Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi ƙarin haske kan dalilin da ya sa ya yanke shawarar yin takara a inuwa ɗaya da tsohon Gwamnan Anambra, Peter Obi, a matsayin mataimakinsa, gabanin babban zaɓen shekarar 2027 mai zuwa.
Kwankwaso, wanda ke neman tikitin mataimakin shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar NDC, ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa inda ya ce sun ƙulla wannan ƙawance ne domin fito da sabon tsarin shugabanci.
Ya koka kan yadda Nijeriya ta tsunduma a cikin wani mummunan yanayi, inda ya bayar da misali da tsadar kayan abinci, rashin aikin yi ga matasa, gami da taɓarɓarewar tsaro da suka zama ƙarfen-ƙafa ga ƴan ƙasa. Kwankwaso ya jaddada cewa lalacewar tsaro na ci gaba da yin barazana ga al’umma, inda ta’addanci, da ƴan fashin daji, da kuma garkuwa da mutane ke yi wa rayuwar al’umma da tattalin arziƙinsu zagon-ƙasa.
Ya ce lallai “ya kamata manoma su samu isasshen tsaron da zai ba su damar komawa gonakinsu, sannan yara su samu makarantu masu tsaro, kuma kowane ɗan Nijeriya yana da haƙƙin rayuwa ba tare da fargaba ba.”
Baya ga maganar tattalin arziƙi da tsaro, tsohon gwamnan ya bayyana cewa ilimi, da kiwon lafiya, da ayyukan more rayuwa, da kuma yin garambawul ga hukumomin gwamnati na daga cikin abubuwan da gwamnati ya kamata ta ba wa muhimmanci a yanzu. Da ya ke bayani kan dalilinsa na zaɓar haɗa kai da Obi, Kwankwaso ya ce wannan ƙawance ba a yi shi ne bisa tsarin ƙabilanci, ko addini, ko biyan buƙatun kai ba, illa domin ciyar da ƙasar nan gaba sannan kuma su samar da ingantaccen shugabanci mai gaskiya da riƙon amana.
Daga ƙarshe, Kwankwaso ya yi kira ga dukkan ƴan Nijeriya, musamman matasa, mata, da ma’aikata, da manoma, da ƙwararru a fannoni daban-daban da su fito ƙwansu da kwarkwatar su, don su taka rawa yadda ya kamata a wannan gagarumin yunƙuri na tabbatar da canji nagari.














