Yi Zarra Wajen Kashe Kuɗi Don Raya Ilimi A Yammacin Afirka

July 11, 2026
Next Post
Xi Jinping Ya Aike Da Sakon Taya Murna Ga Babban Taron AU Na 39

Xi Jinping Ya Aike Da Sakon Taya Murna Ga Babban Taron AU Na 39

LABARAI MASU NASABA

Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.