ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, July 15, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ya Dace ‘Yan Arewa Su Ƙara Marawa Tinubu Baya Domin Kammala Wa’adi Na Biyu — Shehu Sani

by Sulaiman and Shehu Yahaya
2 months ago
Sani

Tsohon Sanatan Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani, ya bukaci al’ummar Arewacin Nijeriya da su kara bai wa Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu cikakken goyon baya domin ya samu damar kammala sauran shekaru hudu da suka rage masa a wa’adi na biyu.

Shehu Sani, ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan kammala sallar Idi a jihar Kaduna . Ya ce kamar yadda al’ummar Arewa suka tsaya tsayin daka wajen bai wa marigayi tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari damar yin mulki na tsawon shekaru takwas, haka ma Shugaba Tinubu ya cancanci irin wannan goyon baya domin ci gaba da jagorantar kasar nan.A cewarsa, gwamnatin APC karkashin jagorancin Tinubu ta kawo sauye-sauye masu anfani a bangarori daban-daban, musamman a fannin tsaro da ayyukan ci gaba da suka shafi rayuwar jama’a.

Tsohon sanatan, wanda kuma shine dan takarar kujerar Sanatan Kaduna ta Tsakiya a karkashin jam’iyyar APC , ya bayyana cewa ya dace al’ummar Arewa su hada kai wajen tabbatar da nasarar jam’iyyar a babban zaben shekarar 2027.

ADVERTISEMENT

Ya ce duk da cewa a lokacin gwamnatin Buhari manyan mukamai da dama sun kasance a hannun ‘yan Arewa, amma yankin bai samu irin ci gaban da ake tsammani ba, musamman a bangaren tsaro.“Yau idan aka kwatanta da baya, an samu saukin matsalar rashin tsaro a wurare da dama.

Haka kuma gwamnati na aiwatar da muhimman ayyukan raya kasa da jama’a ke anfani da su,” inji Shehu Sani.Ya kuma bayar da misali da jihar Kaduna, inda ya ce a gwamnatin baya an samu korafe-korafe masu yawa kan rushe-rushen gidaje da shagunan jama’a, amma a yanzu karkashin jagorancin Gwamna Uba Sani an samu sauyi domin babu irin wadannan korafe-korafe kamar yadda aka saba gani a baya.A cewarsa, baya ga inganta harkokin tsaro, gwamnatin jihar Kaduna a yanzu na kokarin samar da zaman lafiya da hada kan al’umma domin tabbatar da ci gaba mai dorewa.

LABARAI MASU NASABA

Tsohon Sanatan Gombe, Bayero Nafada, Ya Fice Daga PDP Bayan Ganawa da Shugabannin APC

ADC Ta Nemi A Binciki Nafiu Bala Bayan INEC Ta Ƙaryata Iƙirarinsa

Dangane da zabukan fidda gwani na jam’iyyar APC, Shehu Sani ya yi kira ga duk wadanda suka shiga takara amma ba su samu nasara ba da su rungumi sakamakon zaben cikin kwanciyar hankali tare da hada kai domin ci gaban jam’iyyar.

Ya ce samun mulki ko rashin sa yana karkashin ikon Allah, don haka ya kamata ‘ya’yan jam’iyyar su fifita hadin kai da goyon bayan APC domin tabbatar da nasara a zabukan da ke tafe.Shehu Sani ya kara da cewa hadin kai tsakanin shugabanni da magoya baya shi ne zai tabbatar da dorewar mulki da kuma ci gaban Nijeriya baki daya.

Sani
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Sakamakon Binciken Masana Na Kasar Da Ake Fitarwa Kyauta Yana Kara Jan Hankalin Duniya
  • Sulaiman
    Cinikin Waje Ta Kasar Sin Na Bunkasa Cikin Sauri Da Kwanciyar Hankali A Rabin Farko Na Shekara Ta 2026
  • Sulaiman
    An Yi Tir Da Kalaman Wasu Sassan Ketare Game Da Yayata Batun Cika Shekaru Goma Da Fitar Da Abin Da Aka Kira “Hukuncin Tekun Kudancin Sin”
  • Sulaiman
    Nijeriya Za Ta Zama Ƙasa Mai Zaman Lafiya, Ba Za A Ƙara Samun Kashe-kashen Jama’a Ba – Oluremi Tinubu
Sani
Shehu Yahaya
+ posts Bio
  • Shehu Yahaya
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-yahaya/
    Majalisar Zartarwa Ta Jihar Kaduna Ta Amince Da Manufofin Haɓaka Walwalar Al’ummar Jihar
  • Shehu Yahaya
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-yahaya/
    Rashin Tarbiyya Da Ilimin Addini Ne Ke Sa Matasa Ɗaukar Doka a Hannu – Hon. Aminu Adam
  • Shehu Yahaya
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-yahaya/
    Yadda Ayyukan Titunan Gwamnan Kaduna Suka Farfaɗo Da Ilimi Da Kiwon Lafiya Da Noma A Sabon Gari
  • Shehu Yahaya
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-yahaya/
    Abubuwan Da Ba A Faɗa Ba Game Da Yadda Aka Hallaka Malamar Islamiyya A Kaduna

