ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kogi Poly Ta Sallami Ma’aikata Biyu Kan Cin Zarafin Jima’i Da Rashin Zuwa Aiki

by Abubakar Sulaiman
9 months ago
Kogi

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

Hukumar Gudanarwa ta Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kogi (Kogi State Polytechnic), Lokoja, ta amince da sallamar wasu ma’aikata biyu bisa laifuffuka daban-daban. A cikin wata sanarwa da Daraktan hulɗa da Jama’a da Ladabtarwa, Uredo Omale, ya fitar, an ce an sallami Mukhtar Muhammed, jami’in gudanarwa mataki na biyu, sakamakon samunsa da laifin cin zarafin jima’i, yayin da aka sallami Funmilayo Afolabi, Mataimakiyar Babban Jami’in Gudanarwa, saboda gudun aiki na tsawon watanni tara.

Sanarwar ta ce Majalisar ta kuma amince da rage muƙamin Audu Mathew, Mataimakin Rijista, zuwa Babban Mataimakin Rijista saboda sakaci wajen aiki. Haka kuma, Majalisar ta amince da ɗaga darajar Malamai manya 11 zuwa matsayin manyan Malamai (Chief Lecturers), tare da haɓaka darajar ma’aikata 572 na koyarwa da na gudanarwa a cibiyar.

  • Makarantar Kogi Poly Ta Bankaɗo Masu Ƙirƙirar Takardun Kammala Karatu na Bogi
  • Atletico Madrid Ta Zazzaga Wa Real Madrid Ƙwallaye 5 A Metropolitano

Waɗannan matakai sun fito ne daga taron Majalisar Gudanarwa karo na 72, wanda Shugabanta, Barista Sani Shaibu, ya jagoranta a ranar Juma’a, 19 ga Disamba. Daga cikin waɗanda aka ɗaga matsayi akwai malamai daga makarantu daban-daban na kimiyya, da injiniya, da kasuwanci, da sadarwa, tare da amincewa da ƙarin haɓaka darajar ma’aikata 49 na koyarwa da 71 na gudanarwa a shekarar 2024, da kuma 225 na koyarwa da 227 na gudanarwa a shekarar 2025.

ADVERTISEMENT

A jawabinsa, shugaban na Kwalejin, Farfesa Salisu Ogbo Usman, ya ce matakan na nuna ƙudurin Majalisar wajen tabbatar da ladabi, da gaskiya da ingancin ilimi. Ya kuma bayyana gano wani gungun masu ƙirƙirar sakamakon jarrabawa, inda aka kama Henry Tope da takardun sakamako 30 da shaidar kammala karatu guda ɗaya na bogi. Shugaban Majalisar, Barista Sani Shaibu, ya jaddada cewa Kwalejin ba za ta lamunci duk wani abu da zai ɓata mutuncinta ba, tare da kira ga ma’aikata su bi ƙa’idoji da ɗabi’un sana’a.

Kogi
Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    Iyalin El-Rufai Sun Bai Ministan Tsaro Wa’adin Kwana 7 Kan Zargin Rikicin Kudancin Kaduna
  • Abubakar Sulaiman
    Atiku Ya Zargi Gwamnatin Tarayya Da Cin Bashi Kamar Mashayin Da Kuɗi Ya Ƙarewa
  • Abubakar Sulaiman
    Boko Haram Ta Kai Hari Adamawa, Ana Fargabar Mutuwar Mutane 11
  • Abubakar Sulaiman
    Ƴan Bindiga Sun Kai Hari Sokoto, Sun Kashe Mutane 7, Sun Yi Garkuwa Da 12

MASU ALAKA

Sojoji
Manyan Labarai

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina
Labarai

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Next Post
An Kama Mata 2 Bisa Zargin Shigar Da Miyagun Ƙwayoyi Gidan Gyaran Hali Na Kano

An Kama Mata 2 Bisa Zargin Shigar Da Miyagun Ƙwayoyi Gidan Gyaran Hali Na Kano

LABARAI MASU NASABA

Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.