ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, June 24, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Matsalar Tsaro Ta Ƙara Zafafa Kiran Samar Da Ƴansandan Jihohi

by Yusuf Shuaibu
2 months ago

Sakamakon kashe-kashen da suka faru kwanan nan a jihohin Filato da Kaduna da sauran sassan ƙasar nan, ya sake tada kiran gaggawa kan samar da ƴansandan jihohi a Nijeriya.

Fiye da mutum 40 sun mutu a Rukuba da ke cikin garin Jos na Jihar Filato, da kuma ƙaramar hukumar Kagarko ta Jihar Kaduna.

Ma’aikatan Ofishin Jakadancin Amurkaz ‘Yan Bindiga

ADVERTISEMENT

Majalisar Dokokin Legas Ta Amince Da Kasafin Tiriliyan ₦4.4 Na Shekarar 2026

Haka kuma, a ranar Ista, mutane kusan 26 ne aka kashe a jihohi uku. A Jihar Benue, mutane kusan 17 a Mbalom da ke ƙaramar hukumar Gwer ta yamma, a Jihar Kaduna, an kai hari ga masu ibada yayin bikin Ista, inda aƙalla mutum biyar suka mutu, yayin da a Jihar Borno, jami’an ƴansanda huɗu ne aka kashe a wani hari da da Boko Haram da ISWAP suka kai.

LABARAI MASU NASABA

Ƴan Ta’adda Sun Ƙone Shingen Bincike Na NSCDC, Sun Sace Wani Mutum A Kebbi

Ƴan Bindiga Sun Kashe Hakimin Gundumar Gwande A Jihar Filato

Saboda haka, ƙungiyoyin fararen hula masu zaman kansu sun ce shawarar da babban sufeton ƴansanda, Tunji Disu, ya bayar na mayar da kashi 60 cikin ɗari na ma’aikatan ƴansanda na yanzu zuwa jihohi a cikin shekaru shida ya yi tsawo, la’akari da ƙaruwar matsalolin tsaro a yawancin jihohin tarayya.

A cikin wata takardar mai shafi 75 kan ƴansandan jihohi da aka miƙa ga majalisar ƙasa, Disu ya ba da shawarar cewa kusan kashi 60 cikin ɗari na ma’aikatan ƴansandan Nijeriya da ke akwai za su koma ƴansandan jiha, yayin da kashi 40 cikin ɗari za su ci gaba da kasancewa cikin tsarin tarayya.

Tsohon babban sufeton ƴansanda, Mohammed Abubakar Adamu, ya kuma nuna goyon bayansa ga kiraye-kiraye na kafa ƴansandan jihohi, yana cewa hakan zai taimaka wajen cike giɓin tsarin ƴansanda.

Ya jaddada cewa mafi yawan jihohi suna da tsare-tsare da ke aiwatar da aikin ƴansanda, ya ƙara da cewa abin da ake buƙata shi ne ƙarfafa su.

Duk da cewa ya amince da tsoron yin amfani da ƴansandan jihohi ta hanyar da bai dace ba ga gwamnonin jihohi, Adamu ya ce gwamnonin na amfani da tsarin ƴansandan ƙarƙashin ƙasa a jihohinsu.

“Tsarin mulkin Nijeriya bai ce mu yi amfani da hukuma guda ɗaya ta ƴansanda ba, ya kamata a ƙirƙiro wasu ƴansanda, amma abin da muke da shi a ƙasar a yau ya nuna cewa mun riga mun gudanar da wasu ayyukan ƴansanda. Lokacin da kake aiwatar da ayyuka da aka tsara don ƴansanda, me kake yi? Kana yin aikin ƴansandan ne. Don haka, tuni kana da ƴansandan.

“A matakin ƙasa, muna da wasu tsare-tsare da hukumomi da ke yin irin waɗannan ayyukan. A matakin jiha, muna da ƙungiyoyi na lura da unguwanni, wasu ma ana kiran su da suna Amotekun, wasu kuna ƴan banga. Me suke yi? Suna yin ayyukan ƴansanda ne. Saboda haka, ko da mun kira su ƴansandan jihohi ko a’a, a zahiri muna da su, amma da sunaye daban-daban. Abin da muke buƙata shi ne, mu ƙarfafasu su kasance masu tasiri wajen magance laifuka.

