Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), Farfesa Joash Amupitan, ya yi kira ga jami’an hukumar da su tabbatar da gaskiya, ƙin goyon kowa da nuna ƙwarewa a shirye-shiryen babban zaɓen 2027.
Amupitan ya bayyana haka ne yayin wani taron horas da Sakataren Gudanarwa na INEC da sauran jami’an hukumar na shiyyar Kudu maso Yamma da aka gudanar a Legas. Ya ce yadda zaɓen 2027 zai gudana ya ta’allaka ne sosai kan yadda jami’an hukumar a jihohi za su gudanar da ayyukansu.
Shugaban INEC ya buƙaci Sakataren Gudanarwa su ƙara haɗin gwiwa da Kwamishinonin Zaɓe na Jihohi (RECs), yana mai bayyana su a matsayin ginshiƙin gudanar da ayyukan hukumar a matakin jiha. Ya gargaɗi jami’an da kada su yi sassauci ga saɓa ƙa’ida, ko tsoma bakin ƴan siyasa ko sakaci wajen aiwatar da ayyukansu.
Amupitan ya ce: “Dole ne mu gujewa duk wani sanadin da zargi, domin idanun sama da ƴan Nijeriya miliyan 200, da kuma duniya baki ɗaya, suna kanmu. Aiwatar da zaɓen da bai inganta ba rauni ne ga ruhin ƙasa; mu tabbatar cewa a ƙarƙashin kulawarmu, wannan ruhin ya kasance lafiya.”
Ya kuma jaddada cewa doka ita kaɗai ba za ta iya tabbatar da sahihancin zaɓe ba, matuƙar jami’an da aka ɗora wa alhakin aiwatar da ita ba su yi hakan bisa aminci da rashin goyon bayan kowa ba. Ya buƙaci ma’aikatan INEC su san dokokin zaɓe, su fahimci nauyin da ke kansu, su rubuta bayanan ayyukansu yadda ya kamata, tare da kare amincin tsarin zaɓe.
Shugaban hukumar ya ce gudanar da zaɓe mai inganci a ƙasa mai girma kamar Nijeriya babban aiki ne, amma ya ce INEC na da damar yin hakan ta hanyar bin doka, amfani da fasaha da kuma kishin ƙasa.














