ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Tuesday, July 14, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Su Wa Suka Yi Wa NAHCON Baki?

by Bello Hamza and Sulaiman
5 months ago
NAHCON

Duk da kasancewa hukuma mai kula da aikin da ya shafi addini inda ake sa ran masu tafiyar da ita su kasance masu ilimin addini da kuma tsoron Allah, NAHCON ta kasance hukuma daya tilo a fadin tarayyar kasar nan da shugabannin ta ke fadawa cikin dambarwar badakalar almumdahana na kudadewn jama’a. Cikin shugabbani 5 da hukumar ta yi tun da aka kafa ta a shekarar 2015 dukkanin su sun sauka daga jagorancin hukumar ne tare da zargin wani nau’in badakala ko rashin iya tafiyar da aiki, babu wani daga cikin su daya kammala wa’adin shekara 4 da doka ta tanada wa shugaban hukuma.

Shugaban hukumar na baya-baya nan Farfesa Abdullahi Saleh Usman Pakistan ya sauka daga mukaminsa ne bayan takardar koke da mambobin hukumar gudanarwar Hukumar suka mika wa Shugaba Tinubu inda suka zarge shi da rashin iya gudanar da aiki da kuma bacewar kudade.

  • Ƴan Kasuwa 7 Sun ɓace, Asarar Dukiya Ta Haura Biliyan 5 A Gobarar Kasuwar Singa
  • An Yi Taron Share Fagen Shagalin CMG Na Murnar Shiga Sabuwar Shekarar gargajiyar Kasar Sin A Hedikwatar MDD Da Kasar Jamus

Idan za a iya tunawa bayan kammala aikin hajin bara ne hukumar EFCC ta gayyaci Pakistan domin ya amsa tare da wanke kansa daga wasu zarge-zarge na bacewar wasu kudade da kuma har zuwa yanzu EFCC ba ta kammala bincikenta a kan lamarin ba.

ADVERTISEMENT

Lamarin Farfersa Pakistan ya kara kamari ne inda a kwanakin baya shugabannin hukumomin aikin hajji na jihohi suka fitar da sanarwa inda suka nemi lallai sai Pakistan ya sauka domin take takensa suna barazana ga shirye-shiryen akin hajjin bana, amma bai aiwatar da bukatar tasu ba. Tun daga nan masu lura da al’amurran yau da kullum suka yi hasashen cewa, lokaci ne kawai ake jira na saukar Pakistan.

Wata majiya ta bayyana cewa, “fadar shugaban kasa ce ta tilasta masa ajiye aiki bayan korafe-korafe a kansa tun daga lokacin da aka nada shi, kuma fada shugababn kasa za ta sanar da wanda zai gaje shi nan da dadewa ba”

LABARAI MASU NASABA

Na Yi Tsayin-daka Domin Cika Alƙawarin Ƙasata Nijeriya

Mun Ɗauki Nauyin Karatun Masu Digiri Ta Hanyar Sayar Da Ƙosai Da Ƙuli-ƙuli —Wasu Ƴan Kasuwa

Bincike ya nuna cewa, a ranar 19 ga watan Janairu 2026 ne shugabannin hukumomomin akin hajji na jihohi 11 suka rubuta takardar korafi ga fadar shugaban kasa inda suka nuna rashin amincewar su ga Shugabancin Farfesa Pakistan, sun zargi Farfesa Pakistan da rashin iya tafiyar da harkokin kudi da bayar da kwangila ba tare da amincewar hukumomi ba da kuma zarce ka’idar kudaden da aka amince masa ya kashe a matsayinsa na shugaban hukumar.

Sun bayyana cewa, wadannan zarge zargen sun kara kamari ne ganin cewa, a halin yanzu Farfesa Pakistan na fuskantar bincike na musamnman a kan wasu badakalar da suka shafi aikin hajin bara daga hukumar EFCC.

A wata sanarwar da ya sa wa hannu, Farfesa Pakistan ya bayyana cewa, ya ajiye aiki ne a matsayin shugaban NAHCON a kan radin kansa bayan tattaunawa tare da tuntubar iyalai da makusantansa. Ya kuma mika godiyarsa ga Shugaba Tinubu a kan damar da ya bashi na jagorantar hukumar.

Bayani ya nuna cewa, kusan dukkan wadanda suka jagoranci NAHCON tun da aka kafa ta suna barin kujerar su ne ba tare da sun shirya ba, suna bari ne kuma da zarge-zargen badakalar kudade dana rashin iya gudanar da aiki, duk da cewa, ba a iya tabbatar da yawancin zarge-zargen ba, tun daga, Muhammad Musa Bello 2007 – 2015, Abdullahi Mukhtar Muhammad, 2015 – 2019, Zikrullah Kunle Hassan, 2020 – 2023 (dan kudu na farko da ya jagoranci hukumar), 4. Jalal Ahmad Arabi, 2023 – 2024, sai kuma Farfesa Abdullahi Saleh Usman, 2024 – 2026.

