ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, July 15, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Wacce Ƙungiya Ce Ta Fi Yawan Dakon Tebur A Firimiyar Ingila?

by Abba Ibrahim Wada
3 months ago

Dakon Teburi dai shi ne abin da ake yawan jifan magoya bayan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Arsenal da shi saboda a lokuta da dama ƙungiyar tana samun damar ɗarewa kan teburin gasar firimiya ta Ingila har a kusa kammala gasar kafin daga baya kuma ƙungiyar ta dinga yin wasa da damarta ta lashe kofin.

Kalmar dakon teburi dai ana yawan jifan magoya bayan ƙungiyar kuma ana amfani da ita ne wajen tsokanar magoya bayan ƙungiyar da ta daɗe a kan teburi amma ta kasa lashe kofi. A taƙaice yanayi ne da ƙungiyar da ta nuna kamar za ta lashe kofin amma ya kuɓuce mata. Yanzu haka Arsenal na ƙoƙarin yakice wannan tambari da aka yi mata bayan shaharar da ta yi wajen “dakon tabur” a cikin kusan shekaru 20 a baya-bayan nan. To amma ba Arsenal ce kawai ta taɓa shiga irin wannan hali, hasali ma akwai wasu ƙungiyoyin da nasu “dakon teburin” ya fi na Arsenal ciwo.

  • ‘Yansanda Sun Kama Shugaban PFIPC, Adeyemi
  • ‘Yansanda Sun Kama Wani Kan Zargin Yi Wa ‘Yan Bindiga Safarar Makamai A Kano
  • Sakamakon Binciken Masana Na Kasar Da Ake Fitarwa Kyauta Yana Kara Jan Hankalin Duniya
  • Cinikin Waje Ta Kasar Sin Na Bunkasa Cikin Sauri Da Kwanciyar Hankali A Rabin Farko Na Shekara Ta 2026
  • An Yi Tir Da Kalaman Wasu Sassan Ketare Game Da Yayata Batun Cika Shekaru Goma Da Fitar Da Abin Da Aka Kira “Hukuncin Tekun Kudancin Sin”

A ƙoƙarin ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Liɓerpool  na lashe kofin Premier karon farko a kakar wasa ta 2018 zuwa 2019 Liɓerpool ta kama hanya tiryan-tiryan wajen tabbatar da hakan a kakar, inda ta tattara maki 97, wanda a lokacin ita ce ƙungiya da ta tara maki mafi yawa a tarihin gasar. Matsala ɗaya ce ta samu, wato Manchester City ta fi ta da maki ɗaya.

ADVERTISEMENT

Liɓerpool a lokacin, ƙarƙashin Jurgen Klopp ta samu nasara a wasa 30 kuma ta kasance a kan teburin Premier na tsawon kwana 141 – yayin da a cikin watan Disamba na kakar Manchester City tana ƙasanta da maki 10. Amma wasan da Liɓerpool ta sha kashi da ya fi shahara a lokacin shi ne wanda ta ziyarci Manchester City – inda ɗan wasan baya na Manchester City, John Stones ya hana ƙwallo shiga raga a kan layi – kuma wannan wasa shi ne ya yanke hukunci kan ƙungiyar da za ta lashe kofin. Duk wani yunƙuri da Liɓerpool ta yi na ganin ta riƙe wuta, abin ya ci tura, har ya kai ga City ta lashe kofin.

Arsene Wenger ya yi fatan shafe kakar wasan ba tare da an doke shi ba, bayan lashe kofuna biyu a shekarar 2002, inda a lokacin ake tunanin Arsenal za ta zama ‘giwar Ingila’ bayan ƙwace kofi daga hannun Manchseter United. A wannan lokaci Arsenal ƙarƙashin Wenger, wanda ake wa laƙabi da ‘Farfesa’, ta kwashe kusan wata biyar a kan teburi.

LABARAI MASU NASABA

FIFA Na Nazarin Faɗaɗa Gasar Kofin Duniya Zuwa Ƙasashe 64

Harry Kane: Lashe Kofin Duniya Ya Fi Mini Muhimmanci Fiye da Takalmin Zinare

Sai dai ba da daɗewa ba Manchester United ta yi nasara a kan Liɓerpool ta kuma sake yin nasara a kan Newcastle United, yayin da Arsenal ta yi canjaras da Aston Ɓilla a filin wasa na Highbury a tsakiyar Afrilu. Aka yi wasa tsakanin ƙungiyoyin biyu, inda Theirry Henry ya zura ƙwallo biyu bayan Ruud ɓan Nistelrooy ya ci da farko, sai dai Ryan Giggs ya ƙara jefa ɗaya, aka tashi 2-2. Tun daga lokacin United ta ci gaba da ƙoƙari a wasanninta, yayin da ita kuma Arsenal ta yi tuntuɓe a wasanninta da Bolton da kuma Leeds.

