ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ƴan Kasuwa 7 Sun ɓace, Asarar Dukiya Ta Haura Biliyan 5 A Gobarar Kasuwar Singa

by Abubakar Sulaiman
7 months ago
Gobara

Aƙalla mutane bakwai ne aka bayyana sun ɓace bayan wata mummunar gobara da ta tashi a Kasuwar Singa da ke Jihar Kano. Shugaban Ci Gaban Kasuwar Sings (SIMDA), Barrista Junaidu M. Zakari, ya shaida wa manema labarai cewa har yanzu ba a gano inda mutanen suke ba, yayin da ake ci gaba da bincike domin tabbatar da ko suna raye ko a’a.

Zakari ya ce gobarar ta lalata kadarori da darajarsu ta haura Naira biliyan 5, yana mai bayyana lamarin a matsayin ɗaya daga cikin mafi muni a tarihin kasuwar. Ya ƙara da cewa wutar ta ƙone gidaje huɗu da ke ɗauke da dubban ƙananan rumfunan ’yan kasuwa, tare da lalata kayayyaki da kayan aiki da suka kasance tushen rayuwar ɗaruruwan iyalai.

  • Gobara Ta Sake Tashi A Kasuwar Singa A Kano
  • Sin Ta Mika Sakon Ta’azziya Sakamakon Gobara Da Ta Kone Wani Babban Kanti A Pakistan

Wani jami’in kasuwar, Ibrahim, ya ce gobarar ta ƙone sama da shaguna 100 da kuma rumbuna fiye da 50, inda wasu daga cikinsu ke ɗauke da kayayyakin da darajarsu ta kai miliyoyin Naira. Ya ce wutar ta ci gaba da ci har tsawon dare, kuma ana zargin na’urorin samar da wuta mai amfani da hasken rana (solar panel) na iya kasancewa sanadin tashin gobarar.

ADVERTISEMENT

Shugaban SIMDA ya ce jami’an agajin gaggawa da hukumomin tsaro na ci gaba da bincike domin gano musabbabin gobarar. Ya kuma yaba wa gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, bisa ziyarar da ya kai wurin yayin da gobarar ke ci, yana mai cewa hakan ya nuna tausayi da goyon baya ga waɗanda abin ya shafa.

Har yanzu hukumomi ba su fitar da sakamakon bincike kan musabbabin gobarar ba, yayin da ’yan kasuwa ke ƙoƙarin kwashe abin da ya rage daga dukiyoyinsu, tare da kira ga gwamnati da masu ruwa da tsaki su tallafa musu domin farfaɗo da kasuwancinsu.

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

Gobara
Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    Iyalin El-Rufai Sun Bai Ministan Tsaro Wa’adin Kwana 7 Kan Zargin Rikicin Kudancin Kaduna
  • Abubakar Sulaiman
    Atiku Ya Zargi Gwamnatin Tarayya Da Cin Bashi Kamar Mashayin Da Kuɗi Ya Ƙarewa
  • Abubakar Sulaiman
    Boko Haram Ta Kai Hari Adamawa, Ana Fargabar Mutuwar Mutane 11
  • Abubakar Sulaiman
    Ƴan Bindiga Sun Kai Hari Sokoto, Sun Kashe Mutane 7, Sun Yi Garkuwa Da 12

MASU ALAKA

Sojoji
Manyan Labarai

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Ballon D'or
Manyan Labarai

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

September 8, 2026
Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue
Manyan Labarai

Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue

September 8, 2026
Next Post
An Yi Taron Share Fagen Shagalin CMG Na Murnar Shiga Sabuwar Shekarar gargajiyar Kasar Sin A Hedikwatar MDD Da Kasar Jamus

An Yi Taron Share Fagen Shagalin CMG Na Murnar Shiga Sabuwar Shekarar gargajiyar Kasar Sin A Hedikwatar MDD Da Kasar Jamus

LABARAI MASU NASABA

Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.