“A ganina, mutane waɗanda ke adawa da ƴansanda na jihohi suna da dalilansu, cewa gwamnonin za su yi amfani da su ta hanyar da bai kamata ba. Amma gwamnonin tuni suna amfani da ƴan bijilanti da sauran tsare-tsare.

“Saboda haka, muna da tsarin ƴansanda jihohi tuni, abin da muke buƙata kawai shi ne mu ƙarfafa su,” in ji shi.

Haka kuma, tsohon mataimakin sufeton ƴansanda, John Odey, ya bayyana cewa Nijeriya ta yi jinkiri wajen samun ƴansandan jihohi.

A cewarsa, matsalolin tsaro a yanzu a Nijeriya, waɗanda tushen su a ƙananan matakai suke, za a iya warware su idan saka samar da tsarin ƴansanda jihohi a kowane jiha.

Ya yi iƙirarin cewa ƴansandan jihohi za su kawo ayyukan ƴansanda kusa da al’umma, ta haka za su daƙile rikice-rikice tun kafin su zama manyan laifuka da za su shafi jihar da ƙasa baki ɗaya.

Tsohon mataimakin sufeton ƴansanda ya bayyana cewa jihohin kamar Benuwai, Borno, Nijar da Kwara, waɗanda a halin yanzu ke fuskantar ayyukan laifi na ƴan bindiga da masu ta’addanci, za su fi samun matsaya mai kyau tare da ƴansandan jihohi waɗanda za su mai da hankali kan yanayin cikin gida da warware matsalolin da ke akwai.

Wani tsohon kwamishinan ƴansanda, Abiodun Samuel, ya yi iƙirarin cewa ƴa sandan jihohi yanzu suna da muhimmanci kuma ba su sake zama batun muhawara ba.

A cewarsa, zamanin tsoron gwamnonin jihohi suna amfani da su don ayyukan siyasa ya wuce, kasancewar al’amarin laifuka yana zama babbar damuwa.

Ya yi kira ga babban sufeton ƴansanda na yanzu, IGP Olatunji Disu, da ya tabbatar cewa ya bar kyakkyawan tarihi kan kafa ƴansandan jihohi nan gaba, yana mai lura cewa ya fara da kyau tare da kwamitin da aikin da aka yi zuwa yanzu.

A ɓangarensu kuwa, wasu ƙungiyoyin farar hula, watau cibiyar tattaunawa kan dokokin farar Hula (CISLAC) da ‘Transparency International Nigeria, sun ce watanni 60 ba su da muhimmanci, kamar yadda aka gabatar a cikin shawarwarin.

Shugaban ƙungiyoyin, Auwal Musa Rafsanjani, ya shaida wa LEADERSHIP cewa yana da muhimmanci ga gwamnati a dangantakarta da ƴansanda, ta bayar da amsoshi da matakan gaggawa ga ƙalubalen tsaro a matakin jiha.

“A kan shawarar da mataimakin sufeton ƴansanda ya bayar, ina ganin yana da muhimmanci ga gwamnati ta mayar da martani cikin gaggawa tare da shiga tsakani a matsalolin tsaro na matakin jiha. Ba mu buƙatar wani lokaci na watanni 60 kamar yadda aka bayar a shawara ba.

“Muna buƙatar shiga tsakani cikin lokaci da sanya ido a jihohi daban-daban, musamman waɗanda ke yaƙi da rashin tsaro a Nijeriya. Ba ma buƙatar ɓata lokaci wajen tura isassun jami’an tsaro a faɗin jihohi daban-daban da ke fuskantar matsalolin tsaro.

“Don haka, wannan ya kamata ya zama shawarwari na dogon lokaci, amma a yanzu akwai buƙatar tsarin gaggawa, na matsakaici da na dogon lokaci. Gwamnati ya kamata ta tura ƙarin jami’an ƴansanda zuwa matakin jiha saboda a nan ne ake buƙatarsu sosai.

“A matakin tarayya, mafi yawan ƴansanda suna hidima ga fitattun mutane, alhali akwai ƙarancin jami’an tsaro a jihohi daban-daban da ƙananan hukumomi da al’ummomi inda ake samun yawaitar hare-hare masu tashin hankali.

“Don haka, muna kira ga babban sufeton ƴansanda da ya bai wa lamarin fifiko na ƙarin jami’ai cikin gaggawa don ceton rayuka da hana ɓarkewar rikice-rikice a sassa daban-daban na ƙasar,” ya ƙara da cewa.

