Jerin Sabbin Jarumai Matan Kannywood Takwas Da Za Su Ja Zarensu A 2027
Masana'antar Kannywood tana samun gagarumin sauyi, a halin yanzu, hakan na zuwa ne yayin da ake kara samun wasu jarumai mata. Irin waxannan sabbin fuskokin jaruman mata, sun nuna kwazo da zai sa su ci gaba a harkar. Wannan sharhin zai yi duba ne kan jeren jarumai mata da masu bibiyar masana’antar ke ganin za su ja zarensu a shekarar 2027. Aisha Soba: Ta farkonsu daga cikin wannan jeren ita ce, Aisha Soba, wacce kuma ta na xaya daga cikin sabbin fuskokin da suka yi fice cikin sauri a Kannywood. Soba, har ta kai ga shiga cikin jerin rukunin jarumai mata da ke a kan gaba wajen fitowa a cikin fina-finai". Kazalika jarumar ta shahara wajen iya fitar da tsarin da aka ba ta cikin natsuwa. Tauraronta ya fara haskawa ne a shekarar ta 2025, inda ta fito a wasu fitattun wakoki, kamar irin su 'Makauniya' da Auta MG ya rera wakar kamfanin Arewa Medium ya xauki nauyin fim xin, inda ta fito, a matsayin makauniya a bidiyon wakar. Fatima Ibrahim: Matashiyar jarumar, tauraruwa ce da ke kara samun karvuwa a wurin masu kallo musamamn masoyanta. Jarumar na samun karvuwar ne saboda karsashi da kuma kwarewa a fina-finai na zamani, inda hakan ya sanya, ta shiga cikin jeren waxanann jarumai mata, da za su ja Zarensu a baxi. Asmau Jika: Ita kuwa wannan jarumar, ta kasance jigo ce, a tsakanin sabbin jarumai mata da ke tasowa. Jarumar, ta mai kazar-kazar da kuzar, ta kuma kasance mai jini a jiki, musamman a cikin fina-finan da ta fito. Asmau na da tasiri a fina-finan da ake saki a dandalin YouTube, wanda hakan, ya sanya, ita ma bi sahun wannan jeren. Aisha Muhammed Jogana: Tun bayan fitowarta a shirin Jahilan kauye, jarumar ta kuma fito a cikin wasu fina-finai masu dogon zango kamar irin su in da Ranka da Rayuwar Duniya, hakan ya sanya ta shiga cikin jeren jaruman mata, da masu kallo za su sanya ido a kansu a 2027. Wasu daga cikin masu fashin baki a masana’antar ta Kannywood na hasashen Aisha za ta taka muhimmiyar rawa a masana’antar, a 2027. Ummassalama Sadik: Wannan jarumar da ake yi wa lakabi da Salma Gezawa, ta shafe lokaci tana aikin bayan fage, sai dai, Gezawa, ta fito fili a matsayin babbar jaruma a fim xin Baban Ladi. ...



















