ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sadakin Budurwa ₦3,000 Na Bazawara ₦1,500: Gwamnatin Bauchi Ta Ƙaryata Batun

by Sulaiman and Khalid Idris Doya
2 months ago
Bala Mohammed

Gwamnatin Jihar Bauchi ta bayyana wani bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta, wanda ke iƙirarin cewa Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed ya amince da kayyade sadakin Zawarawa zuwa naira 1,500, a matsayin ƙarya tsagwaronta da wasu suka ƙirƙiro domin sanya ruɗani a zukatan al’umman jihar.

Bidiyon, wanda ya bazu sosai a shafukan Facebook da TikTok, ya kuma yi zargin cewa Sarkin Sayawa (Gum Zar) ya umarci al’ummar yankin da su bi wannan sabuwar tsarin da gwamnati ta ɓullo da shi.Haka kuma, wani mai amfani da kafar sada zumunta mai suna Boroh James Hussaini ya wallafa cewa sadakin budurwa da ta taɓa haihuwa ba tare da aure ba zai kasance Naira 3,000, yayin da matan da suka daɗe ba su yi aure ba kuma ba su taɓa haihuwa ba za a aurar da su ga direbobi ba tare da an biya sadaki ba.

Da ya ke ƙaryata batun yayin ganawa da manema labarai a Bauchi ranar Asabar, Kwamishinan kula da harƙoƙin addini, Injiniya Muhammad Binni Abdulkadir, ya bayyana waɗannan iƙirari a matsayin ƙirƙirarru, marasa tushe balle makama kuma karya ce gaba ɗaya.

ADVERTISEMENT

Ya jaddada cewa Gwamnatin Jihar Bauchi ba ta taɓa ƙirƙirar ko amincewa da wata manufa da ta shafi kayyade sadakin matan da aka sake su ko kuma mata marasa aure ba, yana mai cewa an ƙirƙiri waɗannan rahotanni ne da gangan domin ruɗar da jama’a.

Kwamishinan ya buƙaci al’ummar jihar da su yi watsi da waɗannan jita-jita, tare da gujewa yaɗawa ko kambama bayanan da ba a tantance ba, domin hakan na iya haifar da ruɗani da tashin hankali ba tare da wani dalili ba.

LABARAI MASU NASABA

Jerin Bankuna 32 Da Aka Amince Su Sayar Da Hannun Jarin Matatar Dangote

Uganda Za Ta Fara Fitar Da Man Fetur Zuwa Ƙasashen Waje

Ya ƙara da cewa tun daga lokacin da ya hau mulki, Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed ya kasance mai mutunta koyarwar addini, al’adun gargajiya da kyawawan ɗabi’un al’ummar Jihar Bauchi.

Injiniya Binni ya kuma yi kira ga jama’a da su tabbatar da sahihancin duk wani bayani kafin su yaɗa shi a kafafen sada zumunta, yana gargaɗin cewa yaɗa labaran ƙarya na iya yin illa ga zaman lafiya, haɗin kai da martabar Jihar Bauchi, tare da lalata kyawawan al’adunta da gadon addininta.

Sadaki
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna
  • Sulaiman
    Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba
  • Sulaiman
    Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa
  • Sulaiman
    Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina Kasa
Sadaki
Khalid Idris Doya
+ posts Bio
  • Khalid Idris Doya
    https://hausa.leadership.ng/author/khalid-idris-doya/
    PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi
  • Khalid Idris Doya
    https://hausa.leadership.ng/author/khalid-idris-doya/
    Yaro Ya Harbe Kansa Har Lahira Bayan Mafarauci Ya Yi Sakaci Da Bindigarsa A Bauchi
  • Khalid Idris Doya
    https://hausa.leadership.ng/author/khalid-idris-doya/
    An Kama Mutane 5 Da Sassan Jikin Ɗan’Adam Za Su Yi Tsafi A Bauchi
  • Khalid Idris Doya
    https://hausa.leadership.ng/author/khalid-idris-doya/
    Tsohon Mai Neman Takarar Gwamnan Bauchi, Bala Jibrin, Ya Fice Daga APC Kan Zargin Ɗoki-ɗora

MASU ALAKA

Sadaki
Labarai

Jerin Bankuna 32 Da Aka Amince Su Sayar Da Hannun Jarin Matatar Dangote

September 10, 2026
Sadaki
Labarai

Uganda Za Ta Fara Fitar Da Man Fetur Zuwa Ƙasashen Waje

September 10, 2026
Cutar Mashaƙo Ta Ɓarke A Kano, Katsina Da Filato
Manyan Labarai

Mashaƙo: Adadin Mutanen Da Suka Rasu Sun Kai 27 A Filato

September 10, 2026
Next Post
Sadaki

Ƴan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Alƙalin Babbar Kotu A Kebbi

LABARAI MASU NASABA

Sadaki

Jerin Bankuna 32 Da Aka Amince Su Sayar Da Hannun Jarin Matatar Dangote

September 10, 2026
Sadaki

Uganda Za Ta Fara Fitar Da Man Fetur Zuwa Ƙasashen Waje

September 10, 2026
Cutar Mashaƙo Ta Ɓarke A Kano, Katsina Da Filato

Mashaƙo: Adadin Mutanen Da Suka Rasu Sun Kai 27 A Filato

September 10, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

Wane Ne Dan Shagamu: Su Wane Ne Suka Kashe Shi A Kano?

September 10, 2026
Al’umma Sun Yaba Wa Sojoji Kan Yaƙar ’Yan Bindiga A Zamfara

Al’umma Sun Yaba Wa Sojoji Kan Yaƙar ’Yan Bindiga A Zamfara

September 10, 2026
Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

September 10, 2026
’Yansanda Sun Kama Wadda Ta Yaɗa Labarin OPay Zai Daina Aiki A Nijeriya

’Yansanda Sun Kama Wadda Ta Yaɗa Labarin OPay Zai Daina Aiki A Nijeriya

September 10, 2026
2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

September 10, 2026
Zabe: Gwamnatin Kano Ta Taƙaita Zirga-zirgar Mutane Da Ababen Hawa

Gwamna Yusuf Ya Umarci Jami’an Tsaro Su Gano Waɗanda Suka Kashe Danshagamu

September 10, 2026
Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

September 9, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.