ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Tuesday, July 14, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kasashe 10 Da Suka Fi Yawan Masu Fama Da Yunwa A Duniya

by Sulaiman and Rabi'u Ali Indabawa
2 months ago
Yunwa

Wani sabon rahoto da kungiyar Global Network Against Food Crises (GNAFC) mai yaki da karancin abinci a duniya ta fitar, ya nuna damuwa kan karuwar matsalar yunwa a fadin duniya.

Cikin rahoton kungiyar na 2026, da ta saba fitarwa shekara-shekara ya nuna cewa fiye da mutum miliyan 266 a kasashe 47 na duniya fuskantar matsananciyar yunwa.

GNAFC ta lissafo kasashe 10, ciki har da Nijeriya da aka fi samun masu fama da matsalar yunwa a duniya, a rahoton nata na 2026.

ADVERTISEMENT

Kungiyar ta kuma yi gargadin samun karuwar matsalar idan ba a yi kokarin magance matsalolin da ke haddasa karuwar yunwar ba.

La’akari da rahoton kungiyar, GNACF da kuma na shirin Samar da Abinci na Majalisar Dinkin Duniya, WFP, mun lissafo kasashe 10 da ke kan gaba a yawan masu fama da yunwa a duniya.

LABARAI MASU NASABA

Mun Ɗauki Nauyin Karatun Masu Digiri Ta Hanyar Sayar Da Ƙosai Da Ƙuli-ƙuli —Wasu Ƴan Kasuwa

Matsalar Tsaro: Masana Sun Firgita Da Fitowar Sabon Bidiyon Bello Turji

Nijeriya – Mutum Miliyan 35

Nijeriya ce kan gaba cikin jerin kasashe da rahoton na GNAFC ya ambata a matsayin wadda taka fi yawan masu fama da yunwa a duniya.

Shirin Samar da Abinci na Majalisar Dinkin Duniya WFP ya bayyana cikin wani rahoto da ya fitar a watan Maris na 2026, cewa mutum miliyan 35 ne ke fama da matsalar yunwa a Nijeriya.

Rahoton na WFP ya ce yankin arewa maso gabashin Nijeriya ne inda matsalar ta fi katutu, inda kananan yara da mata suka fi fuskantar matsalar.

WFP ya ce Jihohin Borno da Yobe da Adamawa ne matattarar matsalar, inda kusan mutum miliyan 5.8 ke fuskantar matsalar yunwa a jihohin uku.

DR Congo – Mutum Miliyan 26.6

A cewar alkaluman Shirin Samar da Abinci na Majalisar Dinkin Duniya da Shirin lura da wadatar abinci a kasashen duniya (IPC) kimanin mutum miliyan 26.6 ne ka fama da matsalar yunwa a kasar Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo.

IPC ta ce daga cikin wadannan alkaluma akwai kimanin mutum miliyan 3.9 da ke cikin tsananin yunwa.

Kungiyar Abinci da Noma ta Duniya (FAO) da kuma shirin WFP sun yi gargadin cewa karuwar matsalar jin kai a kasar ta DR Congo ka iya kara tsananta matsalar yunwa a kasar, wadda ke fama da rikici.

Sudan – Mutum Miliyan 19

Cikin rahoton da Shirin Samar da Abinci na Majalisar Dinkin Duniya ya fitar a watan Afrilun da muke ciki ya nuna cewa fiye da mutum miliyan 19 ne ke fama da matsalar yunwa a kasar Sudan.

Rahoton ya bayyana rikicin da kasar ke ciki da hana kungiyoyin agaji kai kayan tallafi a matsayin abubuwan da suka kara ruruta matsalar.

Shirin na WFP ya ce kusan rabin al’ummar Sudan na fama da matsalar yunwa, musamman a wuraren da ake fama da yake-yake, kamar El-Fasher, inda fiye da mutum miliyan shida ke kan hanyar fadawa kangin yunwa.

