ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Manyan Nasarorin Da Abubakar Dantsoho Ya Samar A NPA A 2025

by Leadership Hausa
9 months ago

Yau kusan shekaru biyu ke nan, da shugaban kasa Bola Tinubu, ya nada Dakta Abubakar Dantsoho, a matsayin Shugaban Hukumar kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Kasa NPA.

Dantsoho wanda aka haifa a garin Jalingo na Jihar Taraba, akasarin ‘yan jihar, sun nuna jin dadinsu da kuma gamsuwarsu, bisa nadin dansu, a kan wannan mukamin

  • ‘Yansanda Sun Kama Mutane 22, Sun Ƙwato Makamai, Motoci, Da Ƙwayoyi A Faɗin Nijeriya 
  • An Yi Bikin Murnar Cika Shekaru 15 Da Kafuwar Asibitin Abota Na Sin Da Ghana

Shugaban ya kasance ya na rike da shedakar karatu ta Digiri a fannin kimiyyar Maritime Technology, da ya samo daga jami’ar Liberpool John Moores, da ke a Birtaniya da kuma wata takardar Digiri ta harkar sufuri ta kasa da kasa da ya samo daga jami’ar Cardiff da ke a yankin Wales, na Birtaniya.

ADVERTISEMENT

Kafin Tinubu ya nada shi, shugaban NPA, Dantsho ya rike mukamin dama a NPA.

A wannan shirhin, ya karkarta ne, kachokam kan irin manyan dimbin nasarorin da Dantsoho ya samar, tun bayan nada shi, shugaban NPA.

LABARAI MASU NASABA

Yadda Taron Bikin Maulidi Ya Gudana A Unguwar Mile 12 A Legas

NPA Ta Bayyana Cewa Kirkiro Da Sabuwar Hukumar NPERA Ba Zai Zame Mata Tarnaki Ba

Kasancewarsa, jajirtaccen shugaba kuma mai rikon amana da kuma yin aiki tukuru, musamman domin kai NPA ga tudun mun tsira.

A bisa irin wannan kyakyawan shugabancin na Dantso ne, shugaba Bola Tinubu a ‘yan makwannin baya, ya karrama Dantsoho, da lambar yabo ta musamman ta NEAPS bisa gudunmawar da ya ke ci gaba da bayarwa wajen samar da kyawan sauye-sauye, a fannin sufurin Jiragen Ruwa na kasar nan, tare da kuma samar da kayan aiki na zamani a Tashoshin Jiragen Ruwa na kasar wadanda kuma suka yi daidai, da na fadin duniya.

A karkashin shugabancinsa, shugaba Tinubu, ya bayar da umarnin a fara aikin gyran Tashoshin Jiragen Ruwa na Apapa da Kalabar da Fatakwal da kuma ta Warri, inda aka amince da a kashe Naira biliyan daya, domin yin aikin.

Kazalika, Dantsoho ya samar da tsarin NSW ta hanyar yin amfani da dabarar PCS domin janyo ra’ayin masu zuba jari daga ketare a Tashoshin Jiragen Ruwa na kasar nan.

Akawi kuma batun kara daga darajar Tashoshin Jiragen Ruwa na kasar a tsakanin hukumomin Jiragen Ruwa da ke a Afirka ta Yamma wato PMAWCA.

Bugu da kari, a 2025, an zabi Dantsoho, a matsayin mataimakin shugaban kungiyar masu tafiyar da hukumomin Jiragen Ruwa ta kasa da kasa wato IAPH.

A karkashin shugabancin Dantsoho an sake zabar Nijeriya, zuwa mataki na C a karkashin kungiyar kasa da kasa ta tafiyar da harkar sufurin Jiragen Ruwa wato IMO.

Hakazalika, a karkashin shugabancin Dantsoho, shugaba Tinubu ya amince a fara aikin Tashoshin Jiragen Ruwa na Apapa da Kalabar da Fatakwal da kuma ta Warri, inda Tinubu ya amince da a kashe Naira biliyan daya, domin yin aikin.

A bangaren bunkasa tattalin arzikin Nijeriya, ta kara samun dimbin masu son zuba hannun jari a fannin, musamman biyo bayan sauye-sauyen da Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya kirkiro da su.

NPA ta yi hadaka da sauran masu ruwa da tsaki a fannoni daban-daban.

Dantsoho ya tabbatar da ya kawar da shakku a zuciyar masu zuba jari, sabanin yadda abin yake a baya, kafin nadinsa kan mukamin.

Bisa irin wannan yadarce, wani Kamfani da ke a kasar Singapore ya bai wa NPA kwangila wadda za a gudanar da ita, a karkashin shirin NSW na kasar nan.

NPA na ci gaba da yin kokari wajen sama da saukin wajen gudanar da hada-hadar kasuwanci ta hanyar Tashoshin Jiragen Ruwan kasar, wanda hakan ya sanya, har manyan Jiregen Ruwa suka fara shigo da manyan Kwantainoni zuwa cikin Tashoshin.

