ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, June 24, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Rikicin Shugabanci Ya Rarraba Kan ‘Yan Kungiyar ACF

by Sulaiman and Sani Anwar
2 months ago
ACF

Kungiyar tuntuba ta Arewa (ACF), ta tsunduma cikin rikicin shugabanci da kuma zargin karkatar da kudade, a cewar rahoton Daily Trust.

Rikicin shugabancin, wanda har ya kai ga dara kungiyar gida biyu, ya ta’allaka ne a kan ayyukan kwamitin amintattu (BoT), da na kwamitin zartarwa na kasa dangane da harkokin yau da kullum na kungiyar.

A hannu guda kuma, shugaban kungiyar, Alhaji Bashir Dalhatu, tare da goyon bayan irin su Janar Haliru Akilu (mai ritaya), da dai sauransu, sun bukaci wasu mambobin kungiyar kwamitin amintattu da na kwamitin zartarwa na kasa, wadanda aka ce wa’adinsu ya cika, da su bar ofishinsu.

ADVERTISEMENT

Dalhatu, wanda shi ne Wazirin Dutse a Jihar Jigawa, ya taba rike mukamin Ministan Sufuri da Jiragen Sama a shekarar 1993, a lokacin gwamnatin rikon kwarya ta kasa, ta Cif Ernest Shonekan. Ya kuma rike mukamin ministan wuta da karafa daga 1993 zuwa 1997, sannan ya rike ministan harkokin cikin gida daga 1997 zuwa 1998, a lokacin mulkin Janar Sani Abacha.

A daya bangaren kuma, babban sakataren kungiyar, Malam Murtala Aliyu, wanda yana daya daga cikin wadanda aka bukaci da su tafi, ya ce; wa’adinsa zai kare ne a watan Disamba, ba yanzu ba.

LABARAI MASU NASABA

An Nemi Shugabanni Su Rungumi Tafarkin Adalci A Tsakanin Al’ummunsu

Ƴan Bindiga Sun Tilasta Wa Ƙauyukan Sakkwato Biyan Sabon Haraji

Rahotanni sun bayyana cewa, yana samun goyon bayan wasu mambobin da suka hada da shugaban hukumar zabe, Barista Mamman Mike Osuman, SAN; mai magana da yawun Farfesa Tukur Baba, da dai sauransu.

An kafa kungiyar ACF a shekara ta 2000, kungiyar al’adu da zamantakewa da ta fito daga jihohin Arewa 19, tana kokarin kare muradun Arewacin Nijeriya.

Daga cikin sauran, manufarta ita ce; inganta hadin kai, zaman lafiya da ci gaban tattalin arziki a fadin Arewa, tare da bayar da shawarwari a kan muradun siyasa da tsaro na yankin a cikin tarayyar Nijeriya. Har ila yau, dandalin ya zama wani dandalin tattaunawa tsakanin shugabannin Arewa.

Duk da cewa, an dade ana samun sabani a cikin kungiyar dangane da ayyukan da ke cikin kungiyar, lamarin ya kara fitowa fili jim kadan bayan cika shekaru 25 da kafa kungiyar ta ACF.

Majiya mai tushe daga cikin ACF ta shaida wa jaridar Daily Trust cewa; wasu makudan kudade kimanin naira biliyan 3.9 da aka bai wa kungiyar a cikin wani sabon asusu na bankin JAIZ, maimakon a cikin wani babban asusun kungiyar na First Bank da UBA da Unity Bank, ya haifar da rashin jituwa a tsakanin mambobin kungiyar.

Idan dai za a iya tunawa, an samu wani asusun bayar da tallafi a yayin bikin cika shekara 25 da kafa kungiyar ta ACF a watan Nuwambar 2025, inda wasu fitattun shugabanni da ’yan kasuwar Arewa suka bayar da gudunmawar sama da Naira biliyan 3.9, baya ga alkawuran da har yanzu ba a kai ga biya ba.

Bayan haka, akwai kuma kusan naira miliyan 700 da wasu shugabannin Arewa suka bayar, domin shirya bikin cika shekara 25. Ana ta tambayar cikakkun bayanai kan yadda aka yi amfani da kudaden.