A shekarar 2008, bayan komawa wasa a filin wasa na Emirates, Arsenal wadda ta nuna kamar za ta taka rawa, ya zuwa watan Maris ta yi rashin nasara ne sau ɗaya kacal, kuma ta shafe kwana 156 a kan teburi, amma ya zuwa watan Maris Arsenal ta koma ta uku, a ƙasan Manchester United da Chelsea. Daga nan ne Arsenal ta shiga cikin halin ha’ula’i a Premier bayan ɗan wasa Eduardo ya karya ƙafarsa a karawa da Birmingham, inda Arsenal ta yi wasa 5 ba tare da yin nasara ba.

Ba a Premier kawai ba, Arsenal ta sha kashi ta ko ina, inda Tottenham ta lallasa ta a matakin kusa da ƙarshe na gasar League Cup, United ta taka mata burki a kofin FA sannan Liɓerpool ta yi waje da ita a gasar zakarun Turai. Tun daga wannan lokaci Arsene Wenger bai ƙara lashe Premier ba, inda ƙungiyar ta kwashe kakar wasa 9 ba tare da cin kofi ba, lamarin da ya sanya Mourinho ya bayyana Wenger a matsayin “ƙwararre kan rashin nasara”.

Arsenal ba ta sake cin komai ba har sai wuraren ƙarshe-ƙarshen jagorancin Wenger inda ta lashe kofin FA.

Idan muka matso nan kusa-kusa a kakar 2022-23 Arsenal na kafa tarihi. Abin takaici ƙungiyar ta zamo wadda ta fi shafe kwanaki a kan teburi ba tare da lashe kofin ba, kwana 248. A cikin mako 30, Arsenal ta sauka daga saman teburi ne na kwana 3 kacal, bayan da Manchester City ta yi nasara a wani kwantan wasanta a watan Fabarairu sannan daga baya Arsenal ta sake komawa saman teburi kuma ta ci gaba da zama a sama har zuwa lokacin da ta je baƙunci a gidan Manchester City a ranar 26 ga watan Afrilu, inda ƴan wasan na Guardiola suka lallasa Arsenal da ci 4-1.

Manchester United: 1997-98

A shekarar 1998, Arsenal ce ke sheƙe-aya. Inda Wenger ke sauya yadda abubuwa a ƙungiyar. Arsenal ta samu nasarar cike giɓin maki mai yawa har ta zo ta lashe kofin Premier sannan kuma ta lashe FA. Da farko Manchester United ce a gaba, har ma wasu suna da tabbacin tamkar ta riga ta lashe kofin saboda ƙungiyar Blackburn ce ke biye wa United ya zuwa lokacin da aka kai rabin kakar, Arsenal tana a matsayi na 6. Sannan a wani lokaci a kakar, Arsenal na ƙasan United da maki 13.

Daga United ta shiga mummunan hali, inda ta samu maki ɗaya tal a karawarta da Southampton da Bolton da kuma Leicester, sannan ta yi rashin nasara a hannun Sheffield Wednesday, ta yi canjaras da West Ham kafin ta yi wata muhimmiyar karawa da Arsenal a watan Maris. Marc Oɓermars ya ci ƙwallo gab da tashi wasa yayin da Arsenal ta yi nasara a wasa 10 a jere. Daga nan United ta koma matsayi na biyu a kan tebur bayan yin canjaras da Liɓerpool da Newcastle United a watan Afrilu, inda suka ƙare kakar a mataki na biyu, bayan gazawa da maki ɗaya.

Liverpool: 2013- 2014

Zamewar da za a daɗe ba a manta da ita ba – lokacin da ɗan wasan tsakiya na Liɓerpool, Steɓen Gerrard ya zame, kuma na take ɗan wasa Demba Ba ya ɗauke ƙwallon sannan ya jefa ta a raga, lamarin da ya bai wa Chelsea nasara da ci 2-0 a filin wasa na Anfield. Damar da Liɓerpool ta samu ta kuɓuce.

A karawar kusa da ta ƙarshen kaka a Premier, Liɓerpool ta zura ƙwallo uku da farko, amma daga baya Crystal Palace ta farke, inda a ƙarshe aka tashi canjaras. A kakar da ta biyo ne Gerrard ya bar Liɓerpool ba tare da lashe Premier ba, duk da dai daga baya Liɓerpool ta lashe kofin a 2020.

Manchester United: 2011-2012

Ɗaya daga cikin hotunan gasar Premier mafi shahara shi ne na ɗan wasan Manchester City, Sergio Aguero na wulwula rigarsa bayan zura ƙwallo a minti na 94, ƙwallon da ta ƙwace kofin Premier daga hannun abokan hamayyarsu Manchseter United. United ta yi nata ƙoƙarin a wannan rana cikin watan Mayun 2012, inda ta yi nasara kan Sunderland. To amma matsalar ita ce ta ɓarar da damarta ne tun kafin wannan lokacin bayan da ƙungiyar ƙarƙashin Aleɗ Ferguson ta zubar da maki takwas yayin da ya rage saura wasa shida a kammala kakar.

A wannan kakar ma Arsenal ce take zaune a kan teburin gasar firimiya da tazarar maki shida tsakaninta da Manchester City kuma a ranar Lahadi ƙungiyoyin za su kece raini a filin wasa na Ettihad, idan har Manchester City ta samu nasara a wasan zai rage saura maki uku tsakaninsu kuma Manchester City ɗin tana da kwantan wasa. Idan kuma Arsenal ta samu nasara zai koma maki tara a tsakainsu sai kwantan wasa ɗaya da Manchester City take da shi.

