ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

NNPP Ta Jaddada Shirinta Na Gudanar Da Taron Jam’iyya Saɓanin Umarnin Kotu Da INEC

by Muhammad
5 months ago

Jam’iyyar NNPP ta bayyana cewa za ta ci gaba da gudanar da tarurrukanta na jam’iyya, duk da rikicin da ke tattare da bin umarnin kotu da Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC).

Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da wanda ya kafa jam’iyyar, Boniface Aniebonam, ya fitar a ranar Asabar a Lagos.

Aniebonam ya ce jam’iyyar ta riga ta miƙa jadawalin shirinta na gudanar da tarukan jam’iyya, zaɓen fidda gwani da babban taron ƙasa ga INEC, kuma za ta shiga dukkan zaɓuɓɓuka, ciki har da na shugaban ƙasa a 2027.

ADVERTISEMENT

Ya zargi INEC da jinkirta saka sunayen shugabannin kwamitin gudanarwa na ƙasa (NWC) na jam’iyyar da Dr Agbo Major ke jagoranta, duk da umarnin kotu.

A cewarsa: “Jinkirin da INEC ke yi wajen bin umarnin kotu, da kuma rikicin shugabanci da ya daɗe yana gudana a kotu, sun hana NNPP da mambobinta damar shiga wasu zaɓuɓɓuka a faɗin ƙasa.”

LABARAI MASU NASABA

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi

Ya ƙara da cewa saboda haka ne suka yanke shawarar ci gaba da gudanar da tarukan jam’iyya da babban taron ƙasa, yayin da suke jiran INEC ta bi umarnin kotu.

“Ba za mu ci gaba da hana mambobinmu damar shiga zaɓe a Nijeriya ba. Zaɓen 2027 babban zaɓe ne, kuma lokaci na tafiya, dole ne mu shirya tun da wuri,” in ji shi.

Aniebonam ya jaddada cewa jam’iyyar ba za ta daina fafutukar ganin INEC ta sabunta bayananta tare da amincewa da shugabancin Dr Agbo Major ba.

Ya ce sun yi tsammanin INEC za ta bi umarnin kotu, amma hakan bai faru ba, lamarin da ya sa suka nemi tattaunawa da hukumar domin fahimtar dalilin rashin bin umarnin kotu.

Ya kuma jaddada cewa umarnin kotu ya fi ƙarfin duk wani mataki ko hukunci da INEC za ta ɗauka, har ma da matakan ladabtarwa na cikin gida na jam’iyya.

A ƙarshe, ya kawo misalai na baya da suka nuna yadda rashin bin umarnin kotu ya taɓa haifar da matsaloli a harkokin zaɓe a Nijeriya.

Muhammad
+ postsBio
  • Muhammad
    Yadda Na Tsira Daga Cutar Mashaƙo A Katsina: “Na Fara Da Tsartuwar Jini Tare Da Yawu”
  • Muhammad
    An Naɗa Yusuf Nasidi Nasir A Matsayin Talban Barayan Kano
  • Muhammad
    Wani Kamfani Ya Tallafa Wa Masu Sana’ar Shayi A Kano
  • Muhammad
    Kosan Waka Ya Rasu, Gwamnan Kano Ya Jajanta Wa Iyalansa

MASU ALAKA

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027
Siyasa

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi
Manyan Labarai

2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi

September 8, 2026
Siyasa

Muna Da Yan Takarar Gwamna A Jihohi 28 Don Shiga Zaben 2027

September 6, 2026
Next Post
Wace Dama Ce Ta Ragewa Arsenal?

Wace Dama Ce Ta Ragewa Arsenal?

LABARAI MASU NASABA

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

September 9, 2026
Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.