Manyan lauyoyi a ƙasar sun shaida wa LEADERSHIP cewa babu wani lokaci mafi kyau fiye da yanzu don kafa ƴansandan jihohi a matsayin cibiyar gwamnati.

Sun bayyana goyon bayansu ga kafa ƴansandan jihohi don yaƙi da rashin tsaro a sassa daban-daban na ƙasar nan.

Mista Abdul Balogun, SAN, ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta ayyana dokar ta-ɓaci kan rashin tsaro kuma ta gyara tsarin samar da tsaron ƙasar.

Ya nuna damuwarsa kan yawan rashin tsaro da tashin hankali kuma ya yi kira a ɗauki matakan gaggawa don magance halin da ake ciki.

“Kowa yana cikin damuwa sosai game da halin da ƙasar ke ciki, musamman rashin tsaro a ƙasar, wanda a yanzu haka yana da mummunan tasiri ga kowa, manya da ƙanana.

“Manoma a yankunan karkara ba za su iya zuwa gona ba saboda tsoron makiyaya masu kisa da satar mutane, kuma abin da hakan zai haifar shi ne ƙarin tsadar abinci, wanda zai haifar da wahala a ƙasa.

“Babu wani lokaci mafi kyau don ƴansanda jihohi kayar yanzu. Dole ne a fuskanci rashin tsaro kai tsaye don coto ƙasar daga tarwatsewa,” in ji shi.

Wani lauya, Paul Arua, ya nemi gwamnatin tarayya ta gudanar da cikakken bitar halin tsaro, ciki har da kafa ƴansandan jihohi.

A cewarsa, ƴan Nijeriya na fuskantar mawuyacin hali na rashin tsaro marar iyaka, kuma dole ne a ɗauki mataki na gaggawa.

“Ana buƙatar ƴansandan jihohi cikin gaggawa a halin yanzu fiye da kowane lokaci. Ba za mu iya ci gaba da jiran dogon tattaunawa ba kafin mu sanya shi ya zama gaskiya.

“Muna yawan magana, wanda ke haifar da ƙarancin aiki a wannan ƙasar, amma kamar yadda abubuwa suke yanzu, muna buƙatar ƙarin aiki fiye da tattaunawa a wannan lokaci,” in ji shi.

A ɓangarensa, Lauya Moses A. Aham ya ce ƴansandan jihohi za su taka muhimmiyar rawa wajen magance yanayin tsaro. Duk da haka, ya ƙara da cewa dole ne a haɗa masu ruwa da tsaki a cikin kwamitocin gwamnati don nemo hanyoyin warware matsalolin ƙasar na dindindin.

“Duk wani mataki nagari da zai sa ƙasar ta shiga hanya zuwa aminci ya kamata a ƙarfafa, kuma ya kamata a haɗa ƙungiyoyin ba na gwamnati ba wajen nemo mafita ga matsalolin da ƙasar ke fuskanta,” in ji shi.

Kazalika, malamin kimiyyar siyasa a jami’ar Nnamdi Azikiwe, Dakta Christian Okeke ya yabo wa babban sufeton ƴansanda, Tunji Disu kan bayyana shirin canji na tsawon watanni 60 don kafa ƴansandan jihohi, yana bayyana shi a matsayin mataki mai jarumta kuma mai muhimmanci.

Okeke ya ƙara da cewa kiran kafa ƴansanda jihohi sun daɗe suna cikin muhawarar jama’a, kuma shirin babban sufeton ƴansanda ya wakilci mataki mai muhimmanci wajen ganin an aiwatar da shi.

“Godiya ga sabon babban sufeton ƴansanda, saboda wannan shawarar abun yabawa ne, wadda ke buƙatar shiga tsakani da ci gaba don yin nasara,” in ji shi.

Ya jaddada muhimmancin bayar da cikakken tallafin dokoki ga hukumar tsare-tsaren ƴansanda ta ƙasa da aka bayar domin daidaita ayyukan ƴansanda na tarayya da na jihohi.

“Dole ne a cike shi da ƙwararrun jami’an tsaro masu kishin ƙasa, ba masu ra’ayin siyasa ba kuma masu ƙwarewa,” in ji Okeke.

Okeke ya kuma jaddada rawar da ma’aikatan ƴansanda ta jihohi ke takawa wajen tabbatar da ƙwarewa da girmama haƙƙn Ɗan’adam.

