ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

ADC Reshen Kaduna Ta Buƙaci Gwamnati Ta Daina Tsangwamar El-Rufai

by Muhammad
5 months ago
ADC

Jam’iyyar ADC reshen Jihar Kaduna ta buƙaci gwamnati da ta dakatar da abin da ta kira ci gaba da tsanantawa da muzgunawa da daukar matakan siyasa da ake ɗauka kan tsohon gwamnan jihar, Nasir Ahmed El-Rufai, da sauran shugabannin adawa a jihar da ma ƙasa baki ɗaya.

Da yake magana a wani taron manema labarai da aka gudanar a Kaduna ranar Talata, tsohon kwamishinan ilimi na jihar, Sani Bello, wanda ya yi magana a madadin shugabannin ADC na jihar, ya yi kira da a mutunta doka ba tare da gundaya wani sharaɗi ba, ciki har da bin ƙa’idojin shari’a da kuma kare martabar kotuna.

  • El-Rufai Ya Ƙaryata Rahoton Goyon Bayan Yanki Ko Wani Mutum A Zaɓen 2027
  • Kwamitin Zartarwa Na ADC Na Ƙasa Ya Yi Watsi Da Bangaran David Mark Da Bala Gombe, Ya Naɗa Shugabancin Riƙo

Bello ya buƙaci a kawo ƙarshen amfani da hukumomin tsaro da na yaƙi da cin hanci da rashawa wajen cimma muradun siyasa na ɓangarenci.

ADVERTISEMENT

A cewar shugabannin ADC, sun buƙaci a dawo da cikakken tsarin dimokuraɗiyya, ciki har da ‘yancin siyasa, ‘yancin jam’iyyu, da za su ci ‘yancin kansu.

Ya ce, “Wannan bayani ya biyo bayan nazari mai zurfi kan abubuwan da ke faruwa a baya-bayan nan, waɗanda ke nuna wani yanayi mai tayar da hankali na amfani da hukumomin gwamnati ba daidai ba da watsi da bin ƙa’idojin shari’a, da kuma raunana tsarin dimokuraɗiyya.”

LABARAI MASU NASABA

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

Rashin Mulki Ke Firgita Atiku – Kakakin APC Na Kaduna

Ya ƙara da cewa, “Dangane da haka, shugabancin ADC na Jihar Kaduna na buƙatar a gaggauta dakatar da duk wata tsangwama da barazana da gurfanar da Mallam Nasir Ahmed El-Rufai da sauran ‘yan adawa a gaban kotu bisa dalilan siyasa. Haka kuma, a saki duk wanda aka tsare ba bisa ka’ida ba, ko kuma a gudanar da shari’a cikin gaskiya da adalci.”

Bello ya jaddada cewa dimokuraɗiyya tana bunƙasa ne idan akwai adawa mai ƙarfi, mutunta haƙƙoƙin ɗan adam, da kuma aiwatar da adalci ba tare da son kai ba.

Ya ce halin da ake ciki a yanzu na barazana ga waɗannan muhimman ginshiƙai, tare da iya raunana amincewar jama’a ga gwamnati da cibiyoyin dimokuraɗiyya.

A ƙarshe, jam’iyyar ADC ta yi kira ga hukumomin da abin ya shafa, ƙungiyoyin fararen hula, da kuma ƙasashen duniya da su lura da halin da ake ciki tare da ɗaukar matakan da suka dace domin kare dimokuraɗiyya, adalci da bin doka a Jihar Kaduna da Nijeriya gaba ɗaya.

ADC
Muhammad
+ postsBio
  • Muhammad
    Gwamna Yusuf Ya Umarci Jami’an Tsaro Su Gano Waɗanda Suka Kashe Danshagamu
  • Muhammad
    Yadda Na Tsira Daga Cutar Mashaƙo A Katsina: “Na Fara Da Tsartuwar Jini Tare Da Yawu”
  • Muhammad
    An Naɗa Yusuf Nasidi Nasir A Matsayin Talban Barayan Kano
  • Muhammad
    Wani Kamfani Ya Tallafa Wa Masu Sana’ar Shayi A Kano

MASU ALAKA

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu
Manyan Labarai

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

September 9, 2026
Rashin Mulki Ke Firgita Atiku – Kakakin APC Na Kaduna
Siyasa

Rashin Mulki Ke Firgita Atiku – Kakakin APC Na Kaduna

September 9, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027
Siyasa

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Next Post
Amurka Da Iran Sun Amince Da Tsagaita Wuta Na Mako Biyu

Amurka Da Iran Sun Amince Da Tsagaita Wuta Na Mako Biyu

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Ceto Fasinjoji Uku Da ‘Yan Bindiga Suka Harba A Filato

Sojoji Sun Ceto Fasinjoji Uku Da ‘Yan Bindiga Suka Harba A Filato

September 10, 2026
Xi Zai Halarci Taron BRICS Karo Na 18 A Indiya

Xi Zai Halarci Taron BRICS Karo Na 18 A Indiya

September 10, 2026
Rodri Ya Nemi Afuwar Valencia Dangane Da Kalaman Da Yayi Akanta

Rodri Ya Nemi Afuwar Valencia Dangane Da Kalaman Da Yayi Akanta

September 10, 2026
Za A Gudanar Da Taron Koli Na Shugabannin Harkokin Masana’antu Da Cinikayya Na APEC Na 2026 A Shenzhen

Za A Gudanar Da Taron Koli Na Shugabannin Harkokin Masana’antu Da Cinikayya Na APEC Na 2026 A Shenzhen

September 10, 2026
Amurka Ta Bai Wa Nijeriya Sabbin Kayan Yaƙi Domin Yaƙi Da Ta’addanci

Amurka Ta Bai Wa Nijeriya Sabbin Kayan Yaƙi Domin Yaƙi Da Ta’addanci

September 10, 2026
Xi Ya Bukaci A Kara Azamar Dakile Aukuwar Muggan Hadurra Sakamakon Aukuwar Gobara A Wani Jirgin Ruwan Dakon Kayayyaki

Xi Ya Bukaci A Kara Azamar Dakile Aukuwar Muggan Hadurra Sakamakon Aukuwar Gobara A Wani Jirgin Ruwan Dakon Kayayyaki

September 10, 2026
ADC

Jerin Bankuna 32 Da Aka Amince Su Sayar Da Hannun Jarin Matatar Dangote

September 10, 2026
ADC

Uganda Za Ta Fara Fitar Da Man Fetur Zuwa Ƙasashen Waje

September 10, 2026
Cutar Mashaƙo Ta Ɓarke A Kano, Katsina Da Filato

Mashaƙo: Adadin Mutanen Da Suka Rasu Sun Kai 27 A Filato

September 10, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

Wane Ne Dan Shagamu: Su Wane Ne Suka Kashe Shi A Kano?

September 10, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.