ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kwamitin Majalisar Wakilai Kan Noma Zai Binciki Rashin Sakin Naira Biliyan 174.26

by Naziru Adam Ibrahim
7 months ago
Noma

LABARAI MASU NASABA

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue

Kwamitin Majalisar Wakilai kan Harkokin Noma da Ayyuka ya fara shirye-shiryen gudanar da bincike kan zargin rashin sakin Naira biliyan 174.26 na kuɗaɗen tallafin noma. Binciken ya biyo bayan ƙudurin da Majalisar ta amince da shi a watan Janairu domin tantance yadda ake aiwatar da shirye-shiryen noma da abokan hulɗar raya ƙasa ke tallafawa.

Shugaban Kwamitin, Hon. Bello Ka’oje, ya buƙaci Ma’aikatun Gwamnati da Hukumomi da Sassan Gwamnati (MDAs) da su gabatar da duk muhimman takardu tare da bayar da cikakken haɗin kai. Ya ce an ɗora wa kwamitin alhakin gano dalilan da suka haddasa jinkirin sakin kuɗaɗen, tare da duba tasirin hakan kan tsadar taki da samar da abinci a ƙasa.

  • Abin Da Ya Sa Manoman Rani Na Alkama Suka Samu Matsala A Kano
  • NiMet Ta Yi Hasashen Ruwan Sama Da Wuri, Ta Nemi Manoma Su Jinkirta Shuka

A cewarsa, Nijeriya ta samu rancen dala miliyan 134 daga African Development Bank domin aiwatar da shirin NAGS-AP, inda aka saki dala miliyan 99.67, amma har yanzu Naira biliyan 55.30 da aka ware wa manoma da dillalan kayan noma na noman rani na 2024 da 2025 ba a sake su ba.

ADVERTISEMENT

Haka kuma, an samu rancen Yen biliyan 15 daga Japan International Cooperation Agency, inda aka saki Yen biliyan 12 (kimanin Naira biliyan 118.96) a watan Maris 2025, amma ba su kai ga hukumomin da za su aiwatar da shirin ba. Kwamitin ya yi gargaɗin cewa jinkirin na iya jefa girbin 2025 da kakar noma ta 2026 cikin haɗari, tare da barazana ga ƙarin tallafin dala miliyan 200 da ake sa ran samu idan ba a aiwatar da shirye-shiryen da suka gabata yadda ya kamata ba.

Noma
Naziru Adam Ibrahim
+ postsBio
  • Naziru Adam Ibrahim
    https://hausa.leadership.ng/author/naziru-adam-ibrahim/
    Ya Kamata Farashin Siminti Ya Sauka — Umahi Ga Masana’antun Siminti
  • Naziru Adam Ibrahim
    https://hausa.leadership.ng/author/naziru-adam-ibrahim/
    Yari Ya Dace Da Rayuwar Mulki Da Kasuwanci
  • Naziru Adam Ibrahim
    https://hausa.leadership.ng/author/naziru-adam-ibrahim/
    A Ƙarshe Jamilu Gwamna Ya Samu Babbar Dama Ta Yin Takara
  • Naziru Adam Ibrahim
    https://hausa.leadership.ng/author/naziru-adam-ibrahim/
    Shugaba Tinubu Ya Isa Nairobi Domin Halartar Taron Tattalin Arzikin Nahiyar Afirka

MASU ALAKA

Ballon D'or
Manyan Labarai

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

September 8, 2026
Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue
Manyan Labarai

Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue

September 8, 2026
2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi
Manyan Labarai

2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi

September 8, 2026
Next Post
Fadar Sarkin Musulmi Ta Umarci A Fara Duban Jinjirin Watan Ramadan Ranar Talata

Fadar Sarkin Musulmi Ta Umarci A Fara Duban Jinjirin Watan Ramadan Ranar Talata

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.