ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, July 15, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda Cacar Zamani Ke Tatike Matasan Arewacin Nijeriya

by Bello Hamza
6 months ago
Cacar

Caca wata matsala ce da ta dade a tsakanin al’ummar arewacin Nijeriya, a shekarun baya matasa da magindata aka fi samu a wararen caca inda ake amfani da karta wajen gudanar da ita. A lokutta da dama zaka samu an tatike mutun tun daga kudaden da yake dauke da su har zuwa kayan da ya sa a jikinsa. Duk da haramcin da addini da al’ada suka yi ga aikata caca har zuwa yanzu an kasa samo hanyoyin kawo karshen wannan mummunan lamarin, musamman saboda yadda kamfanonin gudanar da cacar a wanna lokacin suka fito da wasu hanyoyi daban-daban da suka yi daidai da wannan zamanin wajen yaudarar matasa wajen shiga harkar cacar.

A wannan lokacin harkar caca na kara bazuwa sako da lungunan arewacin Nijeriya ne saboda wasu dalilai da masana suka bayyana kamar haka- na daya shi ne matsanancin matsalar tattalin arziki da ya addabi al’umma sun kuma kasa jurewa tare da fuskantar yadda za su fitar da kansu daga matsalar. Sai kuma ci gaba da aka samu na kimiyya da fasaha musamman bayyanar wayoyin hannu da hanyoyin sarrafata, sai kuma yadda aka samu guguwar son kallon kafa musamman wadanda ake gudanarwa a kasasshen Turai. A halin yanzu lamarin caca a tsakanin matasa ya bunkasa duk kuwa da kyamarta da ake a arewacin Nijeriya saboda haramcin addini da al’ada, haka ya sa lamarin ya fi bunkasa a kudancin kasar nan amma a yanzu caca a tsakanin matasanmu na arewa ya kai kashi 40 a cikin dari yayin a kudacin kasa suke da kashi 60.

  • Cinikayyar Waje Ta Jihar Xinjiang Ta Bunkasa A Shekarar 2025
  • Akpabio: Ba A Canza Komai A Cikin Sabbin Dokokin Haraji Ba 

A bayyane lamarin yake cewa, arewacin Nijeriya na fuskantar matsanancin talauci da tsananin rashin aikin yi a tsakanin matasa abin da yake tunzura matasa yin hijira biranen kudancin Nijerira donmin neman aikin yi, daga nan ne kuma wasu da yawa a cikin su ke koyo wasu muggan dabi’u wadanda suka hada da caca An kiyasta cewa, lamarin talauci ya kai kashi 77.7 a yankin arewa maso yammacin kasa, abin da ke tunzura wasu matasan fadawa harkar caca domin su samu tsira da mutumci daga sharrin talauci da hauhawar farashin kayayyakin amfani na yau da kullum.

ADVERTISEMENT

Bazuwar wayoyin hannu da aka fi sani da ‘Smart phone’ ya taimaka wajen bazuwar caca a tsakanin matasa, a yanzu mutum zai iya ci gaba da harkar cacarsa ba tare da kowa ya sani ba musamman a wuraren babu shagunan cacar da wuraren da ake nuna kyama ga masu caca da kuma wuraren da aka haramta cacar gaba daya. Sai ya zamana kana tare da mutum na tsawon lokaci amma baka san ya yi nisa a harkar caca ba. A kan haka a halin yanzu wasu kasashe ke kafa dokar kayyade shekarun sake wa yara masu tasowa mallakar wayar hannu tare da kuma sanya ido a kan yadda suke amfani da ita.

Tasirin kallon kwallon kafa musamman wadanda ke gudana a kasashen Tura da aka fi sani da ‘English Premier League’ ya zama dandamali na tarkon kamo matasa da shigar da su harkar caca ba tare da makusantar su sun sani ba. Da yawa daga cikin su sun yi imanin cewa, sanin su na yadda ake gudanar da harkar kwallon da sanin sanin su na shahararrun ‘yan wasan yana taimaka musu wajen samun nasara a cacar da suke yi. Sai dai abin takaicin shi ne har yanzu sun kasa fahimta tare da nuna wani na kusa da su da rayuwarsa ta canza saboda ya ci wasu makudan kudade ta hanyar cacar.