Kasar Sudan na fama da yakin basasa tun 2023, lamarin da ya tilasta wa al’umomi da dama barin gidajensu.

Afghanistan – Mutum Miliyan 17.4

Wani rahoton hadin gwiwa na Majalisar Dinkin Duniya da Kungiyar Tarayyar Turai a 2025 ya nuna cewa Afghanistan ce kasa ta biyar cikin kasashen da mutanensu suka fi fama da yunwa a duniya.

Rahoton kungiyar da ke lura da matsalar abinci ta duniya, GRFC ya nuna cewa kimanin mutum miliyan 17.4 ne ke fama da matsalar yunwa a kasar ta Afghanistan.

A cewar GRFC kusan kashi 36 na al’ummar kasar na fuskantar matsalar yunwa.

Yemen – Mutum miliyan 17

Yakin basasar da aka kwashe fiye da shekara 10 ana gwabzawa a kasar Yemen ya jefa ta cikin halin matsalar yunwa kamar yadda MDD ta bayyana.

Shirin Samar da Abinci na Majalisar Dinkin Duniya ya ce kimanin mutum miliyan 17 ne ke fama da matsalar yunwa a kasar da ke yankin Gabas ta Tsakiya.

Rahotonni na cewa kimanin mutum miliyan 4.8 ne suka rasa muhallansu sakamakon yake-yaken da kasar ke fuskanta.

Bangladesh – Mutum miliyan 15

Kasar Bangladesh da ke yakin kudancin Asiya na daga cikin wannan jeri na inda aka fi fama da yunwa a duniya.

A cewar rahoton kungiyar GNAFC na 2026, kusan mutum miliyan 15 ne ke fama da matsalar yunwa a wannan shekara da muke ciki.

Shirin WFP na tallafa wa ‘yan gudun hijirar Rohingya kusan miliyan 1.2 a kasar, wadanda suka tsallako daga Myanmar.

Rahoton ya nuna cew a kashi 33 cikin 100 na al’ummar Bangladesh na fuskantar barazanar yunwa.

Myanmar – Mutum miliyan 12

Kasar Myanmar mai makwabtaka da Bangladesh na cikin jerin kasashen duniya da ke fama da matsalar yunwa a wannan shekara ta 2026, a cewar sabon rahoton na kungiyar GNAFC.

Fiye da al’ummar kasar miliyan 12 ke fama da yunwa kamar yadda rahoton Shirin Samar da Abinci na Majalisar Dinkin Duniya ya nuna.

A kasar Myanmar – wadda ta jima tana fama da yake-yake – iyaye mata ba sa iya samun abincin da za su kula da lafiyarsu, lamarin da ke jefa dubban kananan yara cikin matsalar tamowa.

Siriya – Mutum miliyan 9.1

Shekaru kusan 13 da aka shafe ana tafka yakin basasa a Siriya, sun jefa wasu al’ummar kasar da dama cikin halin yunwa.

Rahoton Shirin Samar da Abinci na Majalisar Dinkin Duniya ya nuna cewa mutum miliyan 9.1 ne ke fama da matsalar yunwa a kasar.

Bayanai na cewa al’ummar Siriya na shan wahalar gaske wajen samun damar ciyar da iyalansu.

A cewar rahoton, Siriya ce kasa ta biyu mafi yawan ‘yangudun hijiya a fadin duniya.

Pakistan – Mutum miliyan 7.5

Cikin wani rahoto da Majalisar Dinikin duniya ta fitar cikin watan Fabrairun da ya gabata ya nuna cewa kusan mutum miliyan 7.5 na fama da yunwa a kasar Pakistan.

Pakistan ta tsinci kanta cikin wannan hali ne sakamakon mummunar ambaliya ruwa da ta auku a kasar a shekarar da ta gabata, lamarin da ya haifar da mummunar asara ga fannin noman kasar.

Baya ga ambaliya, Pakistan ta kuma fuskanci mummunan fari, wanda shi ma ya gurgunta harkokin noman kasar.

