Jami’an Rundunar ƴansandan Jihar Kano tare da haɗin gwuiwar mazauna garin Garun Mallam, sun daƙile yunƙurin satar wani basaraken gargajiya, Sarkin Noman Kano, Alhaji Yusif Nadabo, a ƙaramar hukumar Garun Mallam. Lamarin ya faru ne da misalin karfe 11:30 na daren Asabar, 29 ga Agusta, 2026, bayan rundunar ta samu rahoton cewa wasu ’yan bindiga sun mamaye garin tare da harbe-harbe.
Maharan sun yi nasarar yin garkuwa da Nadabo, tare da harbin wasu mazauna garin uku, waɗanda aka bayyana sunayensu da Yusif Nasiru mai shekaru 20, da Salisu Garba da kuma Ibrahim Hassan.
Bayan samun rahoton, jami’an ’yansanda da sauran jami’an tsaro daga sassan da ke makwabtaka da yankin sun yi gaggawar zuwa wurin, inda suka haɗa kai da mazauna garin wajen bin sawun ’yan bindigar. Matsin lambar da jami’an tsaro da mutanen garin suka yi ya tilasta wa maharan watsar da Nadabo tare da tserewa, inda aka same shi ba tare da wani rauni ba.
An kai Nadabo da mazauna garin uku da aka harba zuwa Asibitin Koyarwa na Aminu Kano domin kula da lafiyarsu. A halin yanzu, rundunar ’yansandan ta ƙaddamar da farautar waɗanda suka kai harin tare da ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.
Kwamishinan ƴansandan Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya yaba da hadin gwiwar mazauna Garun Mallam da jami’an Vigilante da Neighborhood Watch Corps wajen kuɓutar da basaraken. Ya kuma bukaci mazauna yankin su kwantar da hankalinsu tare da ci gaba da bai wa jami’an tsaro sahihan bayanai da za su taimaka wajen kama waɗanda suka aikata laifin.