Da aka tambayi Bukar Zarma da Janar Akilu, Murtala Aliyu daga wakilin Daily trust ya bayyana cewa; a wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, 1 ga watan Mayu, Janar Akilu, wanda kuma mamba ne a kungiyar kwamitin amintattu, kuma shugaban kwamitin zaben shugabannin kungiyar ta ACF, ya ce; sun mika shawarwarin da suka shafi karewar wa’adin wasu manyan jami’ai da kuma cike guraben da aka samu.

Ya ce, a cikin wata takarda mai dauke da kwanan watan 23 ga Afrilun 2026, kwamitin amintattu (BoT) ta bayyana cewa; mambobin kungiyar sun tattauna kan wa’adin wasu jami’an kungiyar.

Janar Akilu ya kara da cewa, bayan taron, an yanke shawarar cewa; bisa ga kundin tsarin mulkin ACF, shugabannin kwamitin amintattu (BoT), su fitar da wa’adi guda na shekara shida, yayin da shugabannin hukumar za su yi wa’adin shekara uku, wanda za a sabunta su na tsawon shekara uku.

Har ila yau, ya ci gaba da cewa, wa’adin jami’an da suka fara aiki a ranar 10 ga Maris, 2020, kuma suka kammala wa’adinsu na shekara shida a ranar 10 ga Maris, 2026 ya kare.

Wadanda abin ya shafa, a cewarsa, sun hada da mataimakin shugaban kwamitin amintattu (BoT), Sanata Fred Orti daga Jihar Benue; Mataimakin shugaban kwamitin na amintattu (BoT), Amb. Ibrahim Mai Sule daga Jihar Yobe; mataimakin shugaban hukumar zabe, kuma Wazirin Katsina, Sanata Ibrahim Ida; da Babban Sakatare, Murtala Aliyu.

A cewar Janar Akilu, “Kwamitin ya lura cewa, yanzu an sauke masu wadannan mukamai, an kuma bai wa Mallam Murtala Aliyu, har zuwa ranar Juma’a 15 ga watan Mayun 2026, domin ya kammala takardar mika mulki da sauran tsare-tsaren tafiyarsu.

Ya ci gaba da cewa, kwamitin tantancewar ya dauki wasu matakai da suka hada da samar da bayanai na masu son tsayawa takarar mukamai hudu da babu kowa a kai.

“In ban da mukamin babban sakatare, an dage zabe da nada sauran mukamai guda uku, har sai an kammala sake duba kundin tsarin mulkin na ACF,” in ji shi.

A cewar Janar Akilu, “A bangaren rikon kwarya, an nada babban sakatare, domin tabbatar da gudanar da harkokin yau da kullum cikin sauki, inda aka nada Mallam Bukar Zarma a matsayin babban sakatare na riko, nadin nasa zai kare ne bayan nada wani sabon babban sakataren.

“Ni dai na zama babban sakatare, Murtala Aliyu.

Sai dai, da aka tambaye shi dalilin da ya sa aka ware shi a kan wasu, Murtala Aliyu ya ce; wa’adin babban sakataren ba wa’adi ba ne kai tsaye na tsawon shekaru shida kamar na mambobin kungiyar kwamitin amintattu (BoT) ba.

Ya ce, ‘yan kwamitin amintattu na da wa’adin shekara shida, yayin da mambobin kuungiyar da ya kamata su yi shekara uku, suna da damar yin wasu shekaru ukun.

Murtala ya kara da cewa, bayan sun kammala shekara uku na farko a matsayin mambobin kungiyar da aka zaba, shi da mataimakin shugaban, Sanata Ibrahim Ida an sake zabarsu na tsawon shekara uku.

Babu Jituwa Tsakanin Shugaban Zartarwa Na Kasa Da Shugaban Kwamitin Amintattu

Daily trust ta ruwaito cewa, ‘yan mintoci kadan bayan sanarwa daga shugaban kwamitin amintattu (BoT), Alhaji Dalhatu, sai ga shugaban zartawa na kasa, Barista Osuman, ya sake fitar da wata sanarwar, inda ya jaddada cewa; taron na Kaduna zai gudana ne kamar yadda aka tsara.

