ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, June 24, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda Gidajen Gyaran Hali Ke Mayar Da Ɗaurarru Masu Ilimi Da Sana’o’i

by Sulaiman and Idris Aliyu Daudawa
3 months ago
Ilimi

A cikin hukumomin gyara hali da ke sassa daban- daban na Nijeriya, akwai wani tattalin arziki da yake bunkasa daga cikinsu, Jaridar LEADERSHIP Lahadi ta yi rahoto dangane da hakan.Fursunoni suna shuka ganyayen miya, suna sayar da kayan abinci, suna yin wasu harkoki, sun maida gidajen gyara halin ka zama kasuwanni

Fursunoni sun zama masu harkokin kasuwanci, masu ilimi, a kwararru masu dabarun ayyuka, inda suka nuna ko da kuwa a tsakanin Fusunonin wasu kamar dai yadda rahotanni daga hukumar gyara halinka sun kammala wa’adin da aka ware masu, ba kawai halayensu sun sauya, suna barin gidajen gyara halin ka, ba kawai abin ya tsaya kan yadda aka canza masu halayensu bane, har ma da lamarin suna iya dogaro da kansu, su fara yin harkoki da dabarun da suka koya da kudaden da suka samu lokacin suna Gidan Maza, Gidan Kaso, Kurkuku, ko Gidan Gyara Galinka.

Wakilanmu sun gano cewa yawancin Fursunonin da suke a Gidajen gyara halinka na Nijeriya ba wai ana basu gwale- gwale bane; abin yana canzawa ne yanzu uwa wuraren gyara halaye, tare da bayanan da suke nuna yanzu wasu daga cikin Fursunonin, suna bude sabbin babi na samun milyoyin Naira ta hanyar yin abubuwan da za su bunkasa rayuwrasu da kansu.

ADVERTISEMENT

LEADERSHIP Lahadi domin haka ba tayi wata kasa a gwiwa ba domin kuwa bayanan da ta samu daga wani mutum babba wanda ba yaso a ambaci sunan sa daga Shalkwatar hukumar gyara halin ka ta kasa, ya bayyana cewa ywancin wadanda suka fi maida hankalinsu sun koma lamarin aikin gona inda suka zuba kudaden da suka samu ta bangarorin ilimi da zurga- zurga, wadanda duk lokacin suna cibiyoyin koyon sana’oi da ita Hukumar gyara halin ka, ta kasa ta tanada .

Majiyar ta ce Fursunonin yanzu sun kasance sune ke taimakawa iyalansu, inda daya daga cikinsu ya dauki nauyin ‘ya’yan sa uku har sai da suka kammala ilimin Jami’a.

LABARAI MASU NASABA

An Nemi Shugabanni Su Rungumi Tafarkin Adalci A Tsakanin Al’ummunsu

Ƴan Bindiga Sun Tilasta Wa Ƙauyukan Sakkwato Biyan Sabon Haraji

Duk da yake dai majiyar ta mu bata bayyana ko su wanene ba daga cikin Fursunonin, Jaridar LEADERSHIP Lahadi ta samu labarin cewa daya daga cikinsu yana cibiyar koyon sana’oi da ke karkashin hukumar ta Jihar yayin da sauran an aje su ne a irin cibiyoyin na koyon sana’oi da suke Jihar Enugu da kuma Abuja ba da dadewa ba.

An samu labarin cewa Fursunan da ke Kaduna ya samu kudaden da suka zarce Naira milyan 4.5 ta hanyar sayar da kayan lambu da suka hada da ganyaye a lambun shi da ke cibiyar, yayin da sauran suna irin cibiyoyin da suke Enugu da kuma gonar Dukpa da ke Gwagwalada, Abuja ya yi amfani ne da kudaden da ya samu ta hanyar sayar da amfanin gona, da kujeru da gadajen da ya yi, ya gina gidaje da gidajen Gurodi,da kuma sayen motoci na haya.

Da yake amsa tambayoyin Jaridar LEADERSHIP ta Lahadi, Jami’ar hulda da jama’a na Hukumar gyara halin ka, ta kasa, Babbar Safuritendar ta gyara halin ka Jane N.Osuji, cewa ta yi a cikin gidan da yake da babbar Katanga da kofofin da aka kullewa, da akwai dubban Fursunoni wadanda suke sake rubuta tarihin rayuwarsu, na kasuwanci mai dalili,sai kuma yadda aka takura su saboda da wata damar da suke bukata a gaba, saboda yadda ake fatan rayuwar ta kasance a gaba.

