Yunkurin Dauda Lawal Na Bunkasa Bangaren Ma’adanan Jihar Zamfara
Yunkurin Dauda Lawal Na Bunkasa Bangaren Ma'adanan Jihar Zamfara
Yunkurin Dauda Lawal Na Bunkasa Bangaren Ma'adanan Jihar Zamfara
Shugaban kungiyar Fulani ta Miyetti Allah Kautal Hore, Alhaji Abdullahi Bello Bodejo ya karyata zargin da a ke yi masaa kan aikata laifuka 12 da ya hada da halatta kudin haramun da kuma hannu a tallafa wa ayyukan ta’addanci. Bodejo wanda ya gurfana a gaban babban kotun tarayya da ke Abuja a ranar Alhamis na maida bayani ne a kan zargin da a ka gabatar a kansa da Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC ke yi, a karkashin mai sharia Inyang Ekwo. A yayin fara shari’an a karo na farko, Hukumar ta bakin lauyanta Wahab Shittu, ta zargi shugaban na Miyetti Allah da aikata laifin hallata kudin haram da ta ce ya kai dalar Amurka milayan 2 da doriya. Bayan karyata tuhumar da ke yi masan, lauyan Hukumar EFCC ya bukaci kotun da ta sa ranar fara sauraron bayanai a kan karar da su ka shigar, sai kuam bukatar cigaba da tsare shi har zuwa lokacin. Da ya ke mayar da martini, lauyan Shugaban na Miyetti Allah mai suna Ahmed Raji ya bukaci kotun da ta bada belin jagoran kamar yadda ya ce ya gabatar tun a farko. Lauyan ya shaidawa kotun cewa laifin da a ke tuhumar wanda ya ke karewan na cikin rukunin wadanda doka ta amince a bada beli a kansu, bukatar da lauyan EFCC ya bayyana ja a kai. A karshe kotun ta bada umarnin a cigaba da tsare wanda a ke tuhumar a hannun Hukumar ta EFCC, tare da sanar da ranar 20 ga watan nan ta Yuli a matsayin ranar yanke hukunci a kan bukatar bada belinsa.
Muaaddashin Shugaban Hukumar da ake shirin kafa ta National Institute for Public Health and Infectious Diseases (NIPHID) da ke Zariya,...
Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta ƙaddamar da wasu muhimman ayyuka a Hadejia ta Jihar Jigawa, waɗanda suka da...
Ƙungiyar National Progressiɓes Councillors’ Forum (NPCF), wadda ke wakiltar kansiloli 10,378 na jam’iyyar APC a faɗin Nijeriya, ta yi kira...
Bankin Duniya, ta ɗora Tashoshin Jiragen Ruwa na Apapa da na Tin Can Island, a mizanin ƙasashen 20, a duniya...
Shugaban matasan jam’iyyar African Action Congress (AAC), Comrade Yahaya M. Abdullahi, ya bayyana damuwa kan abin da ya kira karkatar...
Ƙungiyar Dandalin Hadin Kai da ci gaban Kansiloli ta Kasa 'National Progressives Councillors’ Forum (NPCF)', mai wakiltar kansilolin jam'iyyar APC...
A yayin da al’ummar musulmin duniya ke murnar shiga sabuwar shekarar musulu7nsi ta Hijira 1448, an yi hasashen cewa, duk...
Muna gina tsarin tashoshin jiragen ruwa mai inganci wanda zai iya gogayya a matakin duniya, domin ƙarfafa sauƙaƙa harkokin kasuwanci,...
© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.
© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.