Shugaban Comoros, Azali Assoumani ya tsallake rijiya da baya a wani hari da aka kai masa a wajen wani taro da aka gudanar a ƙasar.
A ranar Juma’ar da ta gabata, fadar shugaban ƙasar Comoros ta bayar da rahoton cewa, an kai wa shugaba Azali Assoumani, harin, wanda aka nufin a soke shi da wuƙa a lokacin da yake halartar bikin jaje ga wani Sarki a ƙasar.
- Matatar Man Dangote: Za Mu Shigo Da Mai Idan Kudin Sufurinsa Ya Fi Sauki Daga Waje -IPMAN
- An Fara Amfani Da Kimiyya Da Fasaha Wajen Yaki Da Cutar Kyandar Biri
To, sai dai shugaban ya sha da kyar tare da samun ƙananan raunuka a yayin da aka kai masa harin.
Talla
A cewar sanarwar a hukumance, shugaba Assoumani ya koma gida, kuma ba tare da ɓata lokaci, sannan hukumomin tsaron kasar sun cafke wanda ya kai harin.
Talla