ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sabon Nau’in Zakara Na ‘MoorBeta’ Zai Ƙara Haɓaka Fannin Kiwon Kaji

by Abubakar Sulaiman
5 months ago
Zakara

A makon da ya gabata ne, a hukumance aka ƙyanƙashe wani sabon nau’in Zakara tare da yi masa rijista, wanda ake kira da ‘MoorBeta’.

Har ila yau, an bayyana cewa; wannan nau’i na da ɗauke da wasu manyan abubuwa da masu kiwonsa za su amfana da su.

An dai sanar da wannan sabon nau’i ne a wani taro karo na 36 da kwamitin ƙasa na jinsin dabbobi (NACGRAB), ya gudanar.

ADVERTISEMENT

Shugaban kwamtin, Farfesa Soji Olufajo ne ya jagoranci taron, wanda ya gudana a garin Ibadan.

  • Manoma Da Dama Za Su Yi Watsi Da Fannin Noma A Taraba A 2026 -AFAN
  • Yadda Masu Kwace Suka Yanke Wa Malamin Makaranta Hannu A Kano

Wata tawagar gudanarwa daga cibiyar bincike da bayar da horo kan lafiyar kaji da kula da aikin noma ta ƙasa (IAR&T) ce, ta sanya ido kan ƙyanƙyasar nau’in na ‘MoorBeta’.

LABARAI MASU NASABA

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

An dai samar da wannan nau’i ne, saboda ƙananan masu kiwon kaji, wanda kuma za a iya kiwata nau’in a kowane irin yanayi na ƙasar.

A cikin mako goma kacal, zakaran na ‘MoorBeta’, nauyinsa zai iya kai wa kimanin kilo 2.8, musamman idan ana ciyar da shi abinci yadda ya kamata.

An fi samun mai farin gashi ko mai ɗauke da gaurayen ruwan ƙasa ko baƙi ko kuma ja, wanda kuma ya kasance yana da girma, inda ake samun nama mai yawa tare da shi.

Bisa fashin baƙin da aka yi a 2025 na ribar da ake samu daga kiwon nau’in na ‘MoorBeta’, musamman wanda ya kiwata guda 100, zai iya samun ribar da ta kai ta kimanin naira 278,000, a cikin mako goma kacal.

Ma’aikatar Bunƙasa Kiwon Dabbobi, ta yi maraba da wannan nau’in, wanda ta alaƙanta a matsayin wanda zai ƙara tallafawa, wajen samar da nama a ƙasar.

A cikin sanarwar da ma’aikatar ta fitar ta ce, za ta ci gaba da yin aiki kafaɗa da kafaɗa da cibiyoyin binciken, musamman domin a ƙara samar da nama da kuma ƙara ƙarfafa samar da kuɗaɗen shiga ga masu kiwata irin wannan nau’in.

Kazalika, kwamitin ƙasa na tantance nau’ika wato NƁRC, a wani taron da ya gudanar a a garin Ibadan, ya fitar da wani nau’ikan masara biyu da ake kira da ‘ARTPOP 001’ da kuma ‘ARTPOP 002’ wanda cibiyar NACGRAB, ta ƙirƙiro da su.

A cewar cibiyar, waɗannan nau’ikan biyu na zakaran da kuma na masarar, za su taimaka wajen ƙara samar da wadataccen abinci a ƙasar.

Ta ƙara da cewa, wannan babban ci gaban da aka samar, ya nuna a zahiri na irin mayar da hankali da cibiyar ke ci gaba da yi, wajen bunƙasa fannin gudanar da bincike tare kuma da nufin ƙara haɓaka fannin noma na manoman da ke ɗaukacin faɗin ƙasar nan baki-ɗaya.

Wannan sabon nau’in na masara, an samar da shi ne bisa jaroranci tawagar masu bincike a cibiyar da Farfesa D. J. Ogunniyan, tare da shugaban sashen shirin haɓaka fannin noman Masara J. O. Olasoji, da kuma shugaban sashen samar da ‘yaƴan Itatuwa Farfesa. O. F. Owolade, suka jagoranta.

Shin Ina Batun Nau’in Kajin ShikaBrown Da Cibiyar Bincke Ta Shika Ta Ƙirƙiro Da Su?

A kwanakin baya, cibiyar gudanar da binciken lafiyar dabbobi da ke garin Shika a Ƙaramar Hukumar Zaria, wato NAPRI ta ƙirƙiro da wani nau’in Kaji da ake kira da ‘ShikaBrown chicken’.

Sai dai, duk da irin muhimmancin da wannan nau’i yake da shi, musamman domin ƙara bunƙasa tattalin arziƙin masu kiwon kaji da ke wannan ƙasa, musamman ƙananan masu kiwon kajin, ya kasance ba sa iya samun wannan nau’i a cikin sauƙi.

Amma, bisa uzurin da cibiyar ta NAPRI ta bayar kan wannan ƙalubale, ta bayyana cewa; rashin samar da wadatatun kuɗaɗe ne, suka sanya ba ta iya samar da wadataccen wannan nau’i a Nijeriya, musamman ga ƙananan masu kiwon kaji.

Kazalika, masu ruwa da tsaki a fannin kiwon kaji a ƙasar nan, na ci gaba da bayyana fargabarsu, kan ɗorewar wannan sabon nau’i na MoorBeta a ƙasar nan. musamman yadda rashin samar da wadatatun kuɗaɗe ga ɗimbin cibiyoyin gudanar da binciken da ake da su a ƙasar.

Zakara
Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    Iyalin El-Rufai Sun Bai Ministan Tsaro Wa’adin Kwana 7 Kan Zargin Rikicin Kudancin Kaduna
  • Abubakar Sulaiman
    Atiku Ya Zargi Gwamnatin Tarayya Da Cin Bashi Kamar Mashayin Da Kuɗi Ya Ƙarewa
  • Abubakar Sulaiman
    Boko Haram Ta Kai Hari Adamawa, Ana Fargabar Mutuwar Mutane 11
  • Abubakar Sulaiman
    Ƴan Bindiga Sun Kai Hari Sokoto, Sun Kashe Mutane 7, Sun Yi Garkuwa Da 12

MASU ALAKA

'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina
Labarai

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare
Labarai

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Next Post
Sirrin Kasancewar Mu Shekara Fiye Da 40 A Matsayin Mata Da Miji”

Sirrin Kasancewar Mu Shekara Fiye Da 40 A Matsayin Mata Da Miji”

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.