ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Tuesday, July 21, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Abin Da ‘Yan Nijeriya Ke Bukata A 2026

by Leadership Hausa and Sulaiman
6 months ago
Nijeriya

A yayin da ‘yan Nijeriya suka shiga sabuwar shekarar 2026, sun bayyana godiyarsu, bisa raya su da Allah yayi, har suka ga shiga cikin sabuwar shekarar.

Shekarar ta 2025 ta kasance, cike take da manyan kalubale, musamman na kalubalen rashin tsaro, da ta addabi kasar.

2025, ta kuma kasance an fuskanci garkame makarantu da yawan samun yajin aikin manyan makarantu, musammman na gwamnati, wanda hakan ya haifar da jani in ja ka, a bangaren gwamnati da kuma kungiyoyin kwadado.

ADVERTISEMENT

Shekarar ta kuma zamo wacce a rinka sace dalibai, daga makarantunsu na kwana da kai hare-hare a cikin alumma da kuma kai wasu hare-haren, a guraren ibada.

Abin farko da ‘yan kasar suke fata a 2026 daga gun masu rike da madafun iko na siyasa a kasar shi ne, sauke nauyin da aka dora masu, na yin shugabanci, na gari.

LABARAI MASU NASABA

Ana Ci Gaba Da Tafka Muhawara Kan Shirin Gwamnati Na Haramta Masana’atun Sarrafa Robobi

Kisan Gillar Marabar Jos: Bai Kamata Jinin Malama Ummulkhairi Ya Tafi A Banza Ba

Kazalika, yayin da zabukan 2027 ke kara karatowa, akasarin masu rike da madafun ikon, burinsu shi ne, su sake dare Karagarsu, inda tuni, tun kafin a kada Gangar siyasar, suka fara kai gauro da mari, domin ganin sun ci gaba da shugabantar alumomin su. Idan har suka ci gaba da yin wannan hakilon na son ci gaba da rike madafun iko na su, ba makawa, shugabancin, zai samu matsala,  wanda hakan zai kuma sanya, talakwan kasar, su ci gaba da ji a jikinsu.

Wani abin dubi a nan shi ne, yankin Arewacin kasar nan, ne ya fi fuskantar matsalar ta rashin tsaro, a fadin daukacin kasar.

Akasarin ‘yan Nijeriya dai, na fatan jami’an tsaro, su ci gaba da kamin da suke yi, na yakar ‘yan ta’adda da kuma kawo karshen aikata daukacin manyan laifuka.

Kasar dai, na ci gaba da zama a cikin fargabar hare-haren ‘yan bindiga daji da  na ‘yan ta’adda da masu yin garkuwa da mutane da kuma ci gaba da samun rikice-rikice, a cikin alumma, wanda hakan, ke ci gaba da tarwatsa tattalin arzikin kasar.

Hakazalika, abinda ‘yan kasar ke fata a 2026, shi ne, hada karfi da karfe, a tsakanin jami’an saro domin kawo karshen matsalar, musamman kuma a tabbatar da an yi gaskiya, wajen magance  kalubalen.

Dole ne a samar wa da jami’an tsaron kasar da kayan aiki, musamman domin su samu sukunin gudanar da aikinsu, na wanzar da tsaron rayuka da kuma dukiyoyin ‘yan kasar, inda yin hakan, ba zai sanya su rinka karbar na Goro, a gun masu yiwa tsaron kasar, zagon kasa ba.

Bugu da kari, ya kuma kamata Gwamnatin Tarayya ta nemi daukin kasashen waje, domin ta lalubo da mafita, kan kalubalen rashin tsaron kasar wanda kasar ta shafe shekaru 16, ta na fuskanta.

Koda yake dai, Gwamnatin shugaba Bola The Tinubu, ta fara daukar irin wannan matakin, duba da yadda ta nemi daukin kasar Amurka, inda Jiragen yakinta, suka kai munanan hare-hare kan sansanonin ‘yan bindiga da ke a jihar Sokoto.

Ya kamata kuma gwamnatin, ta kara fadada hadakar ta da Amurak, musamman wajen samun kayan yaki na zamani, domin ci gaba da yakar ‘yan bindiga da kuma ‘yan ta’adda, musamman irinsu Al Kaeda da ISIS, da suka kusto cikin kasar, suke aikata ta’addancin su.

Hakazalika, ya wajaba kasar, ta nemi taimakaon kasasshn da take abotaka da su, domin ta murkushe ‘yan ta’adda da kuma ‘yan bindiga a 2026.

Dole ne kuma, Gwamnatin Bola Tinubu ta ajiye batun siyasa a gafe guda, domin ta yaki ‘yan ta’addar.

Yau a Nijeriya, ‘yan gudun hijira sun kai kimanin miliyan takwas, inda kuma wasu dubban mutane, ‘yan bindiga, ke ci gaba da rike su haka manoma da dama, basa iya zuwa gonakansu, domin noma su, saboda suna jin tsoron, kar a kashe su.

Zuba jari na kai tsaye daga ketare, zai taimaka wajen rage kangin talauci , musamman a  tsakanin talakwan kasar.

‘Yan Nijeriya ba wai kawai batun siyasa suke son ji, a fatar baki ba, amma suna sun su gani a kas.

Samar da fasahar zamani ta yin zabe musamman IREB, hakan ya sanya, ‘yan Nijeriya na da yakinin za a gudanar da sahihin zabe a 2027, musamman ganin yadda a zaben shugaban kasa na 2023, aka yiwa ‘yan Nijeriya, sakiyar da ba ruwa, ta hanyar lalata fatan da suke da shi, na samun shugabanci na gari.

