ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Abin Da Ya Sa Ta’addanci Ya Samu Gindin Zama A Arewa – Tsofaffin Janarori

by Sani Anwar and Sulaiman
7 months ago
Ta'addanci

Manyan tsoffin hafsoshin soji da kwararru a harkar tsaro da suka yi ritaya, sun bayyana dalilin da ya sa ake ci gaba da samun yawaitar sace-sacen mutane da ‘yan bindiga a Arewa, duk da kokarin da ake yi na ganin an shawo kan matsalar.

Sun danganta al’amarin ne da rashin tantance matsalar da kuma rashin tsaro a yankunan karkara da ake kai wadannan hare-hare.

  • Gobara Ta Sake Tashi A Kasuwar Singa A Kano
  • Gwamnatin Tarayya Ta Ankarar Da Masu Kiwon Kaji Kan Ɓullar Murar Tsintsaye

Jihohin Katsina, Zamfara, Kaduna, Sakkwato da Neja, sun sha fama da hare-haren da ba su ji ba, ba su gani ba a ‘yan kwanakin nan.

ADVERTISEMENT

Haka zalika, a kwanakin baya, Jihar Kwara ta shiga tsaka mai wuya, inda wadannan ‘yan ta’adda suka shiga cikin al’ummarta, suka yi mummunar barna.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu, a ranar 26 ga Nuwamban 2025, ya ayyana dokar ta-baci a dukkanin fadin wannan kasa, sannan ya umarci sojoji da ‘yansanda, da su dauki dubunnan karin jami’ai, domin magance munanan tashe-tashen hankula a fadin kasar.

LABARAI MASU NASABA

Karuwar Farin Jinin Gwamna Umaru Bago A Siyasar Jihar Neja

Kyakkyawan Tsarin Laken Asiri Zai Dakile Shirin Magudin Zabe A Nijeriya —Mohammed

Har ila yau, Tinubu ya umurci ‘yansanda da su dauki karin jami’ai 20,000, tare da bayar da izinin amfani da sansanonin masu yi wa kasa hidima a matsayin wuraren horaswa.

Kazalika, ya kuma bayar da umarnin janye jami’an ‘yansanda daga aikin gadi na manyan mutane (BIP), don sake tura su wuraren da ake fama da rikici, bayan sake horas da su.

Amma, fiye da wata biyu kenan bayan wadannan sanarwa, ba a ga wani gagarumin sauyi a tsakanin al’ummomin da ke fama da wadannan matsaloli ba.

Manjo Janar Chris Olukolade mai ritaya, wanda tsohon mai magana da yawun rundunar tsaro ne, ya alakanta matsalar ta’addancin kan rashin kula da iyakoki yadda ya kamata da kuma nuna banbance-bancen addini da siyasa.

Ya ce, wadannan su ne manyan tushen da suka sa ake ci gaba da aikata laifuka a yankin.

Har ila yau, ya kara da cewa; “Wani batu kuma shi ne, matsalar ra’ayin addini da siyasa da son zuciya, na matukar taimakawa wajen ta’azzarar wadannan laifukan.”

Ya ci gaba da cewa, sakacin da mutane suka yi da kuma rashin jajircewar gwamnati, na daya daga cikin abubuwan da suka kara taimakawa wajen tabarbarewar lamarin.

“Sakacin da aka samu daga wurin wasu al’ummomin, musamman ta fuskar zamantakewa da tattalin arzikin jama’a da kuma rashin isassun matakai, don kawo karshen rikicin, sun taimaka kwarai da gaske,” in ji shi.

Birgediya Janar Sani Usman mai ritaya, ya danganta rashin iya magance matsalar rashin tsaron da matsalar rashin hadin kai wajen daukar matakan da suka dace da kuma rashin fahimtar rikicin shi kansa.

Ya zargi “rashin kwararrun masu bincike da gudanar mulki” da bazuwar wannan rashin tsaro da ake fama da shi.

Manajan Darakta na ‘Beacon Security and Intelligence Ltd’, Dakta Kabir Adamu ya ce; wata biyu bayan sanarwar Shugaba Tinubu, babu wani abu da ya canza sosai, saboda har yanzu al’ummomin karkara na cikin matsalar rashin tsaro.

“Gwamnatin tarayya ta gaza wajen gudanar da harkokin tsaro, sannan majalisar tsaro ta kasa, ita ma tag a gaza a matsayin hukumar da ke kula da harkokin tsaron kasarmu, kazalika kuma, majalisar dokokin kasar ta gaza wajen gudanar da ayyukanta na tabbatar da bin doka da oda a bangaren tsaro,” in ji shi.

Haka nan, ya kuma zargi gwamnonin jihohi da rashin yin abin da ya dace, wajen tabbatar da tsaron ‘yan kasa.

“Gwamnoni, wadanda su ne shugabannin tsaro na jihohi daban-daban, wadanda suke karbar kudaden tsaro, suna kashewa amma babu wani abin a zo a gani da suke yi a jihohin nasu,” in ji shi.

Ta'addanci
Sani Anwar
+ posts Bio
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Ko Kun San Amfanin Kwanciya Da Bangaren Hagu?
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    2027:Mata Shida Da Ke Takarar Neman Shugabancin Nijeriya
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Dambarwa A Kasuwancin Iyalan Indimi
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Illar Shan Taba Sigari Da Dangoginta
Ta'addanci
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi
  • Sulaiman
    Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

MASU ALAKA

Gwamnatin Neja Ta Bayar Da Umarnin Kawo Karshen Matsalar Tsaro
Rahotonni

Karuwar Farin Jinin Gwamna Umaru Bago A Siyasar Jihar Neja

September 5, 2026
Kyakkyawan Tsarin Laken Asiri Zai Dakile Shirin Magudin Zabe A Nijeriya —Mohammed
Rahotonni

Kyakkyawan Tsarin Laken Asiri Zai Dakile Shirin Magudin Zabe A Nijeriya —Mohammed

September 5, 2026
Jihar Katsina Da UNICEF Sun Ceto Rayuwar Yara Ta Hanyar Samar Da Abinci Mai Gina Jiki
Rahotonni

Jihar Katsina Da UNICEF Sun Ceto Rayuwar Yara Ta Hanyar Samar Da Abinci Mai Gina Jiki

September 5, 2026
Next Post
An Nuna Bidiyon Gabatarwar Shirye-Shiryen Bikin Bazara Na CMG A Sassan Afirka

An Nuna Bidiyon Gabatarwar Shirye-Shiryen Bikin Bazara Na CMG A Sassan Afirka

LABARAI MASU NASABA

Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.