Osuji ta bayyana maganar gyara hali gwamnatin tarayya ce ta ke daukar nauyin lamarin,wanda hakan ya sa ake ta kara kaimi wajen yin gyare- gyare a cibiyoyin da ake koyon sana’oi na gyara halin ka,ta hanyar Noma da kuma yin hadin gwiwa da wadanda suke zaman kansu da suke da halin na taimakawa.

Da yake tabbatar da sahihancin maganar da ke nuna wasu Fursunonin da suka maida hankalinsu sun mallaki gidaje da sayen motocin haya saboda harkoin zurga- zurga,kai har ma da kaddarorin gidaje duk ta hanyar sayar da kayan amfanin gona, jami’ar hulda da jama’a ta bayyanawa wakilan mu cewar Fursunoni daga Kudu maso gaba, Arewa ta tsakiya,da sauran sassa wadanda suka kammala wa’adinsu suna tafiyar da harkokinsu abin gwanin ban sha’awa.

Jami’in hulda da jama’a na Hukumar gyara halin ka ta kasa tana da cibiyoyin aikin gona wadanda suke a sassa daban- daban na Nijeriya, suna da Taraktocin noma masu kayan aiki “suna noman manja, Shinkafa, masara, da sauran hatsi domin a taimaka wajen cike gurbin da ake da shi tsakanin Fursunoni.”

Osuji,duk da hakan ta ce,Fursunoni wadanda suke jiran, a yanke masu hukunci, wadanda su suka fi kowa yawa a gidajen gyara halin ka, yawanci ba,a cika kai su gonaki ba,da sauran taimakawar da ake yi, ’duk kai ayyukan suna da alaka da yadda za a gyara halayen su Fursunonin domin su amfani kansu da kuma al’umma a gaba.

Da yake bayani akan ciyar da su Fursunoni da kuma jin dadinsu, lamarin da shi ne ya tsaya a makogwaron hukumar cewar, Osuji, yayin da gwamnati ita ce ke samar da bukatun su Fursunonin da suka hada da alawus din abinci, kula da lafiya, kayan sawa, da kuma gado.

Sai dai kuma binciken da, LEADERSHIP Lahadi ta yi ya nuna cewa abincin ba wani abin da za a dogara da shi bane, illa nau’in abincin da yake bada karfin jiki ko bada kuzari.

Wannan shi yasa Fursunoninsun dogara ne da abincin da ‘yan’uwansu ke kawowa, yayin da wasu kuma suke yin aikin wucin gadi a cikin Gian gyara halin ka,kamar wankin kaya, taimako a Kicin, ko taimakawa abokin zama Fursuna saboda su samu wani abinda zai taimaka masu wajen tafiyar da rayuwa. Sai dai kuma kamar yadda ake fuskantar kuncin rayuwa yadda fashin kaya suke ci gaba da yin tashin gwauron Zabo abin yana da kamar wuya.

Mai kula da al’amuran hulda da jama’a ta hukumar maganar gaskiya cewa ta yi, a gidajen gyara halin ka, Fursunonin suna koyon sana’oi saboda damarmakin da suka samu saboda ci gaba da kuma inganta, sana’oi kamar Kafinta, Tela, Walda, da kuma aikin gona, yayin da wasu kuma neman ilimi suke yi kamar ilimin bai daya, har zuwa karatu mai zurfi.

Ta ce, “Wasu sun su har ma sun yi digiri, kai har ma digirin digirgir lokacin da suke a gidan gyara halinka, wato sun maida shekarun da suka yi a tsare zuwa shekarun da suka gay a dace su ba mara da kunya, wajen kishin kansu.”

Kamar yadda ta jaddada, “Wani wuri ne in da Fursunonin da suka aikata laifuka amma ba wadanda suka shafi, shafi badana ba kamar yi wa mata fyade, ya kasance kuma sun yi daya bisa hudu wato kwata na shekarun da ake yanke masu hukunci a wuraren gyara halin ka.”

An maida su zuwa can ne domin a samu damar lura da su saboda ‘yantasu da ake son yi, wannan kuma ya dogara ne da irin shawarar da jami’an wurin da aka fara ajiye su inda akwai kayan da za su yi amfani da su .Lura da su kafin a ‘yantasu su samu ‘yanci hakan na nuna bin ba zai kasance kyauta ba ne ba tare da wasu sharudda ba, sai dai kuma suna iya zuwa wani wuri ba tare da jami’in tsaro na hukumar tare da su yana sa ido a kansu.

Sai dai kuma duk da hakan akwai wani taron da ba a dade da yin shi ba da hukumar gidajen gyara halin ka ta kasa ta shirya tare da hadin gwiwar, kungiya mai zaman kanta Hope Behind Bars Africa da kuma taimakon ( tsarin tafiyar da aiki da gaskiya da kuma tsarin hana lamurran cin hanci), hakan ya sa masu ruwa da tsakin saboda a samu kulaw kwarai da gaske musamman ma hadin kan al’umma da masu zaman kansu don tabbatar da samun kawo gyara na lamarin da ya shafi Fursunoni.

