ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

An Cafke Mutum 7 Kan Satar Waya Da Fasa Gidaje A Jihar Yobe

by Rabi'u Ali Indabawa
5 months ago
Cafke

Rundunar ‘Yansandan Jihar Yobe ta kama wasu mutum bakwai da ake zargi mambobin wata kungiyar masu aikata laifuka, wadanda ake zargin suna da hannu a fasa gidaje, sata da kuma kwacen wayoyi a wasu sassan Damaturu, babban birnin jihar.

‘Yansanda sun ce an cafke wadanda ake zargin ne a wani samame na hadin gwiwa da jami’an sashen “A Dibision” na Damaturu suka gudanar tsakanin ranakun 16 zuwa 19 ga Afrilu, 2026.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar, SP Dungus Abdulkarim, ya fitar a ranar Talata.

ADVERTISEMENT

Abdulkarim ya ce samamen ya mayar da hankali ne kan ayyukan ta’addanci a yankunan Nayinawa, Bindigari, One Million Road da Pompomari.

Sanarwar ta ce: “Rundunar ‘Yansandan Jihar Yobe ta sake samun gagarumar nasara a kokarinta na yaki da laifuka da masu aikata su a fadin jihar.”

LABARAI MASU NASABA

Direbobi 123 A Kano Suna Fuskantar Tuhuma Kan Laifin Keta Dokokin Amfani Da Lambar Mota

‘Yansanda Sun Kama Mutum Biyu Kan Zargin Damfarar Wayar Salula A Jihar Adamawa

Abdulkarim ya bayyana sunayen wadanda ake zargin da suka hada da Usman Mohd mai shekara (20), Abubakar Adamu mai shekara (20), Mohd Ibrahim mai shekara (22), Mohd Goni mai shekara (19), Khalifa Mohd (mai shekara 19), Abubakar Mohammed mai shekara (19), da Ali Mohammed mai shekara (23).

Ya kuma bayyana cewa wadanda ake zargin sun amsa aikata laifuka da dama yayin bincike.

“Yayin tambayoyi, sun amsa cewa suna da hannu a jerin laifukan fasa gidaje, sata da kwacen waya a yankunan da abin ya shafa,” in ji shi.

Kakakin ‘yansandan ya kara da cewa sun amince da satar wayoyin Android guda bakwai da kuma wayoyi na maballi guda biyu, inda aka riga aka kwato guda shida daga cikinsu.

“Sun amsa cewa sun sace wayoyin Android guda bakwai da kuma wayoyi biyu na maballi. An riga an kwato guda shida daga cikin wayoyin da aka sace,” in ji Abdulkarim.

Ya kara da cewa bincike na ci gaba, kuma za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala binciken.

“Bincike na gudana domin gurfanar da su yadda ya dace,” ya kara.

A wani bangare, Kwamishinan ‘Yansanda na jihar, Usman Kanfani Jibrin, ya yaba wa jami’an da suka gudanar da aikin, tare da bukatar su ci gaba da irin wannan kokari.

Sanarwar ta ce: “Kwamishinan ‘Yan Sanda ya yaba da kwarewa da jajircewar jami’an, tare da ba da umarnin ci gaba da gudanar da samame kan maboyar masu aikata laifuka a fadin jihar.”

Har ila yau, CP din ya jaddada muhimmancin amfani da bayanan sirri wajen aikin ‘yan sanda, tare da kira ga al’umma da su ci gaba da bai wa jami’an tsaro hadin kai.

“Ya jaddada bukatar kara sa ido da kuma amfani da bayanan sirri wajen aikin ‘yansanda, tare da rokon jama’a su ci gaba da bayar da sahihan bayanai domin taimakawa wajen yaki da laifuka,” in ji Abdulkarim.

A gefe guda kuma, Rundunar ‘Yansandan Jihar Ogun ta kama wasu mutum hudu da ake zargi ‘yan kungiyar asiri ne bisa zargin kai hari, fashi da makami da kuma mallakar bindiga ba bisa ka’ida ba.

An bayyana sunayen su da Samson John mai shekaru 25, Olufowora Michael mai shekaru 28, Odeh Samuel Ejeh mai shekaru 25, da Olajide Jeremiah mai shekaru 28.

Cafke
Rabi'u Ali Indabawa
+ postsBio
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ƙungiya Ta Gudanar Da Zaɓen Sabbin Shugabanninta A Abuja
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Jihar Katsina Da UNICEF Sun Ceto Rayuwar Yara Ta Hanyar Samar Da Abinci Mai Gina Jiki
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Yadda Tinubu Ya Kashe Naira Biliyan 37.64 A Tafiye-tafiye
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ta’addaci: Mutum 14,500 Sun Bace A Arewa Maso Gabas

MASU ALAKA

Direbobi 123 A Kano Suna Fuskantar Tuhuma Kan Laifin Keta Dokokin Amfani Da Lambar Mota
Kotu Da Ɗansanda

Direbobi 123 A Kano Suna Fuskantar Tuhuma Kan Laifin Keta Dokokin Amfani Da Lambar Mota

July 18, 2026
An Kama Matashi A Kano Kan Zargin Kashe Abokinsa
Kotu Da Ɗansanda

‘Yansanda Sun Kama Mutum Biyu Kan Zargin Damfarar Wayar Salula A Jihar Adamawa

July 18, 2026
Disu
Kotu Da Ɗansanda

IGP Disu Ya Hana Jami’an Ƴansanda Yin Amfani Da TikTok Da Instagram Da Sauransu

June 26, 2026
Next Post
Rashin Ingantattun Cibiyoyin Kiwon Lafiya Da Talauci Ke Sa Al’umma Amfani Da Unguwarzoma Wajen Haihuwa A Yankunan Arewa

Rashin Ingantattun Cibiyoyin Kiwon Lafiya Da Talauci Ke Sa Al’umma Amfani Da Unguwarzoma Wajen Haihuwa A Yankunan Arewa

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.