A karkashin jagorancin Dantsoho, kungiyar Injiniyoyi ta Kasa NSE ta kaulla hadaka da NPA domin kara bunkasa tattalin arziki na teku.

Ya samar da saukin cunko, musamman na manyan motoci a Tashar Jiragen Ruwa ta Apapa, wanda har Kwamitin da ke kula da ke a jihar Legos wato LASTCOC ne, ya jinjina masa.

Ya kirkiro da sabon tsarin Na’urar Electronic Call Up a Tashar Onne domin rage cunkoso wanda ya fara aiki

A lokacinsa ne, Jiragen Ruwa 20 dauke da Man Fetur da kayan abinci suka sauka a Tasahoshin Jirgin Ruwa ta Legas

Kazalika, a lokacinsa NPA ta yi hadaka da Tashar Jiragen Ruwa ta Snake Island Port wadda za ta shafe tsawon shekaru 45.

An kuma fara aikin sabunta Tashoshin Jiragen Ruwa na Warri da Koko jihar Delta, domin bunkasa kasuwanci a Nijeriya.

Bugu da kari, kula da jindadin walwalar ma’aikatan NPA, nan ma Dantsoho baya yin wasa da hakan, duba da cewa, domin kwa ya daga darajar samar da ilimin zamani domin kara daga kwarewar ma’aikatan.

Dantsho ya matsar da aikin tashoshin Apapa da Tin Can zuwa Zango na daya na 2026, da aka tasara za a fara yi a zangon karshe na shekarar 2025.

A bangaren gudanar da ayyukan jin kai ga alumomi nan ma ya mayar da hankali, domin kuwa NPA ta tallafa wa alummar da ke a kauyen Umuoziri da ke a karamar hukumar Inyishi Ikeduru, ta jihar Imo, inda ta tallafa masu da kayan yin sana’oi da bana da ban, inda wadanda suka amfana, suka godewa NPA kan wannan daukin.

NPA na ci gaba da yin kokari wajen sama da saukin wajen gudanar da hada-hadar kasuwanci ta hanyar Tashoshin Jiragen Ruwan kasar, wanda hakan ya sanya, har manyan Jiregen Ruwa suka fara shigo da manyan Kwantainoni zuwa cikin Tashoshin.

A rabin farkon zangon 2025 Tashoshin Jiragen Ruwa suka samar da kaso 19.6 na fitar da kayan da ba su shafi mai ba.

Tun bayan lokacin da aka nada shi, a matsayin Shugaban Hukumar Kula Da Tashoshin Jiragen Ruwa Ta Kasa NPA, Dakta Abubakar Dantsoho ke kai gworo da mari, wajen ganin ya farfado da kima da kuma darajar NPA.

Wannan namijin kokarin da Dantsoho ke ci gaba da yi, na daya daga cikin kudurin Shugaba Tinubu, na Renewed Hope Agenda.

Dantsho ya kirkiro da sauye-sauye da dama da suka hada da, samar da kayan aiki na gyaran Tashoshin na zamani na biliyoyin dala, musamman domin a sauya tsaffin kayan Tashoshin da kayan aiki na zamani.

Dantsoho, saboda tsaikon da ake samu a Kogin Riba Neja, ya kirkiro da aikin yashe hanyoyin ruwan, musamman domin a rage cunkoso da ake samu a Tashar Jiragen Ruwa ta Onitsha, wanda hakan ya taimaka wajen ci gaba amfana da albarkatun tattalin arziki.

Ya kuma kasance a kan gaba wajen ganin an kaddamar da Tashin Tsayawar Jiragen Ruwa na kan tudu, kamar dai, na gain Funtuwa, da ke a jihar Katsina, wnada an yi hakan ne, domin kara habaka fitar da kana da ba su shafi fannin Mai ba da kuma kara habaka hada-hadar kasuwanci.

Shirin aikin kashe dala biliyan daya a Tashar Snake Island wanda za a kara fadada kadada 85 a cikin Tashar, an yi ne, bisa nufin gudanar da harkar hada-hadar kasuwanci a Tashar, wanda hakan zai kuma kara daga darajar Nijeriya a fagen kasuwanci.

Ayyukan ci gaba da Dantsho ke ci gaba da samarwa a NPA, ba wai kawai nan ya tsaya ba, domin kuwa, a kwanan baya, an zabe shi ya zama shugaban kungiyar kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Gabas da yankin Afirka ta Tsakiya wato PMAWCA.

Dantsoho ya amince da kafa tsarin tara kudade shiga na kai tsaye, a NPA ta hanyar yin hadaka da hukumar kula da harkokin sufurin jiragen ruwa ta ta kasa wato NIMAS da kuma hukumar Kwastam.

Wannan manufar, an yi ta ne, domin a tabbatar da ana bin diddigin tara kudaden shigar da kuma kula da su.

