Ministan Tsaron Nijeriya, Janar Christopher Musa mai ritaya, ya ce girman dazuzzukan da ‘yan ta’adda ke amfani da su na daga cikin abubuwan da ke sanya ayyukan jami’an tsaro wajen yaƙar ta’addanci da ceto waɗanda aka yi garkuwa da su cikin wahala.
Musa ya bayyana cewa Dajin Sambisa yana da faɗin kusan murabba’in kilomita 923, yana mai kwatanta girmansa da ƙasar Belgium. Ya ce irin wannan faɗin fili yana sa gano maɓoyar ‘yan ta’adda da bibiyarsu cikin sauki ya zama babban ƙalubale ga jami’an tsaro.
Ministan ya ce a lokutan da aka yi garkuwa da mutane, ‘yan ta’adda kan shiga cikin dazuzzuka kafin jami’an tsaro su samu cikakken bayani kan inda suke. Hakan na buƙatar lokaci da dabarun tattara bayanan sirri kafin a iya gano inda suke da kuma kai musu farmaki.
Ya kuma bayyana cewa jami’an tsaro na samun nasarar ceto wasu daga cikin mutanen da aka yi garkuwa da su ta hanyar katange hanyoyin da ‘yan ta’addan ke bi, tare da hana su samun muhimman abubuwan buƙata. A cewarsa, matsin lamba kan ‘yan ta’addan kan tilasta musu barin waɗanda suka yi garkuwa da su yayin da suke ƙoƙarin tserewa.
Musa ya ce gwamnati da jami’an tsaro na ci gaba da ƙoƙarin magance matsalar tsaro, amma ya buƙaci a fahimci girman yankunan da ake gudanar da ayyukan soji da kuma irin ƙalubalen da jami’an ke fuskanta wajen bibiyar ƙungiyoyin ‘yan ta’adda a cikin dazuzzuka.