LABARAI MASU NASABA

Yayin Da Dangote Ya Bayyana A Ganawar Neman Aiki

A Karshe Jamilu Gwamna Ya Samu Babbar Damar Yin Takara

Wani abin da ke ingiza matasanmu fadawa harkar caca a wannan lokacin shi ne yadda kamfanonin cacar ke amfanbi da wasu fitattaun mutane a cikin al’umma wajen tallar nau’o’in caca daban-daban domin yaudarar matasa. Suna kuma amfani da fitattaun ‘yan kwallon kafa da fitattun mawaka wajen wannna aiki na tallata cacar.

A jihohin arewacin Nijeriya kamar Kano inda shari’a musulunci ta haramta caca a hukumance tun a shekarar 2000, gwamnati ta kara samamen da take kai wa shagunan caca a sassan jihar amma duk da haka harkar caca na ci gaba da bunkasa a sassan kasar baki daya inda aka kiyasta ana samun abin da ya kai Dala Biliyan 3.63 (fiye da Naira tiriliyan 5.6) kamar yadda kididdigar ya nuna a karshen shekarar 2025.

Wani abin da ke daure kai a lamarin cacar nan shi ne yadda yake ninka halin talaucin da masu mu’amala da ita ke ciki maimakon ya yi musu maganin talauci, wannan na faruwa ne saboda yawancinh matasan da ke harkar cacar sukan yi amfani ne da kudaden wasu harkoki ne na rayuwarsu kamar kudin makaranta da saurancu abin da ke jefa su cikin matsanancin bashi hakan kuma zai iya kaisu ga sayar da wasu kayyakin su da wanda bama nasu ba, in abin ya yi kamari yakan kaisu ga sace-sace da shiga wasu kungiyoyin ta’addanci. Bincike ya nuna cewa, harkar caca ta bayar da gummawa wajen matsalar tsaro da ake fuskanta a sassan arewacin Nijeriya.

Haka kuma an gano cewa, wadanda suka yi nisa a harkar caca suna fuskantar matsalar kwakwalwa saboda asarar da suke tafkawa wanda a lokutta dama yake kai wa ga kashe kai (suicide) da kuma yunkurin kisan kai a lokutta da dama. Harkar caca ta lalata rayuwar matasanmu ta fannoni da dama, ‘yan makaranta kan yi watsi da karatu.

A kan haka ya kamata gwamnati, iyaye da masu fada a ji a cikin al’umma su hada hannu wajen dakile yawaitar gidajen caca a garuruwanmu. Dole iyaye su kara sanya ido a kan yadda yaransu ke amfani da wayoyin hannu da kuma irin abokan da suke mu’amala da su. Allah ya shriya mana zuri’a.

Cacar
Bello Hamza
+ postsBio
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    Shugaban Miyetti Allah, Bodejo Ya Karyata Zargin Halatta Kudin Haram A Zaman Kotu
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    Kafa Cibiyar NIPHID: NCDC Ta Yi Kuskuren Fahimtar Ƙudirin Dokar
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    Uwargidan Shugaban Ƙasa Ta Ƙaddamar Da Muhimman Ayyukan Ci Gaba A Jihar Jigawa
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    Ƙungiyar Kansilolin APC Ta Yi Barazanar Janye Goyon Bayanta Idan Ba A Daina Zargin Sanata Yari Ba

MASU ALAKA

Yayin Da Dangote Ya Bayyana A Ganawar Neman Aiki
Bakon Marubuci

Yayin Da Dangote Ya Bayyana A Ganawar Neman Aiki

June 12, 2026
A Karshe Jamilu Gwamna Ya Samu Babbar Damar Yin Takara
Bakon Marubuci