Abba Ibrahim Wada
Website |  + postsBio
  • Abba Ibrahim Wada
    Ronaldo Da Ƴanwasan Da Suka Buga Kofin Duniya Na Ƙarshe A Rayuwarsu
  • Abba Ibrahim Wada
    Ko Ka San Dalilin Da Ya Sa Chana Da Indiya Ba Sa Buga Kofin Duniya?
  • Abba Ibrahim Wada
    Gwamnatin Kaduna Ta Yaba Wa NSA Kan Shirin Samar Da Dakarun Tsaron Daji
  • Abba Ibrahim Wada
    Lampard Zai Ci Gaba Da Zama A Coventry City

MASU ALAKA

FIFA Na Nazarin Faɗaɗa Gasar Kofin Duniya Zuwa Ƙasashe 64
Wasanni

FIFA Na Nazarin Faɗaɗa Gasar Kofin Duniya Zuwa Ƙasashe 64

July 12, 2026
Harry Kane: Lashe Kofin Duniya Ya Fi Mini Muhimmanci Fiye da Takalmin Zinare
Wasanni

Harry Kane: Lashe Kofin Duniya Ya Fi Mini Muhimmanci Fiye da Takalmin Zinare

July 11, 2026
Wasanni

Ronaldo Da Ƴanwasan Da Suka Buga Kofin Duniya Na Ƙarshe A Rayuwarsu

July 11, 2026
Next Post
Malaman Makarantun Gwamnati A Abuja Za Su Tsunduma Yajin Aiki Daga Ranar Litinin

Malaman Makarantun Gwamnati A Abuja Za Su Tsunduma Yajin Aiki Daga Ranar Litinin

LABARAI MASU NASABA

‘Yansanda Sun Kama Shugaban PFIPC, Adeyemi

‘Yansanda Sun Kama Shugaban PFIPC, Adeyemi

July 15, 2026
‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta

‘Yansanda Sun Kama Wani Kan Zargin Yi Wa ‘Yan Bindiga Safarar Makamai A Kano

July 15, 2026
Sakamakon Binciken Masana Na Kasar Da Ake Fitarwa Kyauta Yana Kara Jan Hankalin Duniya

Sakamakon Binciken Masana Na Kasar Da Ake Fitarwa Kyauta Yana Kara Jan Hankalin Duniya

July 14, 2026
Cinikin Waje Ta Kasar Sin Na Bunkasa Cikin Sauri Da Kwanciyar Hankali A Rabin Farko Na Shekara Ta 2026

Cinikin Waje Ta Kasar Sin Na Bunkasa Cikin Sauri Da Kwanciyar Hankali A Rabin Farko Na Shekara Ta 2026

July 14, 2026
An Yi Tir Da Kalaman Wasu Sassan Ketare Game Da Yayata Batun Cika Shekaru Goma Da Fitar Da Abin Da Aka Kira “Hukuncin Tekun Kudancin Sin”

An Yi Tir Da Kalaman Wasu Sassan Ketare Game Da Yayata Batun Cika Shekaru Goma Da Fitar Da Abin Da Aka Kira “Hukuncin Tekun Kudancin Sin”

July 14, 2026
Nijeriya Za Ta Zama Ƙasa Mai Zaman Lafiya, Ba Za A Ƙara Samun Kashe-kashen Jama’a Ba – Oluremi Tinubu

Nijeriya Za Ta Zama Ƙasa Mai Zaman Lafiya, Ba Za A Ƙara Samun Kashe-kashen Jama’a Ba – Oluremi Tinubu

July 14, 2026
Sin Ta Tsara Bunkasa Darajar Cinikayyar Kayayyaki Zuwa Yuan Tiriliyan 60 Yayin Shirin Raya Kasa Na Shekarar 2026 Zuwa 2030

Sin Ta Tsara Bunkasa Darajar Cinikayyar Kayayyaki Zuwa Yuan Tiriliyan 60 Yayin Shirin Raya Kasa Na Shekarar 2026 Zuwa 2030

July 14, 2026
Katsina: Kotu Ta Yanke Wa Hauwa’u Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya Kan Taimaka Wa ’Yan Bindiga

Kotu Ta Tsare Shugaban Makaranta Da Malami Kan Zargin Lalata Da Ɗaliba Mai Shekara 6 A Gombe

July 14, 2026
An Bankado Muguwar Aniyar Japan Ta Haifar Da Tashin Hankali A Tekun Kudancin Sin

An Bankado Muguwar Aniyar Japan Ta Haifar Da Tashin Hankali A Tekun Kudancin Sin

July 14, 2026
Layin Dogo Tsakanin Tanzaniya Da Zambiya Ya Zama Shaidar Abota Tsakanin Sin Da Afirka

Layin Dogo Tsakanin Tanzaniya Da Zambiya Ya Zama Shaidar Abota Tsakanin Sin Da Afirka

July 14, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.