ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Tsagaita Wuta: Wurare 5 Da Sharuɗan Iran Suka Ci Karo Da Na Amurka

by Rabi'u Ali Indabawa
5 months ago

A ƙarshen makon nan ne ƙasashen Amurka da Iran ƙarƙashin jagorancin Pakistan za su yi wani zama a Islamabad domin tattauna yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin ƙasashen biyu.

Kwana biyu da suka gabata aka cimma yarjejeniyar tsagaita wuta ta mako biyu, domin bayar da damar tattauna cikakkiyar yarjejeniyar dakatar da yaƙin Amurka da Isra’ila da kuma Iran a wani ɓangaren.

Duka ɓangarorin biyu sun gabatar da sharuɗɗan kawo ƙarshen yaƙin da aka shafe kimanin kwana 40 ana gwabzawa.

ADVERTISEMENT
  • PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi
  • Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara
  • Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027
  • Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

To sai dai akwai manyan ɓangarori biyar da ƙasashen biyu suka ci karo da juna a sharuɗɗan da kowanesu ya gindaya.

A matsayinta na mai shiga tsakani, Pakistan za ta yi ƙoƙarin daidaita al’amura tare da shawo kan ɓangarorin biyu wajen sassauta sharuɗɗan nasu domin cimma yarjejeniyar ta dindindin.

LABARAI MASU NASABA

Nijar Da Canada Sun Ƙulla Yarjejeniyar Gina Sabuwar Matatar Mai A Jihar Dosso

Kotun ICC Ta Yi Watsi Da Sabbin Takunkuman Amurka Kan Jami’anta

Kodayake ba a wallafa cikakkun sharuɗɗan ba, da suka haɗa da na Iran 10 da na Amurka 15, cibiyar nazarin alaƙa tsakanin ƙasashen duniya, ”Council on Foreign Relations”, ta zayyana wasu wurare biyar da ƙasashen biyu suka ci karo da juna a sharuɗɗan nasu, sun haɗa da:

Mashigar Hormuz

Mashigar Hormuz ta ƙasance ɗaya daga cikin abubuwan da aka fi ambata a tsawon lokacin wannan yaƙi.

Tun bayan fara kai mata hare-hare, Iran ta ɗauki matakin rufe mashigar a matsayin martani ga hare-haren.

Mashigar Hormuz ta ƙasance hanyar da kashi 20 cikin ɗari na man fetur da iskar gas na duniya ke bi ta wurin.

Galibin man da ke bi ta mashigar na ƙasashen Gabas ta Tsakiya da na yankin gulf ne, ƙasashen da Iran ta zarga da taimaka wa Amurka a hare-haren da take kai mata.

Sharaɗin Iran: Za ta riƙa lura da ilahirin mashigar da zirga-zirgar jigaren da ke bi ta ciki.

Sharaɗin Amurka: Iran ta sake buɗe mashigar ba tare da sanya idanu kan zirga-zirgar jiragen da ke bi ta wurin ba.

Shirin nukiliyar Iran

Wannan na ɗaya daga cikin batutuwan da suka haddasa rashin jituwa tsakanin Iran da Isra’ila da kuma Amurka.

Duka ƙasashen sun saka sharaɗi a kansa dangane da kawo ƙarshen yaƙin.

Sharaɗin Iran: Iran ta buƙaci damar ci gaba da inganta sinadarin yureniyom (uranium) zuwa wani mataki, tare da kawo ƙarshen sharuɗan hukumar sanya ido kan makamashin nukiliya (IAEA) kan shirin nukiliyarta.

Sharaɗin Amurka: Amurka ta buƙaci Iran ta haƙura kacokan da burinta na ci gaba da inganta sinadarin da kuma shirinta na nukiliya.

Ƙungiyoyin da ke goyon bayan Iran

Tun bayan fara yaƙin, ƙungiyar Hezbollah da ke Lebanon ta fara kai hare-hare cikin Isra’ila, yayin da ita ma Isra’ila ta mayar da martani ta hanyar kai hare-hare a birnin Beirut.

Baya ga Hezbollah, wata ƙungiyar da ke samun goyon bayan Iran da ta so shiga yaƙin ita ce ƙungiyar ƴantawayen Houthi da ke Yemen.

Sharaɗin Iran: Iran ta buƙaci Amurka da Isra’ila su daina kai wa waɗannan ƙungiyoyi hare-hare.

Sharaɗin Amurka: Iran da daina ɗaukar nauyin ƙungiyoyin ta hanyar ba su kuɗaɗe da kayan aiki.

Taƙaita sojoji

Batun taƙaita yawan soji a yankin na daga cikin abubuwan da ɓangarorin biyu suka ci karo da juna dangane da kawo ƙarshen yaƙin.

Sharaɗin Iran: Iran na son Amurka ta bayar da tabbacin cewa ba za ta ƙara kai mata hari ba, sannan ta janye ilahirin dakarunta daga yankin Gulf da yankin Gabas ta Tsakiya.

Sharaɗin Amurka: Amurka na son Iran ta taƙaita ƙarfin sojinta.

Diyya da takunkumai

Wani abu da sharuɗan ɓangarorin biyu ke cin karo da juna a wannan yarjejeniyar shi ne biyan diyya da batun takunkuman da aka sanya wa Iran.

Ƙasar Iran ta jima tana fuskantar jerin takunkuman tattalin arziƙi a duniya sakamakon shirinta na nukiliya.

Sannan kuma wannan yaƙi ya haifar mata da ɓarna mai yawan gaske.

Sharaɗin Iran: A ɗage mata duka takunkuman da aka sanya mata, sannan a biya ta diyyar ɓarnar da aka yi mata a wannan yaƙi.

Sharaɗin Amurka: Amurka ba ta nuna muradin hakan ba, sai dai Shugaba Trump ya nuna cewa zai iya ɗage wa Iran ɗin takunkuman nata.

Rabi'u Ali Indabawa
+ postsBio
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ƙungiya Ta Gudanar Da Zaɓen Sabbin Shugabanninta A Abuja
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Jihar Katsina Da UNICEF Sun Ceto Rayuwar Yara Ta Hanyar Samar Da Abinci Mai Gina Jiki
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Yadda Tinubu Ya Kashe Naira Biliyan 37.64 A Tafiye-tafiye
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ta’addaci: Mutum 14,500 Sun Bace A Arewa Maso Gabas

MASU ALAKA

Kasashen Ketare

Nijar Da Canada Sun Ƙulla Yarjejeniyar Gina Sabuwar Matatar Mai A Jihar Dosso

August 23, 2026
Kasashen Ketare

Kotun ICC Ta Yi Watsi Da Sabbin Takunkuman Amurka Kan Jami’anta

August 23, 2026
Kasashen Ketare

Rasha Da Ukraine Sun Zafafa Hare-hare Kan Juna Bayan Yaƙinsu Ya Ɗauki Sabon Salo

August 22, 2026
Next Post
James J. Heckman: Matakan Harajin Kwastam Na Kasar Amurka Sun Sabawa Ilmin Tattalin Arziki

James J. Heckman: Matakan Harajin Kwastam Na Kasar Amurka Sun Sabawa Ilmin Tattalin Arziki

LABARAI MASU NASABA

Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.