A yau Laraba ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya taya Carlos Vila Nova murnar sake lashe zaben shugaban kasar Sao Tome da Principe. Shugaba Xi, ya ce a shekarun baya-bayan nan alakar Sin da Sao Tome da Principe na wanzuwa bisa kyakkyawan ci gaba.
Ya ce, sassan biyu sun ci gaba da zurfafa amincewar siyasa tsakaninsu, suna karfafa goyon bayan juna kan batutuwan dake shafar manyan moriyarsu, da wadanda suke mayar da hankali a kai, sun kuma cimma manyan nasarorin hadin gwiwa na hakika a fannoni da dama.
Kazalika, shugaba Xi ya ce, yana dora muhimmancin gaske, kan ci gaban dangantakar kasarsa da Sao Tome da Principe. Daga nan sai ya bayyana shirinsa na yin aiki kafada-da-kafada tare da shugaba Vila Nova, a fannin aiwatar da sakamakon taron dandalin bunkasa hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka ko FOCAC wanda ya gudana a birnin Beijing, a matsayin wata dama ta ci gaba da daga matsayin dangantaka bisa manyan tsare-tsare tsakanin Sin da Sao Tome da Principe zuwa sabon mataki, da kara kyautata gajiyar al’ummun kasashen biyu. (Saminu Alhassan)














