ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Majalisar Ƙoli Kan Shari’ar Musulunci Ta Sake Neman A Cire Shugaban INEC

by Abubakar Sulaiman
7 months ago
Musulunci

Majalisar Ƙoli kan harkokin Shari’ar Musulunci a Nijeriya (SCSN) ta sake nanata kiranta na a cire Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta (INEC), Farfesa Joash Amupitan, tana mai cewa ba ta da amincewa da cewa zai iya gudanar da zaɓe cikin adalci a babban zaɓen ƙasar da ke tafe.

Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da sakatare-janar na majalisar, Nafi’u Baba Ahmad, ya sanyawa hannu. Majalisar ta ce kiran da take yi ba shi da alaƙa da addini ko ƙabilanci, sai dai da batun nagarta da cancantar shugabanci. Ta bayyana cewa sabon bayanin ya zama dole ne bayan fassarar da aka yi wa wata sanarwa da ta fitar a baya ranar 28 ga Janairu.

  • Gudunmawar Shehu Ibrahim Inyass (RTA) Ga Musulunci A Wayewar Zamani (2)
  • Lalacewar Tarbiyar Dalibai Mata A Makarantun Islamiyya Da Na Boko

Rahoton BBC ya bayyana cewa, Majalisar ta jaddada cewa ba a taɓa amfani da bambancin addini wajen amincewa ko ƙin amincewa da sakamakon zaɓe ba tun daga samun ’yancin kai a 1960. Ta ƙara da cewa daga shugabannin INEC 13 da suka gabata, Farfesa Attahiru Jega da Farfesa Mahmood Yakubu ne kaɗai musulmai, amma hakan bai taɓa haifar da ƙin amincewa da zaɓe daga musulman ƙasar ba.

ADVERTISEMENT

A cewar majalisar, dalilin neman cire Farfesa Amupitan ya shafi wasu abubuwan da ta ce ya aikata a baya, musamman wata takarda da ya jagoranci rubutawa a 2020, wadda a cikinta ta ce ya yi kalamai masu cin mutunci ga musulman Nijeriya, da Arewa da kuma Usman Ɗanfodio. Majalisar ta ce takardar ta yi zargin ana yi wa kiristoci “kisan kiyashi” tare da yunƙurin danganta matsalar tsaro da jihadin Ɗanfodio, abin da ta bayyana a matsayin kuskure kuma mai tayar da zaune tsaye.

Majalisar ta ƙara da cewa har zuwa yanzu Shugaban INEC bai fito ya nesanta kansa daga waɗannan kalamai ba, tana mai jaddada cewa shugabancin hukumar zaɓe na buƙatar mutum da ke kauce wa nuna bambancin addini ko ƙabilanci. A saboda haka, majalisar ta ce ba za ta amince da duk wani zaɓe da Farfesa Amupitan zai jagoranta ba.

LABARAI MASU NASABA

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue

Musulunci
Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    Iyalin El-Rufai Sun Bai Ministan Tsaro Wa’adin Kwana 7 Kan Zargin Rikicin Kudancin Kaduna
  • Abubakar Sulaiman
    Atiku Ya Zargi Gwamnatin Tarayya Da Cin Bashi Kamar Mashayin Da Kuɗi Ya Ƙarewa
  • Abubakar Sulaiman
    Boko Haram Ta Kai Hari Adamawa, Ana Fargabar Mutuwar Mutane 11
  • Abubakar Sulaiman
    Ƴan Bindiga Sun Kai Hari Sokoto, Sun Kashe Mutane 7, Sun Yi Garkuwa Da 12

MASU ALAKA

Ballon D'or
Manyan Labarai

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

September 8, 2026
Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue
Manyan Labarai

Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue

September 8, 2026
2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi
Manyan Labarai

2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi

September 8, 2026
Next Post
 ‘Yan Adawa Sun Sauya Sabuwar Dabarun Kifar Da Tinubu A 2027

 ‘Yan Adawa Sun Sauya Sabuwar Dabarun Kifar Da Tinubu A 2027

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.