• English
  • Business News
Tuesday, October 21, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

NDLEA Ta Kama Magidanci Da Tan 7.6 Na Miyagun Kwayoyi

by Rabi'u Ali Indabawa
2 years ago
Kwayoyi

Jami’an Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Nijeriya wato NDLEA sun kama wani mutum mai shekaru 42 da aka ce yana jigilar dubunnan miyagun kwayoyin na Opiod a boye zuwa wani yanki na ‘yan tada kayar baya a yankin Banki na Jihar Borno.

Wanda ake zargin dai yana cikin mutane 24 da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi a fadin kasar, a cewar kakakin hukumar ta NDLEA, Femi Babafemi, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadin da ta gabata.

  • Tsawon Shekaru Nawa Tattabaru Ke Yi A Duniya
  • Dabarun Noman  Kankana A Nijeriya

Sanarwar ta ce a sumamen da aka yi sun kai ga kama wasu miyagun kwayoyi daban-daban da ya kai kilogiram 7,609 a jihohi takwas.

Haka kuma an kama wata mace mai cikin wata shida, mahaifiyar ‘ya’ya uku, da kuma wasu mata uku a cikin wasu manyan samamen.

A cewar sanarwar, an kama mafi yawan masu jigilar kwayoyin ne a Jihar Nasarawa inda jami’an hukumar NDLEA da ke aiki bisa sahihan bayanan sirri, a watan Fabrairu, suka kama wata mota da lambar Legas JJJ 64 YC dauke da buhunan tabar wiwi guda 367 mai nauyin kilogiram 4,037 daga Akure, Babban Birnin Jihar Ondo, wanda za a kai a yankin Shabu da ke Lafia, babban birnin jihar.

LABARAI MASU NASABA

Jami’an Tsaro Sun Kwato Wayoyi 45 Daga Hannun Wata Kungiyar Barayi

‘Yansanda Sun Kama Mutum Hudu Da Ake Zargi Da Aikata Muggan Laifuka A Yobe

Wadanda aka damke ake kuma zargi da hannu a ciki sun hada da Shuaibu Yahaya Liman mai shekaru 35; Monday Audu, mai shekara 33; da kuma Linus Samuel mai shekaru 42.

A Abuja kuma jami’an NDLEA sun kama wasu biyu, Jibrin Shuaibu mai shekaru 23 da Prosper Innih mai shekaru 17 a watan Fabrairu.

An kama wadanda ake zargin dauke da jakunkuna 169 da kuma kunshi-kunshi 80 na tabar wiwi mai nauyin kilogiram 1,961.5 da aka boye a cikin wata mota mai lamba ta Ogun WDE 557 DC.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Jami’an Tsaro Sun Kwato Wayoyi 45 Daga Hannun Wata Kungiyar Barayi
Kotu Da Ɗansanda

Jami’an Tsaro Sun Kwato Wayoyi 45 Daga Hannun Wata Kungiyar Barayi

October 4, 2025
‘Yansanda Sun Ceto Mutum 21 Da Aka Sace, Sun Kwato N4.8m Kuɗin Fansa
Kotu Da Ɗansanda

‘Yansanda Sun Kama Mutum Hudu Da Ake Zargi Da Aikata Muggan Laifuka A Yobe

October 4, 2025
Yaki Da Miyagun Kwayoyi: Kamfanin LEADERSHIP Da NDLEA Sun Kulla Kawance
Kotu Da Ɗansanda

NDLEA Ta Farmaki Masu Safarar Muggan Kwayoyi A Sassan Nijeriya

September 27, 2025
Next Post
‘Yansanda Sun Kama Mutumin Da Ya Kashe Matarsa A Adamawa

‘Yan Bindiga Sun Sace Gami Da Kashe Wani Lauya

LABARAI MASU NASABA

Aikin Jinya Kyauta: Gwamnatin Zamfara Ta Kammala Zagaye Na 10 Na Kula Da Marasa Lafiya 3,447

Aikin Jinya Kyauta: Gwamnatin Zamfara Ta Kammala Zagaye Na 10 Na Kula Da Marasa Lafiya 3,447

October 21, 2025
Ci Gaban Kasar Sin Ya Shaida Cewa Yawan Jama’a Ba Dalili Ne Na Rashin Ci Gaba Ba

Ci Gaban Kasar Sin Ya Shaida Cewa Yawan Jama’a Ba Dalili Ne Na Rashin Ci Gaba Ba

October 21, 2025
Mauludi: Gwamnatin Kano Ta Sake Ɗage Ranar Komawa Makarantu

Gwamna Yusuf Ya Buƙaci Hukumar NBC Da Ta Sa Ido Kan Gidajen Rediyo Da Talabijin Na Yanar Gizo

October 21, 2025
Me Aka Gano Kan Makomar Tattalin Arzikin Kasar Sin Daga Karuwar 5.2% Na Tattalin Arzikinta?

Me Aka Gano Kan Makomar Tattalin Arzikin Kasar Sin Daga Karuwar 5.2% Na Tattalin Arzikinta?

October 21, 2025
Sabbin Ministoci

Majalisa Ta Tabbatar Da Yusuf A Matsayin Sabon Shugaban NPC, Wasu 2 A Matsayin Kwamishinoni

October 21, 2025
Jirgin Kasa Mafi Saurin Gudu A Duniya Ya Fara Zirga-Zirgar Gwaji A Sin

Jirgin Kasa Mafi Saurin Gudu A Duniya Ya Fara Zirga-Zirgar Gwaji A Sin

October 21, 2025
Uba Sani Ya Amince Da Biyan Naira Biliyan ₦2.3 Ga Tsofaffin Ma’aikata Da Iyalansu

Ma’aikatan Manyan Makarantu Na Kaduna Sun Dakatar Da Yajin Aiki Yayin Da Gwamna Sani Ya Amince Da Sabon Tsarin Albashi

October 21, 2025
Jami’an Kasashen Afrika Na Koyon Dabarar Yaki Da Talauci Ta Sin A Jihar Ningxia

Jami’an Kasashen Afrika Na Koyon Dabarar Yaki Da Talauci Ta Sin A Jihar Ningxia

October 21, 2025
Da Ɗumi-ɗumi: Wata Tankar Mai Ta Sake Fashewa A Neja

Da Ɗumi-ɗumi: Fashewar Tankar Man Fetur Ta Yi Ajalin Rayuka 30 A Neja

October 21, 2025
Sin Ta Bayar Da Tallafin Dala Miliyan 3.5 Ga Shirin Samar Da Abinci A Zambia

Sin Ta Bayar Da Tallafin Dala Miliyan 3.5 Ga Shirin Samar Da Abinci A Zambia

October 21, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.