Masana suna ta hasashen cewa Manchester City za ta iya fuskantar koma baya a kakar bana saboda tafiyar babban mai koyarwa Pep Guardiola, wanda ya ajiye aiki a ƙarshen kakar wasan da ta gabata, to amma hausawa na cewa mushen kura ya fi ƙarfin Allah sarki.
Tabbas ƙungiyar ta yi rashin shahararren mai horarwa amma ta maye gurbinsa da Enzo Maresca wanda ya gaza a tsohuwar ƙungiyarsa ta Chelsea. Ɗan wasanta da ke da matuƙar tasiri na tsakiya Bernardo Silɓa shi ma ya tafi a wannan kakar kuma ya zuwa yanzu ba ta sanar da ɗaukar wanda zai maye gurbinsa ba. Sannan shi ma ɗan wasa Rodri ya koma Barcelona a cikin wannan satin.
Amma kuma akwai ƴanwasa irinsu Erling Halaand da Semenyo da Foden da Doku da Diaz, suka suna nan tare da su ga Umar Marmoush. Sannan ƙungiyar ta sayi ɗan Ingila, Elliot Anderson, sannan tana dab da kammala cinikin Ayyuob Boaddy, ɗan Moroko.














