ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kuskure Ne Daukar Harkar Fim A Matsayin Sana’a Kadai —Maryam CTV (2)

by Rabi'at Sidi Bala and Sulaiman
8 months ago
Maryam

Bayan fim kina wata sana’ar ne?

Ina siyar da kayayyaki, su atamfofi, shaddodi, takalma, jakunkuna, kayan yara, sabulai masu hadi masu kyau da gyara jiki, ba wanda za su saka fari ko su lalata fuska ba.

ADVERTISEMENT

Ko akwai wasu matsaloli a cikin masana’antar Kannywood wadanda ki ke ganin ya kamata a gyara su?

Ai matsaloli ba a cikin harkar fim ba, a zamanin nan na yanzu ko’ina akwai matsaloli. Alhmdulillahi mu yanzu mun samu shugabanni na kirki, wadanda suke ruke da ragamar wannan masana’antar me albarka wato Kannywood. Kamar irinsu; Abba El-Mustapha, mutum ne wanda ya san aikinsa ya san makaman aiki, kuma Alhamdulillahi idan da abubuwa duk sun babbaci, yanzu Alhamdulillahi komai ya fara gyaruwa. Yaushe rabon a ji an ce wani dan fim ko ‘yar fim ta janyo magana ko ta dauko wani abu, babu wannan. Sai kuma abin da zan fada ya kamata ace mu iyaye mata ko maza ana girmama mu sosai fiye ma da yadda ake yi mana a baya. Tunda mu gaskiya mun dade muna gwagwarmaya a harkar nan, in ritaya ne ma ai yanzu ana maganar mutum ya kusa ritaya. Duk da in ka yi ritayar ba fansho za a baka ba, ya danganta da yadda furodusa ya dauke ka, amma ni ina kira ne ga furodusoshin tunda su daraktoci saka su ake su yi a biya su. Amma furodusa shi ne dungurugun me aiki a hannu, me kuma kudi a hannu. Ya rika tausayawa ‘yan tsofaffin nan da suka dade a cikin Kannywood, shi ne kawai abin da zan kira.

LABARAI MASU NASABA

Tun Ina Karama Marigayi Tumbuleke Ke Sa Ni Dariya —Hannatu Musawa

Nazari Kan Wasu Dalilan Da Ke Haddasa Sabanin Abotakar Jarumi Ko Jaruma A Kannywood

Misali ki zama shugaba, wane irin cigaba ki ke ganin za ki kawo ga masana’antar Kannywood?

Ni ina ni ina shugabanci, ai shugabanci ya danganta da yadda mutum yayi karatunsa ko gwagwarmayarsa, ba wai na ce ba zan iya shugabanci ba a’a, yanzu muna da zakakuran shugabanni wanda suka tsaya akan harkar. Daman in ka ji ana ina ma ni ne nake shugabanci to, abu ya kwabe an rasa me gyara, amma yanzu Alhmdulillah komai ya gyaru.

Wadanne irin tambayoyi aka fi yi miki da zarar an ci karo da ke a zahiri?

Bai wuce na fim ba, irin na ganki a kaza ya aka yi ki ka yi kaza da sauransu, ko su yi min tambayoyi akan abokan sana’a ta, ko su ce na basu lambar wata abokiyar sana’a ta. Gaisuwa dai na mutunci da darajantawa.

Wacce shawara za ki bawa masu kokarin shigowa cikin masana’antar Kannywood?

Farko su fara da gida, a nemi shawararsu da yardar su. Dan duk abin da iyayenka suka yarda suka baka shawara a kai da amincewarsu duk inda ka shiga, in Allah ya yarda za ka samu nasara. In babu iyaye a nemi shawarar ‘yan’uwa wanda suka isa da su. Idan sun shigo su bi shugabanni su bigirmama su, mu ma iyayensu da akwai kakanninsu ma su gurmamasu. Wacce ta fi ka ta zama Antinka da can haka ake a Kannywood. Sannan kar ki ga kin samu damar fara fim ki je ki ta zuba iyashege, ko a rika ganinki wuraren da bai dace ba, in an kama ki ki ce ke ‘yar fim ce. To, wannan ba daidai ba ne.