MASU ALAKA

Tsohon Sanatan Gombe, Bayero Nafada, Ya Fice Daga PDP Bayan Ganawa da Shugabannin APC
Manyan Labarai

Tsohon Sanatan Gombe, Bayero Nafada, Ya Fice Daga PDP Bayan Ganawa da Shugabannin APC

July 14, 2026
ADC Ta Nemi A Binciki Nafiu Bala Bayan INEC Ta Ƙaryata Iƙirarinsa
Siyasa

ADC Ta Nemi A Binciki Nafiu Bala Bayan INEC Ta Ƙaryata Iƙirarinsa

July 14, 2026
Zaɓen 2027: NNPP Ta Fara Shigar Da Sunayen ’Yan Takara, Ta Nemi INEC Ta Ƙara Mata Lokaci
Siyasa

Zaɓen 2027: NNPP Ta Fara Shigar Da Sunayen ’Yan Takara, Ta Nemi INEC Ta Ƙara Mata Lokaci

July 8, 2026
Next Post
τ-Law Ya Nuna Jajircewar Kasar Sin

τ-Law Ya Nuna Jajircewar Kasar Sin

LABARAI MASU NASABA

Sakamakon Binciken Masana Na Kasar Da Ake Fitarwa Kyauta Yana Kara Jan Hankalin Duniya

Sakamakon Binciken Masana Na Kasar Da Ake Fitarwa Kyauta Yana Kara Jan Hankalin Duniya

July 14, 2026
Cinikin Waje Ta Kasar Sin Na Bunkasa Cikin Sauri Da Kwanciyar Hankali A Rabin Farko Na Shekara Ta 2026

Cinikin Waje Ta Kasar Sin Na Bunkasa Cikin Sauri Da Kwanciyar Hankali A Rabin Farko Na Shekara Ta 2026

July 14, 2026
An Yi Tir Da Kalaman Wasu Sassan Ketare Game Da Yayata Batun Cika Shekaru Goma Da Fitar Da Abin Da Aka Kira “Hukuncin Tekun Kudancin Sin”

An Yi Tir Da Kalaman Wasu Sassan Ketare Game Da Yayata Batun Cika Shekaru Goma Da Fitar Da Abin Da Aka Kira “Hukuncin Tekun Kudancin Sin”

July 14, 2026
Nijeriya Za Ta Zama Ƙasa Mai Zaman Lafiya, Ba Za A Ƙara Samun Kashe-kashen Jama’a Ba – Oluremi Tinubu

Nijeriya Za Ta Zama Ƙasa Mai Zaman Lafiya, Ba Za A Ƙara Samun Kashe-kashen Jama’a Ba – Oluremi Tinubu

July 14, 2026
Sin Ta Tsara Bunkasa Darajar Cinikayyar Kayayyaki Zuwa Yuan Tiriliyan 60 Yayin Shirin Raya Kasa Na Shekarar 2026 Zuwa 2030

Sin Ta Tsara Bunkasa Darajar Cinikayyar Kayayyaki Zuwa Yuan Tiriliyan 60 Yayin Shirin Raya Kasa Na Shekarar 2026 Zuwa 2030

July 14, 2026
Katsina: Kotu Ta Yanke Wa Hauwa’u Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya Kan Taimaka Wa ’Yan Bindiga

Kotu Ta Tsare Shugaban Makaranta Da Malami Kan Zargin Lalata Da Ɗaliba Mai Shekara 6 A Gombe

July 14, 2026
An Bankado Muguwar Aniyar Japan Ta Haifar Da Tashin Hankali A Tekun Kudancin Sin

An Bankado Muguwar Aniyar Japan Ta Haifar Da Tashin Hankali A Tekun Kudancin Sin

July 14, 2026
Layin Dogo Tsakanin Tanzaniya Da Zambiya Ya Zama Shaidar Abota Tsakanin Sin Da Afirka

Layin Dogo Tsakanin Tanzaniya Da Zambiya Ya Zama Shaidar Abota Tsakanin Sin Da Afirka

July 14, 2026
Nijeriya da Masar Sun Ƙulla Haɗin Gwiwa Domin Yaƙi da Miyagun Ƙwayoyi

Nijeriya da Masar Sun Ƙulla Haɗin Gwiwa Domin Yaƙi da Miyagun Ƙwayoyi

July 14, 2026
CMG Ya Gudanar Da Babban Taron Masu Kirkirar Manyan Shirye-Shirye Da Fina-Finai

CMG Ya Gudanar Da Babban Taron Masu Kirkirar Manyan Shirye-Shirye Da Fina-Finai

July 14, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.