Sudan ta Kudu – Mutum miliyan 7.5

Kusan mutum miliyan 7.56 ne ke fama da yunwa, kusan rabin al’ummar kasar kenan.

Rahoton ya nuna cewa fiye da kananan yaran kasar miliyan biyu ne ake fargabar za su fuskanci matsalar tamowa a shekara mai zuwa.

A cewar IPC kusan mutum 28,000 ne za su fada halin matsanciyar yunwa a wasu yankunan da ke fama da rikice-rikice.

Abubuwan da ke haifar da karuwar yunwa a duniya

Rahoton ya ambato wasu abubuwa da ya ce su ke haifar da matsalar yunwa a fadin duniya da suka hada da: Rikice-rikice da yake-yake. Rashin tsaro. Karuwar ‘yangudun hijira. Hauhawar farashi. Dumamar yanayi. Ambali ruwa da fari. Tsadar kayayyakin noma

Hanyoyin magance matsalar

Rahoton ya ce domin magance wannan matsala ta yunwa da ke yi wa duniya barazana akwai bukatar hadin kai da aiki tare tsakanin manyan kasashen duniya da wadanda ke fama da matsalar.

”Akwai bukatar inganta samar da abinci a duniya da daukar matakan bai daya da rage matsalolin jikai da kuma jajircewa wajen magance abubuwan da ke haifar da karuwar matsalar”, kamar yadda rahoton ya yi karin haske.

Haka kuma rohoton ya ce akwai bukatar gwamnatoci a matakai daban-daban da masu bayar da tallafin kudi da sauran cibiyoyi su kara kaimi wajen inganta fannin noma a duniya.

”Yana da kyau a magance matsalolin dumamar yanayi da inganta rayuwar mazauna yankunan karkara da samar da ayyukan yi da karfafa hanyoyin gargadin mutane domin ba su damar daukar matakan kariy a duk lokacin da aka fitar da sabon hasashe”, in ji rahoton na GNAFC.

Daga karshe kuma rahorton na GNAFC ya ce akwai bukatar bai wa kungiyoyin bayar da agaji kariya, ta hanyar karfafa dokokin duniya kan masu bayar da agaji da kuma jaddada kudurorin gwamnatoci domin magance abubuwan da ke haifar da yunwa.

Yunwa
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Tsaka mai wuyar Infantino da Koma bayan mulkin yamma
  • Sulaiman
    Abin Da Ake Kira “Hukuncin Tekun Kudancin Sin” Da Aka Yanke Wa Sin Na Kashin Kanta Ba Shi Da Wani Amfani
  • Sulaiman
    Tafiye-tafiyen Fasinjojin Jirgin Kasa A Kasar Sin Sun Haura Biliyan 2.3 A Rabin Farko Na Bana
  • Sulaiman
    Me Ya Sa Ake Ganin Afrika Na Da Damar Taka Rawa A Tsarin Tattalin Arzikin Duniya?
Yunwa
Rabi'u Ali Indabawa
+ posts Bio
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Wasu Fusatattun Mutane Sun Lakaɗa Wa Mutum Biyu Duka Har Lahira A Kaduna
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Mun Ɗauki Nauyin Karatun Masu Digiri Ta Hanyar Sayar Da Ƙosai Da Ƙuli-ƙuli —Wasu Ƴan Kasuwa
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Adadin Mutanen Da Tsananin Zafi Ya Kashe A Turai Ya Haura Dubu 1,300 —WHO
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Pakistan Ta Kashe Mutum 36 A Hare-haren Da Ta Kai Kan Iyakarta Da Afghanistan

MASU ALAKA

Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya
Rahotonni

Mun Ɗauki Nauyin Karatun Masu Digiri Ta Hanyar Sayar Da Ƙosai Da Ƙuli-ƙuli —Wasu Ƴan Kasuwa