Ko akwai wata shawara da za ki bawa sauran abokan sana’arki na fim?

Alhmdulillahi mu mata kanmu a hade yake, muna zaune lafiya muna mutunta juna, muna ganin girman juna  in wani abu ya tashi na wani za mu dunguma mu je, in na jaje ne mu jajanta masa, in na farinciki ne mu nuna farincikinmu. Daga bangaren mu manya mata kenan.

Me za ki ce da gidan jaridar LEADERSHIP HAUSA, har ma da masu karanta wannan hirar taki?

Sai dai na ce Allah ya kara daukaka, gaskiya kuna fitowa al’umma da manufofi da bayanai akan duk wanda ya kamata su sani, masu karatu idan kuna so ku ji tarihi gaskiya to, ku nemi Jaridar LEADERSHIP HAUSA za ku ji cikakken labarin mutum, kuma daman an ce Waka a bakin me ita ta fi dadi. Allah ya kara muku basira ya kara daukaka, na gode sosai.masana’antar shirya finafinan Hausa ta Kannywood. A wannan makon mun kawo muku ci gaban hirar da wakiliyarmu RABI’AT SIDI BALA ta yi da fitacciyar jarumar wacce ta shafe sama da shekaru ashirin a cikin masana’antar Kannywood wato, HAJ MARYAM SULAIMAN wacce aka fi sani da MARYAM CTB. Inda ta bayyanawa masu karatu babban cigaban da masa’antar Kannywood ta samu a yanzu, da kuma wasu abubuwa da masana’antar ta rasa a yanzu sabanin shekarun baya. Baya ga haka jarumar ta yi kira ga furodusas kan wani nauyi da ya kamata su sauke shi, hadi da wasu batutuwa masu yawan gaske da suka shafi masana’antar da kuma masu yunkurin shiga cikin masana’antar, har ma da wasu batutuwan masu yawa.

Maryam
Rabi'at Sidi Bala
+ posts Bio
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    Yadda Alaƙata Da Adamu Zango Ta Bunƙasa A Kannywood —Jarumi Ibrahim Sodangi 
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    Fim Ko Gaske:Yaushe Masu Kallon Fina-finai Za Su Daina Daukar Fim A Matsayin Gaske
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    Fim ɗin ƙaddara: Anya Ana Samun Irin Wannan ƙaddarar Kuwa?
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    Ko Kafa Ƴansandan Jihohi Zai Taimaka Wajen Kawo Ƙarshen Matsalolin Tsaro?
Maryam
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • Sulaiman
    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna
  • Sulaiman
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

MASU ALAKA

Tun Ina Karama Marigayi Tumbuleke Ke Sa Ni Dariya —Hannatu Musawa
Nishadi

Tun Ina Karama Marigayi Tumbuleke Ke Sa Ni Dariya —Hannatu Musawa

September 5, 2026
Nazari Kan Wasu Dalilan Da Ke Haddasa Sabanin Abotakar Jarumi Ko Jaruma A Kannywood
Nishadi

Nazari Kan Wasu Dalilan Da Ke Haddasa Sabanin Abotakar Jarumi Ko Jaruma A Kannywood

August 29, 2026
Maryam
Nishadi

Dalilan Da Suka Sa Ba Zan Iya Auren Ɗan Film Ba —Bilkisu Bishasha

August 23, 2026
Next Post
Gwamnatin Tarayya Da ASUU Za Su Sanya Hannu Kan Sabuwar Yarjejeniya Ranar 14 Ga Janairu

Gwamnatin Tarayya Da ASUU Za Su Sanya Hannu Kan Sabuwar Yarjejeniya Ranar 14 Ga Janairu

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.