Ya yi kira ga ƴan Nijeriya masu kishin ƙasa su yi aiki tare don kawar da fargabar amfani da siyasa da daƙile aikin ƴansandan jihohi, yana jaddada cewa gwamnonin jihohi suna da muhimmanci ga nasarar wannan gyara.

Yusuf Shuaibu
+ postsBio
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    Rashin Tsaro Na Barazana Ga Zaben 2027 —Rahotanni
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    Yadda Matsin Lamba Ta Sa Amaechi Ya Amince Ya Zama Abokin Takarar Atiku
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    2027: Kallo Ya Koma Kan Yadda APC, ADC Da PDP Ke Neman Abokan Takarar Mataimakin Shugaban Kasa
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    Ko INEC Na Da Hannu A Rikice-rikicen Jam’iyyun Siyasa A Nijeriya?

MASU ALAKA

Ƴan Ta’adda Sun Ƙone Shingen Bincike Na NSCDC, Sun Sace Wani Mutum A Kebbi
Tsaro

Ƴan Ta’adda Sun Ƙone Shingen Bincike Na NSCDC, Sun Sace Wani Mutum A Kebbi

June 21, 2026
Ƴan Bindiga Sun Kashe Hakimin Gundumar Gwande A Jihar Filato
Tsaro

Ƴan Bindiga Sun Kashe Hakimin Gundumar Gwande A Jihar Filato

June 19, 2026
‘Yansanda Sun Kashe Masu Garkuwa Da Mutane 8, Sun Kubutar Da Mutane 3 A Jihar Bauchi
Manyan Labarai

Mata Ta Hallaka Mijinta Da Wuƙa Watanni Biyu Bayan Aure A Kano

June 17, 2026
Next Post

Iran Ta Sake Kulle Mashigar Hormuz, Ta Zargi Amurka Da Kin Janye Shingenta

LABARAI MASU NASABA

‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta

’Yansanda Sun Kama Wani Mutum da Harsasai 174 A Nasarawa

June 24, 2026
Sojoji Sun Kama Ɗan Fashi Da Makami A Taraba

Sojoji Sun Kama Ɗan Fashi Da Makami A Taraba

June 24, 2026
An Kashe Mutum 2, 8 Sun Jikkata Yayin Rikici A Bauchi

An Kashe Mutum 2, 8 Sun Jikkata Yayin Rikici A Bauchi

June 24, 2026
Tsohon Shugaban APC Na Kebbi Ya Rasu A Hannun ’Yan Bindiga

Tsohon Shugaban APC Na Kebbi Ya Rasu A Hannun ’Yan Bindiga

June 24, 2026
Ya Kamata Sin Da Birtaniya Su Yi Aiki Tare Don Ci Gaba Da Inganta Dangantakarsu

Ya Kamata Sin Da Birtaniya Su Yi Aiki Tare Don Ci Gaba Da Inganta Dangantakarsu

June 23, 2026
Firaministan Sin Ya Jaddada Muhimmancin Kara Azamar Bunkasa Kirar Kayayyakin Aikin Masana’antu Na Zamani

Firaministan Sin Ya Jaddada Muhimmancin Kara Azamar Bunkasa Kirar Kayayyakin Aikin Masana’antu Na Zamani

June 23, 2026
Gombe Ta Zabge Farashin Taki Da Kashi 50 Cikin 100

Gombe Ta Zabge Farashin Taki Da Kashi 50 Cikin 100

June 23, 2026
Wang Yi Ya Gana Da Babban Sakataren Majalisar Tsaron Masar Da Ministan Fadar Gwamnatin Afirka Ta Kudu A Indiya

Wang Yi Ya Gana Da Babban Sakataren Majalisar Tsaron Masar Da Ministan Fadar Gwamnatin Afirka Ta Kudu A Indiya

June 23, 2026
‘Yansanda Sun Kashe Masu Garkuwa Da Mutane 8, Sun Kubutar Da Mutane 3 A Jihar Bauchi

’Yansanda Sun Kama Mutane 57 Da Ake Zargi Da Ayyukan Ta’addanci A Adamawa

June 23, 2026
Li Qiang Ya Gana Da Firaministan Kasar Guinea

Li Qiang Ya Gana Da Firaministan Kasar Guinea

June 23, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.