July 11, 2026
Matsalar Tsaro: Masana Sun Firgita Da Fitowar Sabon Bidiyon Bello Turji
Rahotonni

Matsalar Tsaro: Masana Sun Firgita Da Fitowar Sabon Bidiyon Bello Turji

June 26, 2026
An Kashe Mutane Da Dama Da Kone Gidajensu A Wani Hari Da Aka Kai Benuwai
Rahotonni

Yadda Rikice-rikice Ke Ƙara Ta’azzara Talauci A Arewacin Nijeriya —Rahoto

June 26, 2026
Next Post
Binciken CGTN: Ana Goyon Bayan Mayar Da Kayan Tarihi Da Aka Wawashe Zuwa Kasashensu Na Ainihi

Binciken CGTN: Ana Goyon Bayan Mayar Da Kayan Tarihi Da Aka Wawashe Zuwa Kasashensu Na Ainihi

LABARAI MASU NASABA

Tsaka mai wuyar Infantino da Koma bayan mulkin yamma

Tsaka mai wuyar Infantino da Koma bayan mulkin yamma

July 14, 2026
“Buhari Ya Taɓa tambaya Ta Mutane Nawa Na Kashe Saboda Yawan Azumin Dana Ke Yi”

“Buhari Ya Taɓa tambaya Ta Mutane Nawa Na Kashe Saboda Yawan Azumin Dana Ke Yi”

July 14, 2026
Gwamnatin Tarayya Ta Ce Za A Gurfanar Da Tubabbun ’Yan ta’addan Da Suka Sake Aikata Manyan Laifuka

Gwamnatin Tarayya Ta Ce Za A Gurfanar Da Tubabbun ’Yan ta’addan Da Suka Sake Aikata Manyan Laifuka

July 14, 2026
Tinubu Ya Gana da Gwamnan Kwara Bayan Harin Ta’addanci Da Ya Yi Ajalin Sama Da Mutane 160

Kyawawan Manufofin Buhari Za Su Ci Gaba Da Yi Wa ’Yan Nijeriya Tasiri – Tinubu

July 14, 2026
Abin Da Ake Kira “Hukuncin Tekun Kudancin Sin” Da Aka Yanke Wa Sin Na Kashin Kanta Ba Shi Da Wani Amfani

Abin Da Ake Kira “Hukuncin Tekun Kudancin Sin” Da Aka Yanke Wa Sin Na Kashin Kanta Ba Shi Da Wani Amfani

July 13, 2026
Tafiye-tafiyen Fasinjojin Jirgin Kasa A Kasar Sin Sun Haura Biliyan 2.3 A Rabin Farko Na Bana

Tafiye-tafiyen Fasinjojin Jirgin Kasa A Kasar Sin Sun Haura Biliyan 2.3 A Rabin Farko Na Bana

July 13, 2026
Gwamnatin Tarayya Za Ta Ƙaddamar Da Tsarin Daƙile Rugujewar Gine-Gine

Gwamnatin Tarayya Za Ta Ƙaddamar Da Tsarin Daƙile Rugujewar Gine-Gine

July 13, 2026
Me Ya Sa Ake Ganin Afrika Na Da Damar Taka Rawa A Tsarin Tattalin Arzikin Duniya?

Me Ya Sa Ake Ganin Afrika Na Da Damar Taka Rawa A Tsarin Tattalin Arzikin Duniya?

July 13, 2026
Jiragen Kasan Sin Sun Yi Tafiye-Tafiyen Fasinjoji Sama Da Biliyan 2.3 A Rabin Farko Na Bana

Jiragen Kasan Sin Sun Yi Tafiye-Tafiyen Fasinjoji Sama Da Biliyan 2.3 A Rabin Farko Na Bana

July 13, 2026
Kotu Ta Hana INEC Amincewa Da Tarukan ADC Ƙarƙashin Jagorancin David Mark

Kotu Ta Hana INEC Amincewa Da Tarukan ADC Ƙarƙashin Jagorancin David Mark

July 13, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.