A Karshe Jamilu Gwamna Ya Samu Babbar Damar Yin Takara

June 12, 2026
‘Symbolic Interactionism’:Sabuwar Makaranta A Kimiyyar Zamantakewa
Bakon Marubuci

‘Symbolic Interactionism’:Sabuwar Makaranta A Kimiyyar Zamantakewa

June 5, 2026
Next Post
Gwamnan Zamfara Ya Yaba Da Gudumawar Ɗan Majalisa Hon. Mai Palace A Bangaren Kiwon Lafiya

Gwamnan Zamfara Ya Yaba Da Gudumawar Ɗan Majalisa Hon. Mai Palace A Bangaren Kiwon Lafiya

LABARAI MASU NASABA

‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta

‘Yansanda Sun Kama Wani Kan Zargin Yi Wa ‘Yan Bindiga Safarar Makamai A Kano

July 15, 2026
Sakamakon Binciken Masana Na Kasar Da Ake Fitarwa Kyauta Yana Kara Jan Hankalin Duniya

Sakamakon Binciken Masana Na Kasar Da Ake Fitarwa Kyauta Yana Kara Jan Hankalin Duniya

July 14, 2026
Cinikin Waje Ta Kasar Sin Na Bunkasa Cikin Sauri Da Kwanciyar Hankali A Rabin Farko Na Shekara Ta 2026

Cinikin Waje Ta Kasar Sin Na Bunkasa Cikin Sauri Da Kwanciyar Hankali A Rabin Farko Na Shekara Ta 2026

July 14, 2026
An Yi Tir Da Kalaman Wasu Sassan Ketare Game Da Yayata Batun Cika Shekaru Goma Da Fitar Da Abin Da Aka Kira “Hukuncin Tekun Kudancin Sin”

An Yi Tir Da Kalaman Wasu Sassan Ketare Game Da Yayata Batun Cika Shekaru Goma Da Fitar Da Abin Da Aka Kira “Hukuncin Tekun Kudancin Sin”

July 14, 2026
Nijeriya Za Ta Zama Ƙasa Mai Zaman Lafiya, Ba Za A Ƙara Samun Kashe-kashen Jama’a Ba – Oluremi Tinubu

Nijeriya Za Ta Zama Ƙasa Mai Zaman Lafiya, Ba Za A Ƙara Samun Kashe-kashen Jama’a Ba – Oluremi Tinubu

July 14, 2026
Sin Ta Tsara Bunkasa Darajar Cinikayyar Kayayyaki Zuwa Yuan Tiriliyan 60 Yayin Shirin Raya Kasa Na Shekarar 2026 Zuwa 2030

Sin Ta Tsara Bunkasa Darajar Cinikayyar Kayayyaki Zuwa Yuan Tiriliyan 60 Yayin Shirin Raya Kasa Na Shekarar 2026 Zuwa 2030

July 14, 2026
Katsina: Kotu Ta Yanke Wa Hauwa’u Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya Kan Taimaka Wa ’Yan Bindiga

Kotu Ta Tsare Shugaban Makaranta Da Malami Kan Zargin Lalata Da Ɗaliba Mai Shekara 6 A Gombe

July 14, 2026
An Bankado Muguwar Aniyar Japan Ta Haifar Da Tashin Hankali A Tekun Kudancin Sin

An Bankado Muguwar Aniyar Japan Ta Haifar Da Tashin Hankali A Tekun Kudancin Sin

July 14, 2026
Layin Dogo Tsakanin Tanzaniya Da Zambiya Ya Zama Shaidar Abota Tsakanin Sin Da Afirka

Layin Dogo Tsakanin Tanzaniya Da Zambiya Ya Zama Shaidar Abota Tsakanin Sin Da Afirka

July 14, 2026
Nijeriya da Masar Sun Ƙulla Haɗin Gwiwa Domin Yaƙi da Miyagun Ƙwayoyi

Nijeriya da Masar Sun Ƙulla Haɗin Gwiwa Domin Yaƙi da Miyagun Ƙwayoyi

July 14, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.