ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, September 11, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Mutane 5 Sun Mutu, An Yi Garkuwa Da 6 A Harin Ƴan Bindiga A Sokoto

by Abubakar Sulaiman
9 months ago
Mutane

Rahotanni daga Gatawa, wani ƙauye da ke ƙaramar hukumar Sabon Birni a Jihar Sokoto, sun tabbatar da cewa wani mummunan hari da ƴan bindiga suka kai a safiyar ranar ya yi sanadiyyar mutuwar mutune biyar.

Wani mazaunin yankin ya bayyana cewa harin ya faru ne da misalin ƙarfe 1:30 na dare, lokacin da maharan suka mamaye ƙauyen tare da yin harbe-harbe ba kakkautawa. Wasu masu gadin ƙauyen sun yi yunƙurin daƙile su, amma harin ya yi muni inda mutum huɗu daga cikinsu suka rasu nan take.

  • Harin Ƴan Bindiga Ya Halaka Mutum 11 A Pretoria
  • Mutum 4 Sun Mutu Yayin Da ’Yan Bindiga Sake Kai Hari Kogi

Baya ga waɗanda suka mutu a wurin, an ce wasu biyu sun samu raunuka sakamakon harbin bindiga, inda aka garzaya da su asibiti domin kulawa. Daga cikin waɗanda aka jikkata, ɗaya daga cikinsu ya rasu daga bisani, lamarin da ya ƙara adadin waɗanda suka mutu zuwa biyar. Mazauna yankin sun bayyana cewa harin ya jefa al’umma cikin firgici, tare da barin iyalai da dama cikin ƙunci sakamakon asarar dangi da makota.

ADVERTISEMENT

A cewar wani da ya nemi a sakaya sunansa, maharan sun kuma sace mutane shida, ciki har da matan aure biyu, ƴan mata biyu da kuma samari biyu. Ya ce bayan kammala harin, ƴan bindigar sun yi awon gaba da dabbobi kafin su tsere daga yankin ba tare da jami’an tsaro sun iso ba. Ya ce an ji ƙarar musayar wuta daga nesa tsakanin jami’an tsaro da maharan, amma babu wanda aka kuɓutar daga cikin waɗanda aka sace.

Al’ummar ƙauyen sun nuna damuwa kan yadda hare-haren ƴan bindiga ke ci gaba da ta’azzara a yankin, suna kuma kira ga hukumomi da su ƙara kula. Har zuwa lokacin wallafa wannan rahoto, ba a samu ƙarin bayani kan martanin hukumomi ba, sai dai mazauna ƙauyen na cigaba da neman taimako wajen ceto waɗanda aka yi awon gaba da su.

LABARAI MASU NASABA

Dalilin Da Ya Sa Ba Zan Janye Wa Atiku Ba A Zaɓen 2027 – Peter Obi

Buƙatar Ɗaukar Matakan Daƙile Yaɗuwar Cutar Mashaƙo A Nijeriya

Mutane
Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    Dalilin Da Ya Sa Ba Zan Janye Wa Atiku Ba A Zaɓen 2027 – Peter Obi
  • Abubakar Sulaiman
    Jerin Bankuna 32 Da Aka Amince Su Sayar Da Hannun Jarin Matatar Dangote
  • Abubakar Sulaiman
    Uganda Za Ta Fara Fitar Da Man Fetur Zuwa Ƙasashen Waje
  • Abubakar Sulaiman
    Iyalin El-Rufai Sun Bai Ministan Tsaro Wa’adin Kwana 7 Kan Zargin Rikicin Kudancin Kaduna

MASU ALAKA

Mutane
Manyan Labarai

Dalilin Da Ya Sa Ba Zan Janye Wa Atiku Ba A Zaɓen 2027 – Peter Obi

September 11, 2026
Cutar Kwalara Na Ci Gaba Da Yi Wa ‘Yan Nijeriya Kisan Mummuƙe
Manyan Labarai

Buƙatar Ɗaukar Matakan Daƙile Yaɗuwar Cutar Mashaƙo A Nijeriya

September 11, 2026
Sojoji Sun Ceto Fasinjoji Uku Da ‘Yan Bindiga Suka Harba A Filato
Manyan Labarai

Sojoji Sun Ceto Fasinjoji Uku Da ‘Yan Bindiga Suka Harba A Filato

September 10, 2026
Next Post
Ministan Wajen Kasar Jamus Zai Ziyarci Kasar Sin

Ministan Wajen Kasar Jamus Zai Ziyarci Kasar Sin

LABARAI MASU NASABA

Mutane

Dalilin Da Ya Sa Ba Zan Janye Wa Atiku Ba A Zaɓen 2027 – Peter Obi

September 11, 2026
Farashin Siminti Zai Ragu Idan Farashin Kayan Aiki Ya Sauka – BUA

Gwarzon Shekarar 2026 Abdulsamad Rabiu

September 11, 2026
Cutar Kwalara Na Ci Gaba Da Yi Wa ‘Yan Nijeriya Kisan Mummuƙe

Buƙatar Ɗaukar Matakan Daƙile Yaɗuwar Cutar Mashaƙo A Nijeriya

September 11, 2026
Ding Xuexiang Ya Halarci Taron Kolin CIFTIS Tare Da Ganawa Da Manyan Jami’an Kasashen Waje

Ding Xuexiang Ya Halarci Taron Kolin CIFTIS Tare Da Ganawa Da Manyan Jami’an Kasashen Waje

September 10, 2026
Sin Ce Ta Zo Ta Farko A Rahoton Yanayin Tsaron Jama’a Na Duniya

Sin Ce Ta Zo Ta Farko A Rahoton Yanayin Tsaron Jama’a Na Duniya

September 10, 2026
Sin Ta Ciri Tuta Game Da Rawar Gani Da Take Takawa A Fannin Warware Kalubalen Tsaro A Gabas Ta Tsakiya

Sin Ta Ciri Tuta Game Da Rawar Gani Da Take Takawa A Fannin Warware Kalubalen Tsaro A Gabas Ta Tsakiya

September 10, 2026
Gwamnatin Tarayya Ta Gwangwaje Tawagar Kwallon Kwando Ta Mata Da Dala 100,000 Kowace

Gwamnatin Tarayya Ta Gwangwaje Tawagar Kwallon Kwando Ta Mata Da Dala 100,000 Kowace

September 10, 2026
Sin Da Amurka Na Gudanar Da Tattaunawa Dangane Da Yiwuwar Rage Harajin Ramuwar Gayya Wanda Darajarsa Ka Iya Kaiwa Dala Biliyan 30

Sin Da Amurka Na Gudanar Da Tattaunawa Dangane Da Yiwuwar Rage Harajin Ramuwar Gayya Wanda Darajarsa Ka Iya Kaiwa Dala Biliyan 30

September 10, 2026
Gwamnatin Tarayya Ta Dakatar da Shirin Ƙara Kuɗin Jarabawar WAEC da NECO

Gwamnatin Tarayya Za Ta Rika Bai Wa Ɗalibai 100MB Na Data Kyauta Kullum

September 10, 2026
Sin Da Amurka Na Wanzar Da Mu’amala Game Da Shirin Ganawar Da Manyan Shugabannin Kasashen Biyu Za Su Yi A Bana

Sin Da Amurka Na Wanzar Da Mu’amala Game Da Shirin Ganawar Da Manyan Shugabannin Kasashen Biyu Za Su Yi A Bana

September 10, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.