An Zargi Firaministar Japan Da Sassauta Kalamai Dangane Da Laifukan Da Kasarta Ta Aikata Na Nuna Karfin Tuwo
A yau Litinin ne kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya soki lamarin kalaman da firaministar Japan Sanae...
A yau Litinin ne kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya soki lamarin kalaman da firaministar Japan Sanae...
Da karfe 11:02 na ranar yau Litinin, an cimma nasarar harba tauraron dan adam na SEO ta hanyar amfani da...
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi kira da a yi kokarin koyi da hangen nesa da kaifin tunani irin na marigayi tsohon shugaban Sin, Jiang Zemin. Xi wanda shi ne sakatare janar na kwamitin kolin JKS kuma shugaban hukumar koli mai kula da ayyukan soji, ya bayyana haka ne yau Litinin, yayin taron da aka yi a Beijing albarkacin cika shekaru 100 da haihuwar marigayi Jiang Zemin. A cewar shugaba Xi, Jiang Zemin ya daukaka burin JKS da kasar ta hanyar daukar manyan matakai da dama bisa mahangar kasa da kasa da kuma hangen nesa. Ya kuma gudanar da shirye-shirye cikin kaifin basira domin gina al’umma mai matsakaicin ci gaba ta kowace fuska. Haka kuma, ya gabatar da jerin manufofin harkokin waje da muhimman dabaru domin samun duniya da ke da rarrabuwar iko tsakanin kasa da kasa, da dunkulewar tattalin arzikin duniya bisa turbar da ta dace. Shugaba Xi Jinping ya kara da cewa, a wannan sabuwar tafiya, abu ne mai muhimmanci a aiwatar da sabuwar falsafar ci gaba a dukkan fannoni da gaggauta kirkiro sabuwar hanyar ci gaba da samun nasara mai kwari wajen inganta ci gaba mai inganci. Haka kuma, ya yi kira da a kara kokarin gina al’umma mai makomar bai daya ga dan adam da kara kuzari ga zaman lafiya da ci gaba a duniya. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
Shekaru 90 da suka gabata, wasu matasa sanye da takalman ciyawa suka haye tsaunuka masu dusar kankara da ratsa filin...
A yau Lahadi ne kasar Sin ta yi nasarar harba sabon rukunin taurarin dan Adam daga cibiyar harba kumbuna na...
Kakakin Ofishin jakadancin Sin dake kasar Japan, ya soki lamirin ziyarar da wasu manyan jami’an gwamnatin kasar Japan suka kai haikalin Yasukuni, matakin da ya ce ya illata nasarorin da aka cimma bayan yakin duniya na biyu, da odar kasa da kasa da aka cimma bayan yakin. Da yake amsa tambayar manema labarai dangane da batun a jiya Asabar, kakakin ya ce, ziyara da karrama haikalin Yasukuni, makwancin manyan kusoshin kasar da suka aikata munanan laifukan yaki yayin yakin duniya na biyu, wanda firaministanr kasar Sanae Takaichi, da wasu ministocin kasar, da manyan ‘yan siyasar Japan suka gudanar, abu ne da Sin ke matukar adawa da shi, kuma ta yi Allah wadai tare da gabatar da korafi mai karfi, da nuna rashin jin dadi kan hakan ga bangaren Japan. Kakakin ya kara da cewa, Sin na kira ga bangaren Japan da ya yi matukar karatun ta nutsu dangane da laifukan da ya aikata a tarihi, ya yi koyi daga abubuwan da suka gabata, ya martaba alkawuran neman ci gaba ta hanyar lumana, kana ya aiwatar da matakai na hakika don kaucewa amfani da karfin tuwo, da dakatar da mummunan yanayin sake farfado da rundunar soji, da kaucewa sake sanya kasar a matsayi na abar tuhuma a tarihi. (Saminu Alhassan)
Yayin da ake gudanar da babban taro kan ilimin ginshikin kimiyya na duniya wato ICBS na shekarar 2026 a birnin...
A gobe Lahadi, za a wallafa wata makala ta shugaba Xi Jinping, babban sakataren kwamitin tsakiya na Jam'iyyar Kwaminis ta...
Yau Asabar 15 ga watan nan ne ake cika shekaru 81 da mika wuyar da kasar Japan ta yi ba...
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ya amsa tambayar da aka yi masa a yau Asabar 15...
© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.
© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.