Sanarwar ta ce, “Ni a matsayina na shugaban zartarwa na kasa (NEC), na bayar da umarci gabatar da taron majalisar zartarwa na kasa (NEC) a ranar Laraba 6 ga Mayun 2026. A cikin wannan umarni na fake a karkashin sashe na 13 karamin sashe na 1 (a) , (b) , (c) & (d) na kundin tsarin mulkin ACF.

“Sashe na 13 da karamin sashe na 1 (a) ya bayyana tasirin da shugaban yake da shi kamar haka:

“Kiran dukkanin tarukan majalisar zartarwa ta kasa da kwamitin aiki.

“Don haka ne ya sa na ba da umarnin a aika sanarwa ga mambobin ta hanyar dandalin namu, domin sanar da taron shugabannin zartarwa da za a gudanar a ranar Laraba 6 ga Afrilun 2026, a hedikwatarmu ta Kaduna mai lamba 11 A a titin Sokoto Road. Abin mamaki a cewar Bashir Dalhatu, sai ga shugaban kwamitin amintattu (BoT), da kansa ya umarci membobin kungiyar ta ACF da su yi watsi da wannan.

Zargin karkatar da kudade zuwa wani asusu daban,

Daily trust ta ruwaito cewa; baya ga rashin fahimtar da shugabannin kungiyar ta ACF suka samu, wasu mambobin kungiyar sun tada hankalinsu kan yadda ake ajiye kudaden da aka samu a lokacin gudanar da ayyukan ba da tallafi a asusun bankin Jaiz, maimakon asusun ajiyar da aka sani na kungiyarACF.

Ya zuwa yanzu dai, sama da naira biliyan 3.9 ne kungiyar ta ACF ta samu, sai dai wasu ‘yan kungiyar sun ce; suna son a yi karin haske kan inda aka ajiye kudaden da kuma abin da jami’an suke da niyyar yi da su.

Wadanda ake binciken, sun hada da shugaban kwamitin amintattu (BoT, Bashir Dalhatu da Sakatare Janar, Murtala Aliyu.

Aliyu ya tabbatar a wata hira da ya yi cewa, lallai an bude wani asusu na daban a bankin Jaiz, amma kuma ya yi mamakin dalilin da ya sa aka mayar da kudaden zuwa bankin Jaiz da ke Kano.

Haka zalika, ya yarda da cewa; shi da Dalhatu ne suka sanya hannu kan wasikar da ta umarci bankin Jaiz ya bude asusun na ACF. Wannan shi ne lokacin da ya tambayi lokacin da aka bude sabon asusun.

“Abin da ke faruwa shi ne, babu yadda za a yi a ce; shugaban kwamitin amintattu (BoT), bai kamata ya kasance cikin wadanda za su sanya hannu a kan asusun kungiya ba.

“Shugaban kwamitin amintattu (BoT) ne ya sa aka mayar da asusun Kano, maimakon wurin da aka saba yi a Kaduna, don haka ina ganin wannan ne ya sa ake ta cece-kuce, amma kawo yanzu babu wani kudi da ya bata.”

A cewarsa, “naira biliyan 2.5 aka mayar asusun da aka saka hannun jari, sannan wadanda suka rattaba hannu a kai su ne shugaban kwamitin amintattu da ni kaina.

“Amma daga baya, shi (shugaban kwamitin amintattu), shi ne ya mayar da naira biliyan 1.4, ba tare da sa hannun wani ba, shi ya sa abin yake damunsa, amma ko sisin kwabo bai bata ba,” in ji shi.

Da aka tambaye shi dalilin da ya sa ba su ajiye kudaden a asusun da suke da su ba, sai ya ce; abin da ake nufi shi ne su ajiye kudaden tallafi daban.

“An bude asusun bankin Jaiz ne, musamman domin adana tarin kudaden tallafin da ake da su,” in ji shi.