Dokar da ta kafa hukumar NAHCON (Establishment) Act, 2006), ta bayyana cewa, shugaban hukumar na da wa’adin shekara 4 kuma ana iya kara sabunta masa, amma duk da wannan babu wani daga cikin wadanda suka shugabannci hukumar da ya iya kammala wa’adinsa ba tare da fuskanci matsalolin da ke kai ga sallamar su ba, kuma matsalolin su kan shafi badakalar kudade ne da EFCC ke bincika.

A shekarar 2024 da Marubucin nan ya yi aikin hajji tare da tawagar ‘yan jarida daga NAHCON (Media Committee) a lokacin Jalal Ahmad Arabi ker shugabantar hukumar, tun daga kasa mai tsarki hukumar ta fara fuskantar koke-koke daga jami’an alhazai na jihohi a kan yadda ake ciyar da alhazan su da kuma yadda aka dakile wa alhazai kudaden guzurinsu, duk da cewa, NAHCON ta karyata wasu zarge-zargen, amma a lokacin ne gwamnan Jihar Neja, Mohammed Bago ya nermi a soke hukumar NAHCON a bar wa jihohi su jagoranci yadda alhazan jihohinsu za su kasance a kasa mai tsarki. Bayan dawowa gida, Gwamnan Bago ya je majalisar kasa inda ya nemi lallai su sa baki amma daga baya maganar ta lafa.

Lallai lokaci ya yi da ya kaamaka a duba wannan bukatar in har za a samu inganci a yadda a ke gudanar da harkokin aikin Hajji, domin daga dukkan alamu NAHCON na fuskantar wani irin baki ko kuma tsinuwa da ta yadda al’amurra suka kasa tafiya yadda ya kamata a hukumar.

Abin lura a nan shi ne ana samun zarge-zargen cutar da alhazai wadanda suka tattara kudadensu suka biya kudaden aikin hajji domn su gudanar da ibada, bayin Allah da ya kamata a taimaka musu amma a jikin su ake tatsa, kuma wadannan bayin Allah suna tsayawa a gaban Allah (SWT) a wurare masu tsarki, suna gabatar da addu’o’in Allah ya saka musu daga dukkan cutar da a ka yi musu, wannan ne ya sa ake tunanin ko addu’o’in da alhazan da aka cuta ta kama hukumar NAHCON, shi ya sa duk wanda ya hau baya gamawa lafiya?

Idan an bi ta barawo, ya kuma kamata a bi ta mabi sawu, abin da nake nufi a nan a na shi ne, ba wai sallamar shugabannin hukumar kada ya kamata a rinka yi ba, ya kamata a bincika tare da tabbatar an ladaftar da wasu manyan ma’aikatar hukumar musamman wadanda suka dade, daga dukkan alamu sune suke dora duk wani sabon shugaba da ya hau kan karaga hanyoyin tafi da hukumar.

A aikin hajjin shekarar 2024, Jalal Arabi ya dakile wa ma’aikatan hukumar da ‘yan jarida alawus alawus din su, irin wannnan yana da hatsarin gaske, musamman ganin irin addu’o’in da za su gabatar a wurare masu tsari na Allah ya bi musu hakkokinsu, wannan kuma ya kamata ya zama darasi ga shugaba mai kamawa, ‘Ka tabbatar da ka bai wa alhazai da ma’aikata hakokinsu, domin kaucewa, munanan addu’o’in alhazai a kan ka.

NAHCON
Bello Hamza
+ posts Bio
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    Shugaban Miyetti Allah, Bodejo Ya Karyata Zargin Halatta Kudin Haram A Zaman Kotu
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    Kafa Cibiyar NIPHID: NCDC Ta Yi Kuskuren Fahimtar Ƙudirin Dokar
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    Uwargidan Shugaban Ƙasa Ta Ƙaddamar Da Muhimman Ayyukan Ci Gaba A Jihar Jigawa
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    Ƙungiyar Kansilolin APC Ta Yi Barazanar Janye Goyon Bayanta Idan Ba A Daina Zargin Sanata Yari Ba
NAHCON
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Cinikin Waje Ta Kasar Sin Na Bunkasa Cikin Sauri Da Kwanciyar Hankali A Rabin Farko Na Shekara Ta 2026
  • Sulaiman
    An Yi Tir Da Kalaman Wasu Sassan Ketare Game Da Yayata Batun Cika Shekaru Goma Da Fitar Da Abin Da Aka Kira “Hukuncin Tekun Kudancin Sin”
  • Sulaiman
    Nijeriya Za Ta Zama Ƙasa Mai Zaman Lafiya, Ba Za A Ƙara Samun Kashe-kashen Jama’a Ba – Oluremi Tinubu
  • Sulaiman
    Sin Ta Tsara Bunkasa Darajar Cinikayyar Kayayyaki Zuwa Yuan Tiriliyan 60 Yayin Shirin Raya Kasa Na Shekarar 2026 Zuwa 2030

