Ministan Tsaron, Janar Christopher Musa mai ritaya, ya bayyana yadda jami’an tsaro ke samun nasarar ceto mutanen da aka yi garkuwa da su ba tare da kashe ko biyan kudin fansa ga ‘yan ta’addan da suka yi garkuwa da su ba.
Ministan ya ce dabarar da ake amfani da ita, ita ce gano inda ‘yan ta’addan suke, tare da katange hanyoyin tserewarsu da kuma yanke musu damar samun abinci, da ruwa, da man fetur da sauran kayayyakin da suke buƙata domin rayuwa.
Ya ce a wasu lokuta, ‘yan ta’addan kan tsere da zarar jami’an tsaro sun matsa musu lamba, su bar mutanen da suka yi garkuwa da su a baya. Ministan ya bayyana cewa ko da jirgin sama mara matuki ne kawai aka gani, ‘yan ta’addan kan watse saboda tsoron kada a kai musu hari.
Ya bayar da misalin yadda wannan dabara ta taimaka wajen ceto waɗanda aka yi garkuwa da su a wasu hare-haren baya-bayan nan, yana mai cewa fifikon jami’an tsaro shi ne tabbatar da an kuɓutar da waɗanda aka yi garkuwa da su cikin aminci tare da rage asarar rayuka.
Ministan ya jaddada cewa jami’an tsaro na ci gaba da amfani da bayanan sirri, da dabarun kewayewa da sauran hanyoyin soji domin ceto waɗanda aka yi garkuwa da su da kuma daƙile ayyukan ‘yan ta’adda a sassan ƙasar.