ACF
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Ya Kamata Sin Da Birtaniya Su Yi Aiki Tare Don Ci Gaba Da Inganta Dangantakarsu
  • Sulaiman
    Firaministan Sin Ya Jaddada Muhimmancin Kara Azamar Bunkasa Kirar Kayayyakin Aikin Masana’antu Na Zamani
  • Sulaiman
    Gombe Ta Zabge Farashin Taki Da Kashi 50 Cikin 100
  • Sulaiman
    Wang Yi Ya Gana Da Babban Sakataren Majalisar Tsaron Masar Da Ministan Fadar Gwamnatin Afirka Ta Kudu A Indiya
ACF
Sani Anwar
+ posts Bio
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Tattalin Arziƙin Ƙasa: Masana Sun Buƙaci Tinubu Ya Yi Hattara Da Shawarar IMF
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Cututtukan Da Aka Fi Fama Da Su Lokacin Damina Da Yadda Za A Kauce Musu (2)
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Cututtukan Da Aka Fi Fama Da Su Lokacin Damina Da Yadda Za A Kauce Musu (1)
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Talauci Ya Sake Karuwa Da Kashi 63 Duk Da Sauye-sauyen Tattalin Arzikin Da Gwamnati Ta Yi – IMF

MASU ALAKA

Nijeriya
Rahotonni

An Nemi Shugabanni Su Rungumi Tafarkin Adalci A Tsakanin Al’ummunsu

June 20, 2026
Ambaliyar Ruwa Ta Lalata Gidaje 14,940 A Sokoto
Rahotonni

Ƴan Bindiga Sun Tilasta Wa Ƙauyukan Sakkwato Biyan Sabon Haraji

June 20, 2026
IMF
Rahotonni

Tattalin Arziƙin Ƙasa: Masana Sun Buƙaci Tinubu Ya Yi Hattara Da Shawarar IMF

June 20, 2026
Next Post
Jamhuriyar Nijar Ta Dakatar Da Kafafen Yaɗa Labarai 10

Jamhuriyar Nijar Ta Dakatar Da Kafafen Yaɗa Labarai 10

Discussion about this post

LABARAI MASU NASABA

An Kashe Mutum 2, 8 Sun Jikkata Yayin Rikici A Bauchi

An Kashe Mutum 2, 8 Sun Jikkata Yayin Rikici A Bauchi

June 24, 2026
Tsohon Shugaban APC Na Kebbi Ya Rasu A Hannun ’Yan Bindiga

Tsohon Shugaban APC Na Kebbi Ya Rasu A Hannun ’Yan Bindiga

June 24, 2026
Ya Kamata Sin Da Birtaniya Su Yi Aiki Tare Don Ci Gaba Da Inganta Dangantakarsu

Ya Kamata Sin Da Birtaniya Su Yi Aiki Tare Don Ci Gaba Da Inganta Dangantakarsu

June 23, 2026
Firaministan Sin Ya Jaddada Muhimmancin Kara Azamar Bunkasa Kirar Kayayyakin Aikin Masana’antu Na Zamani

Firaministan Sin Ya Jaddada Muhimmancin Kara Azamar Bunkasa Kirar Kayayyakin Aikin Masana’antu Na Zamani

June 23, 2026
Gombe Ta Zabge Farashin Taki Da Kashi 50 Cikin 100

Gombe Ta Zabge Farashin Taki Da Kashi 50 Cikin 100

June 23, 2026
Wang Yi Ya Gana Da Babban Sakataren Majalisar Tsaron Masar Da Ministan Fadar Gwamnatin Afirka Ta Kudu A Indiya

Wang Yi Ya Gana Da Babban Sakataren Majalisar Tsaron Masar Da Ministan Fadar Gwamnatin Afirka Ta Kudu A Indiya

June 23, 2026
‘Yansanda Sun Kashe Masu Garkuwa Da Mutane 8, Sun Kubutar Da Mutane 3 A Jihar Bauchi

’Yansanda Sun Kama Mutane 57 Da Ake Zargi Da Ayyukan Ta’addanci A Adamawa

June 23, 2026
Li Qiang Ya Gana Da Firaministan Kasar Guinea

Li Qiang Ya Gana Da Firaministan Kasar Guinea

June 23, 2026
Maniyyatan Nijeriya

Hajjin 2026: NAHCON Ta Kammala Jigilar Alhazan Nijeriya Daga Saudiyya

June 23, 2026
Kamfanin Sin Ya Kammala Babban Aikin Samar Da Ruwa A Babban Birnin Nijeriya

Kamfanin Sin Ya Kammala Babban Aikin Samar Da Ruwa A Babban Birnin Nijeriya

June 23, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.