Dantsoho, ya kuma tabbatar da ana kara karafafawa masu hada-hadar Jiragen Ruwa na kasar guiwa wanda kuma ya yi daidai da manufar gwamnatin kasar.

Burin da har zuwa yau Dantsoho ya sanya a gaba shi ne, ganin NPA ta tsarewa tsara, wajen kara samar da ci gaba ba wai kawai a tsakanin nahiyar Afirka ba, har a ma fadin duniya.

Baya ga goyon bayan da yake ci gaba da samu daga shugaban kasa, haka kuma yana ci gaba da samun wani goyon bayan daga gun Ministan Bunkasa Tattalin Arzikin Kasa na kan Teku Adegboyega Oyetola, wajen kara ciyar da NPA gaba.

Leadership Hausa
Website |  + postsBio
  • Leadership Hausa
    Wane Ne Dan Shagamu: Su Wane Ne Suka Kashe Shi A Kano?
  • Leadership Hausa
    An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu
  • Leadership Hausa
    Karuwar Farin Jinin Gwamna Umaru Bago A Siyasar Jihar Neja
  • Leadership Hausa
    Kyakkyawan Tsarin Laken Asiri Zai Dakile Shirin Magudin Zabe A Nijeriya —Mohammed

MASU ALAKA

Yadda Taron Bikin Maulidi Ya Gudana A Unguwar Mile 12 A Legas
Tattalin Arziki

Yadda Taron Bikin Maulidi Ya Gudana A Unguwar Mile 12 A Legas

September 4, 2026
NPA Ta Bayyana Cewa Kirkiro Da Sabuwar Hukumar NPERA Ba Zai Zame Mata Tarnaki Ba
Tattalin Arziki

NPA Ta Bayyana Cewa Kirkiro Da Sabuwar Hukumar NPERA Ba Zai Zame Mata Tarnaki Ba

September 4, 2026
NPA Ta Tabbatar Da Maido Da Manyan Kayan Aikin Hukumar Wuta Ta Neja Delta —Babbar Manaja
Tattalin Arziki

NPA Ta Tabbatar Da Maido Da Manyan Kayan Aikin Hukumar Wuta Ta Neja Delta —Babbar Manaja

August 28, 2026
Next Post
Kidayar Jama’a Da Harkar Ilimi

Kidayar Jama'a Da Harkar Ilimi

LABARAI MASU NASABA

Gwamnatin Tarayya Ta Dakatar da Shirin Ƙara Kuɗin Jarabawar WAEC da NECO

Gwamnatin Tarayya Za Ta Rika Bai Wa Ɗalibai 100MB Na Data Kyauta Kullum

September 10, 2026
Sin Da Amurka Na Wanzar Da Mu’amala Game Da Shirin Ganawar Da Manyan Shugabannin Kasashen Biyu Za Su Yi A Bana

Sin Da Amurka Na Wanzar Da Mu’amala Game Da Shirin Ganawar Da Manyan Shugabannin Kasashen Biyu Za Su Yi A Bana

September 10, 2026
Sojoji Sun Ceto Fasinjoji Uku Da ‘Yan Bindiga Suka Harba A Filato

Sojoji Sun Ceto Fasinjoji Uku Da ‘Yan Bindiga Suka Harba A Filato

September 10, 2026
Xi Zai Halarci Taron BRICS Karo Na 18 A Indiya

Xi Zai Halarci Taron BRICS Karo Na 18 A Indiya

September 10, 2026
Rodri Ya Nemi Afuwar Valencia Dangane Da Kalaman Da Yayi Akanta

Rodri Ya Nemi Afuwar Valencia Dangane Da Kalaman Da Yayi Akanta

September 10, 2026
Za A Gudanar Da Taron Koli Na Shugabannin Harkokin Masana’antu Da Cinikayya Na APEC Na 2026 A Shenzhen

Za A Gudanar Da Taron Koli Na Shugabannin Harkokin Masana’antu Da Cinikayya Na APEC Na 2026 A Shenzhen

September 10, 2026
Amurka Ta Bai Wa Nijeriya Sabbin Kayan Yaƙi Domin Yaƙi Da Ta’addanci

Amurka Ta Bai Wa Nijeriya Sabbin Kayan Yaƙi Domin Yaƙi Da Ta’addanci

September 10, 2026
Xi Ya Bukaci A Kara Azamar Dakile Aukuwar Muggan Hadurra Sakamakon Aukuwar Gobara A Wani Jirgin Ruwan Dakon Kayayyaki

Xi Ya Bukaci A Kara Azamar Dakile Aukuwar Muggan Hadurra Sakamakon Aukuwar Gobara A Wani Jirgin Ruwan Dakon Kayayyaki

September 10, 2026

Jerin Bankuna 32 Da Aka Amince Su Sayar Da Hannun Jarin Matatar Dangote

September 10, 2026

Uganda Za Ta Fara Fitar Da Man Fetur Zuwa Ƙasashen Waje

September 10, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.