Kan batun sauye-sauyen da aka samar na haraji ‘yan Nijeriya da dama, na fatan a gudanar da adalaci wajen aiwatar da sauye-sauyen.

‘Yan Nijeriya da dama dai, a 2026, na  fatan ganin cewa, kowanne dan kasar, ya amfana, ba wai kawai wasu ‘yan tsiraru kadai ne, za su amafana da ba.

Nijeriya
Leadership Hausa
Website |  + posts Bio
  • Leadership Hausa
    Batun Yawan Bashin Da Nijeriya Ke Ciyowa Daga Ketare
  • Leadership Hausa
    Tallafa Wa Yara Masu Buƙatu Na Musamman Shi Ne Burina
  • Leadership Hausa
    Dole Mata Su Rungumi Sana’o’i Domin Tsira Daga Takaicin Zamani —Ramatu Bello
  • Leadership Hausa
    Batun Dakile Shan Taba Sigari A Tsakanin Yara A Nijeriya
Nijeriya
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Badaƙalar Binciken Hukumar Bogi: Gbajabiamila Ya Gurfana Gaban ICPC
  • Sulaiman
    Sin Da Amurka Na Tuntubar Juna Game Da Inganta Mu’amalar Shugabanninsu A Bana
  • Sulaiman
    Wang Yi: Kasar Sin Na Matukar Goyon Bayan Manufofin MDD
  • Sulaiman
    Mayar Da Muradun Jama’a A Gaban Komai: Daga Hikimar Da Aka Gada Tsawon Dubban Shekaru Zuwa Akidar Zamani

MASU ALAKA

Ana Ci Gaba Da Tafka Muhawara Kan Shirin Gwamnati Na Haramta Masana’atun Sarrafa Robobi
Ra'ayinmu

Ana Ci Gaba Da Tafka Muhawara Kan Shirin Gwamnati Na Haramta Masana’atun Sarrafa Robobi

July 10, 2026
Kisan Gillar Marabar Jos: Bai Kamata Jinin Malama Ummulkhairi Ya Tafi A Banza Ba
Ra'ayinmu

Kisan Gillar Marabar Jos: Bai Kamata Jinin Malama Ummulkhairi Ya Tafi A Banza Ba

July 3, 2026
sikila
Ra'ayinmu

Buƙatar Mayar Da Hankali Wajen Kawo Ƙarshen Ciwon Sikila A Nijeriya

June 26, 2026
Next Post
Nijeriya

Atiku Ya Fara Neman Mulki Tun Ina NYSC – Datti Baba-Ahmed

LABARAI MASU NASABA

ICPC

Badaƙalar Binciken Hukumar Bogi: Gbajabiamila Ya Gurfana Gaban ICPC

July 21, 2026
Sin Da Amurka Na Tuntubar Juna Game Da Inganta Mu’amalar Shugabanninsu A Bana

Sin Da Amurka Na Tuntubar Juna Game Da Inganta Mu’amalar Shugabanninsu A Bana

July 20, 2026
Wang Yi: Kasar Sin Na Matukar Goyon Bayan Manufofin MDD

Wang Yi: Kasar Sin Na Matukar Goyon Bayan Manufofin MDD

July 20, 2026
Mayar Da Muradun Jama’a A Gaban Komai: Daga Hikimar Da Aka Gada Tsawon Dubban Shekaru Zuwa Akidar Zamani

Mayar Da Muradun Jama’a A Gaban Komai: Daga Hikimar Da Aka Gada Tsawon Dubban Shekaru Zuwa Akidar Zamani

July 20, 2026
NAFDAC Ta Kama Jabun Giya, Gurbataccen Abinci Da Motocin Man Kalanzir

NAFDAC Ta Kama Jabun Giya, Gurbataccen Abinci Da Motocin Man Kalanzir

July 20, 2026
Karfin Sin A Bangaren AI Ya Samarwa Kasashe Masu Tasowa Damarmakin Cin Gajiyar Fasahar

Karfin Sin A Bangaren AI Ya Samarwa Kasashe Masu Tasowa Damarmakin Cin Gajiyar Fasahar

July 20, 2026
Sin Ta Zamo Kan Gaba A Duniya A Fannin Kirar Mutum-Mutumin Inji

Sin Ta Zamo Kan Gaba A Duniya A Fannin Kirar Mutum-Mutumin Inji

July 20, 2026
Shari’ar Malami Ba Za Ta Dakatar Da Burinsa Na Gwamna Ba, Inji Jam’iyyar ADC Ta Kebbi

Shari’ar Malami Ba Za Ta Dakatar Da Burinsa Na Gwamna Ba, Inji Jam’iyyar ADC Ta Kebbi

July 20, 2026
Kimi K3 Ya Bayyana Yunkurin Sin Na Raya Fasahar AI A Bayyane Ta Yadda Kowa Zai Amfana

Kimi K3 Ya Bayyana Yunkurin Sin Na Raya Fasahar AI A Bayyane Ta Yadda Kowa Zai Amfana

July 20, 2026
Kwamandojin Kungiyar Ansaru Biyu Sun Amsa Laifin Garkuwa Da Mutane A Kotu

Kwamandojin Kungiyar Ansaru Biyu Sun Amsa Laifin Garkuwa Da Mutane A Kotu

July 20, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.