ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

NPA Ta Baje Kolinta A Taron Zuba Jari Na Kasa Da Kasa Na Inbestopia

by Bello Hamza
7 months ago
NPA

Nijeriya ta karbar bakunci babban taron na kasa da kasa na masu zuba jari a fannin sufuri, inda Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Kasa NPA, ta zayyano wasu manyan manufofi, domin kara samar da intantattun kayan aiki, ga Tashoshin Jiragen Ruwa na kasar.

Taron wanda zai guna a jihar Legas, ya samu halartar  jiga-jigan masu zuba jari a fannin sufurin Jiragen Ruwa daga ketare.

  • Rikicin Iran Da Amurka: Gabas Ta Tsakiya Ta Ɗauki Zafi
  • Dabara Ta Rage Ga Mai Shiga Rijiya

Za a gudanar da taron ne, a tsakanin Nijeriya da kuma Daular Larabawa wato UAE.

ADVERTISEMENT

Taron wanda ya gudanar a ranar 2 na watan Fabirairun 2026, ya gudana ne, a cibiyar Eko, da ke a Legas, ya samu halartar manyan jami’ian gwamnati da masu zuba jari daga ketare da jagororin manyan masana’antu, inda suka yi tattaunawa mai zurfi, kan yadda za a amafa da albakatun, da ke a yankin.

Kazalika, tattaunawar, ta shafi yadda za a samar da manyan kayan aiki da samar da makamashi da samar da tsarin kudade, wadanda sune, suka kasance, kan gaba, wajen bunkasa tattalin arzkin Afirka, na dogon zango.

LABARAI MASU NASABA

Yadda Taron Bikin Maulidi Ya Gudana A Unguwar Mile 12 A Legas

NPA Ta Bayyana Cewa Kirkiro Da Sabuwar Hukumar NPERA Ba Zai Zame Mata Tarnaki Ba

A cikin sanarwar da Janar Manja na sashen hulda da jama’a a NPA, Ikechukwu Onyemekara, NPA ta ce, halartar masu zuba jarin taron, ya nuna irin mayar da hankali da Nijeriya ta yi, wajen kara saita fannin na sufurin Jiragen Ruwan kasar, musamman domin bayar da damar, ci gaba da gudanar da hada-hadar kasuwanci da kuma kara karfafa hukdar kasuwanci, a tsakanin kasashen da ke a Afirka.

A cewar NPA, taron na Inbestopia Lagas, an gudanar da shi ne, sabada nuna ra’ayin kara bunkasa fannin, da gwamnatin  shugaba Bola Ahmed Tinubu ta yi.

Sanawar ta kara da cewa, taron ya biyo bayan wata ziyara da Nijeriya ta kai UAE ne, a watan Janairun  2026, bayan taron kasa da kasa na mako, da aka gudanar a Abu Dhabi.

Kazalaika, a lokacin ziyarar a Abu Dhabi, Nijeriya da UAE, sun rattaba hannun yarjejeniya ta hadakar  bunkasa tattalin arzikin kasashen biyu, wato  CEPA.

Babban abin da ake son cimma buri, shi ne, kara karfafa hadaka wajen kaara samar da makamashi da kayan aiki da kuma bunkasa hada-hadar kasuwanci, ta hanyar yin amfani da fasahar zamani.

Bugu da kari, shugaba Tinubu, ya sanar da dalilin da ya sa, Nijeriya, za ta karbi bakuncin taron na Inbestopia da za a gudanar a Legas, musamman bisa nufin janyo hanlakin masu zuba jari daga ketare.

Hakazalika, Shugaban Hukumar ta NPA Dakta Abubakar Dantsoho da kuma Mohamed Almenhali, Babban Jami’I a Tashoshin Jiragen Ruwa na Abu Dhabi, sun kasance Alkalai  wajen taron, inda suma suka gabatar da kasida mai taken, “ Samar Da Ingantattun Kayan Aiki a Tashoshin Jiragen Ruwa domin kara bunkasa hada-hadar kasuwanci, a mataki na gaba.

Alkalancin taron, ya kuma mayar da hankali wajen yadda za a kara karfafa samar da kayan aiki a Tashoshin Jiragen Ruwa da zamanantar da hada-hadar kasuwanci ta hanyar yin amfani da fasahar zamani.

Kasashen biyu, za su kuma amfana da juna a bangaren zuba jari, tare da saita kasuwancin a Afirka ta Yamma, wanda hakan, zai kara habaka hada-hadar kasuwanci.

Masu jawabi da ban da ban, sun gabatar da kasidu, wadanda suka hada da, Babban Shugaba na  Inbestopia, Dakta  Jean Fares da ministar ma’aikatar bunkasa kasuwanci da zuba jari, Dakta Jumoke Oduwole da ministan ma’aiktar zuba jari na UAE Mohamed H. Alsuwaidi.

Sauran sun hada da; kasidun Babban Jami’I kuma Manajin Darkta na FIRST da Ademola Adeyemi-Bero shugaba kuma Babban jami’I na  AFC, Samaila Zubairu da sauransu.

Kazalika, Hukumar ta NPA, ta himmatu wajen kara fadada sauye-sauyen ci gaban fannin da kara bunkasa ayyukanta, musamman domin a cimma nasara, kan manufofin kara ciyar da ayyukan hukumar gaba.

A cewar hukumar hadakar da ta yi da UAE wanda hakan ya kuma haifar da taron na Inbestopia, kwalliya ta biya kudin Sabulu, musamman duba da cewa, hakan ya kara samar da damar zuba jari, wanda hakan zai kuma samar da sakamako mai kyau na tattaunawar da shugaba President Tinubu, ya yi a kwanan baya da UAE.

NPA
Bello Hamza
+ postsBio
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    Jihar Kano Za Ta Amfana Matuka Da Gidauniyar Aliko Dangote – Masu Ruwa Da Tsaki
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    An Nuna Damuwa Kan Sake Kamun Da DSS Ta Yi Wa Boɗejo Bayan Samun Belin EFCC
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    Dole Al’ummar Arewa Su Rungumi Hanyoyin Kasuwanci Na Zamani —Alfa Musa
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    Ba Mu Taba Biyan Kudin Fansa Ba Kuma Ba Za Mu Biya Ba – Kwamishinan Katsina

MASU ALAKA

Yadda Taron Bikin Maulidi Ya Gudana A Unguwar Mile 12 A Legas
Tattalin Arziki

Yadda Taron Bikin Maulidi Ya Gudana A Unguwar Mile 12 A Legas

September 4, 2026
NPA Ta Bayyana Cewa Kirkiro Da Sabuwar Hukumar NPERA Ba Zai Zame Mata Tarnaki Ba
Tattalin Arziki

NPA Ta Bayyana Cewa Kirkiro Da Sabuwar Hukumar NPERA Ba Zai Zame Mata Tarnaki Ba

September 4, 2026
NPA Ta Tabbatar Da Maido Da Manyan Kayan Aikin Hukumar Wuta Ta Neja Delta —Babbar Manaja
Tattalin Arziki

NPA Ta Tabbatar Da Maido Da Manyan Kayan Aikin Hukumar Wuta Ta Neja Delta —Babbar Manaja

August 28, 2026
Next Post
Ronaldo Ba Shi Da Ikon Yanke Hukunci A Gasar Saudi Pro League – Mahukunta

Ronaldo Ba Shi Da Ikon Yanke Hukunci A Gasar Saudi Pro League - Mahukunta

LABARAI MASU NASABA

Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.