Taron mai taken“Yadda za a samu hadin kan masu kulawa da cibiyoyin noma na Gidajen gyara halin ka,da al’umma da kungiyoyi masu zaman kansu hanyoyin da za a kawo gyare- gyare kan lamuran da suka shafi Fursunoni ,”an samu haduwar jami’an gwamnati da masu zaman kansu, abokan ci gaba,sai kungiyoyi ma su zaman kansu su bada hanyoyi mafi dacewa da za a samu kawo gyare- gyaren da ake bukata akan yanayin da Fursunoni su ke.

Konturola Janar na hukumar gyara halin ka , Mista. Sylbester Nwakuche, ya bayyana cewa cibiyoyin gonakin gyara hali su ba wai saboda noma ne ba kadai, wurare ne da suke tafiya daidai da tsarin hukuma musamman ma yadda rayuwar su Fursunonin za ta kasance a gaba.

Ya bayyana cewa Hukumar gyara kayanka ta kasa yanzu tana da abubuwan noma masu yawa a kasa baki daya, tare da masu kiwon Alade, sai kuma wasu kayan abinci kamar su Shinkafa, dawa, ganyaye,yayin da su Fursunonin an koya masu dabarun da za su rika amfani da su suna samun kudaden shiga.

Kamar yadda ya ce, su wadancan dabarun an shirya su ne ba kawai domin taimakawa a samu abinci a gidajen gyara hali, amma ana shirya ma su yadda rayuwa za ta kasance bayan sun gama zaman gidan Kaso.

Lamarin ya zarce noma, Shugaban hukumar ya ce akwai wani abinda ake shirin yi mai amfani, wanda zai bada muhimmanci akan gyara, kulawa ta musamman, yadda za a sake hada shi da al’umma, ba kawai maida hankali ba kan horo kadai ba.

Ya kara jaddada cewa, “Abubuwan ko tsare- tsaren da aka yi a cibiyoyin gyara hali, gabatar masu tsari na yadda za su gane gaskiyar wurin da suke wato yadda suke a tsare babu wani’yancin yin abubuwna da aka saba yi, yadda suka rabu da rasa yin wasu abubuwan da aka sabawa yi , sai kuma rashin tabbas din yadda gaba za ta kasance.”

Ya ce su Jami’an gidajen gyara hali da ake yi ma kallon wadanda suke tursasawa, yanzu sun canza taku domin kuwa yanzu sun canza taku saboda kuwa sun zama masu bada shawara rarrashi, da hakan ne ake yin sa’a har su Fursunonin su sauya yadda za su kasance da rayuwa.

Jaridar LEADERSHIP ta bayyana duk da yake su gyaran da ake son kawowa suna fadada, maganar gaskiyar rayuwar gidan gyara hali tana da matsala.Domin kuwa akwai Fursunoni daga cikinsu daga cikinsu suna jiran a yanke masu hukunci, Lamarin da ya shafi tsarin gidajen gyara halin ka, yana ci gaba da tafiyar hawainiya da, ta hakan ne ake daukar alhakin wadanda suk e dadewa.

Ida ana son maganin wannan, irin gyare- gyaren da ake son kawowa da suka hada da yadda za a rika yin shari’a ta kafar sadarwa ta zamani, samar da taimakon da ya shafi lamarin shari’a, mataki irin wanda ba za a ajiye mutum gidan kurkuku ba, sai maganar yi wa al’umma aiki,akwai bukatar samun hadin kai tsakanin hukumomin shari’a.

 

Fursunoni 58 Sun Kammala Jami’a

Gaba daya Fursunon 58 suka kammala jami’a baa dadewa ba daga Jami’ar karatu a Fursunoni 25 sun kammala karatu daga jami’ar, a shekara ta 2022

Mataimakin Shugaban jami’ar ta NOUN, Farfesa. Olufemi Peters, shi ne ya ba Ya bayyana cewa “Muna da ‘yan makaranta masu karatun digiri 21,339 – sai kuma 7,101 wadanda suke karatun digiri na biyu da suka kammala.Daga cikin wadannan akwai Fursunoni 58, daga cikinsu 7 sun kammala karatun digiri na biyu .Ya ce suna da cibiyoyin karatu 14 We habe 14 a Gidajen gyara hali ya ce an kuma basu umarni na su fafad ko bunkasa su.’’

