Amadou Magagi, masanin harkokin cinikayya da tattalin arziki na kasar Niger, ya bayyana manufar kasar Sin ta soke haraji kan kayayyakin kasashen Afrika 53 da ke da huldar diplomasiyya da ita, a matsayin wadda ta wuce batun alfanun cinikayya, inda ya ce tana nuna dadadden kudurin Sin na samun ci gaba na baya daya, da dunkulewar tattalin arzikin duniya da hadin gwiwa bisa ka’idojin mutunta juna da daidaito da moriyar juna. Amadou Magagi, masani a cibiyar bunkasa cinikayya da masana’natu ta Niger, ya bayyana haka ga kamfanin dillancin labarai na Xinhua, inda ya kara da cewa, manufar ta bayar da damar aiwatar da alkawarin da aka yi karkashin dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afrika, na tallafa wa ayyukan masana’antu a Afrika da karfafa shigar nahiyar cikin tsarin samar da kayayyaki na duniya da kirkiro karin damarmaki ga harkokin kasuwanci na nahiyar. Da yake bayani game da alfanun da ake sa ran Niger za ta samu, Amadou Magagi ya bayyana manufar a matsayin wata muhimmiyar dama ta musammam. Ya ce Niger tana da dimbin amfanin gona da dabbobi da albarkatun karkashin kasa, haka kuma tana da karfi a bangarorin da suka shafi ridi da gyada da gurjiya da gam da aya da kayayyakin dabbobi da kuma kayayyaki masu daraja. Ya ce samun damar shiga katafariyar kasuwar Sin za ta taimaka wajen kara yawan abubuwan da Niger ke fitar wa da inganta sarrafa albarkatu a cikin gida da kuma kirkiro karin guraben ayyukan yi. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
Read moreDetailsYau Asabar, babbar hukumar kula da kasuwa ta Sin wato SAMR, ta...
Read moreDetailsAn gudanar da wani taro a kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya,...
Read moreDetailsAlkaluman da hukumomin kasar Sin suka gabatar a jiya Juma'a sun nuna...
Read moreDetailsMa'aikatar tsaron kasar Sin ta soki kokarin Japan na gangancin fadada karfin...
Read moreDetailsZuwa yau Juma’a, hanyar tsakiya ta katafaren aikin karkatar da ruwa daga yankin kudanci zuwa arewacin kasar Sin, ta samar da ruwa sama da cubic mita biliyan 80, inda mutane kusan miliyan 118 na birane 27 suka amfana. Katafaren aikin karkatar da ruwa, wanda shi ne irinsa mafi girma a duniya, na tura ruwa ta wata doguwar hanya daga yankin kudancin kasar Sin mai arzikin ruwa zuwa yankunan arewacin kasar, inda daruruwan miliyoyin mutane suka taba fama da matsanancin rashin ruwa, bisa mizanin MDD. a cewar kamfani mai kula da aikin, bayan shafe shekaru 12 tana aiki, hanyar ta tsakiya ta taimaka wajen samar da daidaito a fannin albarkatun ruwa da samar da ruwan sha da farfado da muhallin halittun ruwa da sake karfafa wadatar ruwa a kasar Sin. (Mai fassara: Fa’iza Msutapha)
Read moreDetailsA yau, hukumar kwastam ta kasar Sin ta fitar da bayanan kididdiga...
Read moreDetailsA ’yan kwanakin baya bayan nan, wani rahoto daga rukunin masanan Amurka,...
Read moreDetailsTakardar tsaro ta farko da aka fitar bayan firaministar Japan Takaichi Sanae...
Read moreDetailsAn gudanar da bikin bude gadar kogin Nyong ta Kamaru, wadda kamfanin...
Read moreDetails© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.
© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.