MASU ALAKA

Na Yi Tsayin-daka Domin Cika Alƙawarin Ƙasata Nijeriya
Rahotonni

Na Yi Tsayin-daka Domin Cika Alƙawarin Ƙasata Nijeriya

July 14, 2026
Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya
Rahotonni

Mun Ɗauki Nauyin Karatun Masu Digiri Ta Hanyar Sayar Da Ƙosai Da Ƙuli-ƙuli —Wasu Ƴan Kasuwa

July 11, 2026
Matsalar Tsaro: Masana Sun Firgita Da Fitowar Sabon Bidiyon Bello Turji
Rahotonni

Matsalar Tsaro: Masana Sun Firgita Da Fitowar Sabon Bidiyon Bello Turji

June 26, 2026
Next Post
Larabawan Da Suka Dauki Kasadar Ceton Yahudawa Lokacin Kisan Kiyashi

Larabawan Da Suka Dauki Kasadar Ceton Yahudawa Lokacin Kisan Kiyashi

LABARAI MASU NASABA

Cinikin Waje Ta Kasar Sin Na Bunkasa Cikin Sauri Da Kwanciyar Hankali A Rabin Farko Na Shekara Ta 2026

Cinikin Waje Ta Kasar Sin Na Bunkasa Cikin Sauri Da Kwanciyar Hankali A Rabin Farko Na Shekara Ta 2026

July 14, 2026
An Yi Tir Da Kalaman Wasu Sassan Ketare Game Da Yayata Batun Cika Shekaru Goma Da Fitar Da Abin Da Aka Kira “Hukuncin Tekun Kudancin Sin”

An Yi Tir Da Kalaman Wasu Sassan Ketare Game Da Yayata Batun Cika Shekaru Goma Da Fitar Da Abin Da Aka Kira “Hukuncin Tekun Kudancin Sin”

July 14, 2026
Nijeriya Za Ta Zama Ƙasa Mai Zaman Lafiya, Ba Za A Ƙara Samun Kashe-kashen Jama’a Ba – Oluremi Tinubu

Nijeriya Za Ta Zama Ƙasa Mai Zaman Lafiya, Ba Za A Ƙara Samun Kashe-kashen Jama’a Ba – Oluremi Tinubu

July 14, 2026
Sin Ta Tsara Bunkasa Darajar Cinikayyar Kayayyaki Zuwa Yuan Tiriliyan 60 Yayin Shirin Raya Kasa Na Shekarar 2026 Zuwa 2030

Sin Ta Tsara Bunkasa Darajar Cinikayyar Kayayyaki Zuwa Yuan Tiriliyan 60 Yayin Shirin Raya Kasa Na Shekarar 2026 Zuwa 2030

July 14, 2026
Katsina: Kotu Ta Yanke Wa Hauwa’u Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya Kan Taimaka Wa ’Yan Bindiga

Kotu Ta Tsare Shugaban Makaranta Da Malami Kan Zargin Lalata Da Ɗaliba Mai Shekara 6 A Gombe

July 14, 2026
An Bankado Muguwar Aniyar Japan Ta Haifar Da Tashin Hankali A Tekun Kudancin Sin

An Bankado Muguwar Aniyar Japan Ta Haifar Da Tashin Hankali A Tekun Kudancin Sin

July 14, 2026
Layin Dogo Tsakanin Tanzaniya Da Zambiya Ya Zama Shaidar Abota Tsakanin Sin Da Afirka

Layin Dogo Tsakanin Tanzaniya Da Zambiya Ya Zama Shaidar Abota Tsakanin Sin Da Afirka

July 14, 2026
Nijeriya da Masar Sun Ƙulla Haɗin Gwiwa Domin Yaƙi da Miyagun Ƙwayoyi

Nijeriya da Masar Sun Ƙulla Haɗin Gwiwa Domin Yaƙi da Miyagun Ƙwayoyi

July 14, 2026
CMG Ya Gudanar Da Babban Taron Masu Kirkirar Manyan Shirye-Shirye Da Fina-Finai

CMG Ya Gudanar Da Babban Taron Masu Kirkirar Manyan Shirye-Shirye Da Fina-Finai

July 14, 2026
Tsohon Sanatan Gombe, Bayero Nafada, Ya Fice Daga PDP Bayan Ganawa da Shugabannin APC

Tsohon Sanatan Gombe, Bayero Nafada, Ya Fice Daga PDP Bayan Ganawa da Shugabannin APC

July 14, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.