 

Ilimi
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Li Qiang Ya Halarci Bikin Bude Dandalin Tattalin Arzikin Duniya Na Davos Na Shekarar 2026
  • Sulaiman
    Xi Ya Yi Kiran Daukar Matakan Zamanantar Da Aikin Gona Da Yankunan Karkara
  • Sulaiman
    Ya Kamata Sin Da Birtaniya Su Yi Aiki Tare Don Ci Gaba Da Inganta Dangantakarsu
  • Sulaiman
    Firaministan Sin Ya Jaddada Muhimmancin Kara Azamar Bunkasa Kirar Kayayyakin Aikin Masana’antu Na Zamani
Ilimi
Idris Aliyu Daudawa
+ posts Bio
  • Idris Aliyu Daudawa
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-aliyu-daudawa/
    Matar Gwamnan Zamfara Ta Sha Alwashin Ci Gaba Da Tsarin Bunƙasa Ilimin Ƴa Mace
  • Idris Aliyu Daudawa
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-aliyu-daudawa/
    Hukumar Ilimin Bai-ɗaya Ta Jihar Yobe Ta Raba Kayan Karatu
  • Idris Aliyu Daudawa
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-aliyu-daudawa/
    2027:Yadda Kuɗi Da Siyasar Uban-gida Suka Daƙile Hanƙoron Matasa
  • Idris Aliyu Daudawa
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-aliyu-daudawa/
    NANS Ta Kafa Kwamitin Ganin Yadda Ake Tafiyar Da Ayyukan TETFund

MASU ALAKA

Nijeriya
Rahotonni

An Nemi Shugabanni Su Rungumi Tafarkin Adalci A Tsakanin Al’ummunsu

June 20, 2026
Ambaliyar Ruwa Ta Lalata Gidaje 14,940 A Sokoto
Rahotonni

Ƴan Bindiga Sun Tilasta Wa Ƙauyukan Sakkwato Biyan Sabon Haraji

June 20, 2026
IMF
Rahotonni

Tattalin Arziƙin Ƙasa: Masana Sun Buƙaci Tinubu Ya Yi Hattara Da Shawarar IMF

June 20, 2026
Next Post
2027: Obi Da Kwankwaso Za Su Fafata Da Atiku Wajen Neman Takarar Shugaban Kasa A ADC

2027: Obi Da Kwankwaso Za Su Fafata Da Atiku Wajen Neman Takarar Shugaban Kasa A ADC

LABARAI MASU NASABA

Li Qiang Ya Halarci Bikin Bude Dandalin Tattalin Arzikin Duniya Na Davos Na Shekarar 2026

Li Qiang Ya Halarci Bikin Bude Dandalin Tattalin Arzikin Duniya Na Davos Na Shekarar 2026

June 24, 2026
Xi Ya Yi Kiran Daukar Matakan Zamanantar Da Aikin Gona Da Yankunan Karkara

Xi Ya Yi Kiran Daukar Matakan Zamanantar Da Aikin Gona Da Yankunan Karkara

June 24, 2026
Tinubu Ya Gaza Wajen Magance Matsalar Tsaro A Nijeriya — Atiku

Atiku Ya Soki Tsare El-Rufai, Ya Ce Sharuɗan Belinsa Sun Yi Tsauri

June 24, 2026
Trump Ne Zai Jagoranci Bayar Da Kofin Duniya A Wasan Ƙarshe – Infantino

Trump Ne Zai Jagoranci Bayar Da Kofin Duniya A Wasan Ƙarshe – Infantino

June 24, 2026
‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta

’Yansanda Sun Kama Wani Mutum da Harsasai 174 A Nasarawa

June 24, 2026
Sojoji Sun Kama Ɗan Fashi Da Makami A Taraba

Sojoji Sun Kama Ɗan Fashi Da Makami A Taraba

June 24, 2026
An Kashe Mutum 2, 8 Sun Jikkata Yayin Rikici A Bauchi

An Kashe Mutum 2, 8 Sun Jikkata Yayin Rikici A Bauchi

June 24, 2026
Tsohon Shugaban APC Na Kebbi Ya Rasu A Hannun ’Yan Bindiga

Tsohon Shugaban APC Na Kebbi Ya Rasu A Hannun ’Yan Bindiga

June 24, 2026
Ya Kamata Sin Da Birtaniya Su Yi Aiki Tare Don Ci Gaba Da Inganta Dangantakarsu

Ya Kamata Sin Da Birtaniya Su Yi Aiki Tare Don Ci Gaba Da Inganta Dangantakarsu

June 23, 2026
Firaministan Sin Ya Jaddada Muhimmancin Kara Azamar Bunkasa Kirar Kayayyakin Aikin Masana’antu Na Zamani

Firaministan Sin Ya Jaddada Muhimmancin Kara Azamar Bunkasa Kirar Kayayyakin Aikin Masana’antu Na Zamani

June 23, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.