ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, September 18, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Rikicin Shugabanci Ya Kunno Kai A ADC Jihar Zamfara

by Abubakar Sulaiman
5 months ago

Rikicin shugabanci ya ɓarke a jam’iyyar ADC reshen jihar Zamfara, inda ɓangarori biyu ke iƙirarin mallakar shugabancin jam’iyyar. Lamarin ya samo asali ne yayin da aka gudanar da taron mazabu da kuma ayyana sabon kwamiti na shugabanci.

Wani ɓangare da Malam Mohammed Mainasara ke jagoranta ya bayyana cewa shugabancin jam’iyyar na ƙasa ne ya umarce su da su kula da gudanar da taron mazaɓar jam’iyyar a Zamfara. Ya ce an naɗa shi shugaban kwamitin taron, tare da Ambasada Zubairu Yalwa a matsayin sakatare da sauran mambobi, inda ya ce sun je jihar domin tabbatar da gudanar da aikin cikin lumana.

Mainasara ya kuma bayyana cewa an cimma matsayar kafa sabon kwamitin zartarwa na jiha (EXCO) ta hanyar sulhu da amincewar masu ruwa da tsaki. A cewarsa, an zabi Malam Shehu Gulubba a matsayin shugaban jam’iyya na jihar, yayin da Dr. Ahmad Hashim ya zama sakatare, tare da Jafar Aliyu a matsayin shugaban matasa da Maryam Abdullahi a matsayin shugabar mata.

ADVERTISEMENT

A nasa ɓangaren, sabon shugaban da aka ce an zaɓa, Malam Shehu Maishanu, ya yi alƙawarin yin aiki tukuru wajen ƙarfafa jam’iyyar da tabbatar da nasararta a faɗin jihar Zamfara. Ya ce jagorancinsu zai mayar da hankali kan ci gaban al’umma da kuma tabbatar da haɗin kai a cikin jam’iyyar.

Sai dai wani ɓangare ƙarƙashin jagorancin Kabiru Garba Gusau ya yi watsi da sakamakon taron, yana mai cewa shi ne halastaccen shugaban jam’iyyar a jihar. Ya zargi wasu da haɗa kai domin tayar da zaune tsaye, tare da gargaɗin cewa ba za su amince da abin da ya faru ba, inda ya ce sun riga sun kai rahoto ga ‘yansanda da DSS. Ya kuma bayyana cewa ya dakatar da duk waɗanda suka halarci taron, yana mai cewa yana da ikon kundin tsarin jam’iyya na yin hakan.

LABARAI MASU NASABA

Ban Taɓa Yi Wa Tinubu Alƙawarin Zan Koma APC Ba – Wike

An Gudanar Da Sallar Zana’idar Tsohon Gwamnan Gongola

Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    ICPC Ta Yi Wa Dan Takarar APC A Ekiti Titsiye Kan Zargin Badakalar Kuɗi
  • Abubakar Sulaiman
    Gyaran Kundin Tsarin Mulki: Abubuwa 12 Da Ya Kamata A Sani Kan Abin Da Aka Aika Wa Majalisun Jihohi
  • Abubakar Sulaiman
    Saudiyya Ta Yi Biris Da Bukatar Nijeriya Ta Ƙarin Kujerun Hajjin 2027
  • Abubakar Sulaiman
    Dalilanmu Na Neman NDLEA Ta Binciki Bello El-Rufai Kan Zargin Amfani Da Hodar Iblis

MASU ALAKA

2023: Me Ya Sa Ake Rububin Wike?
Siyasa

Ban Taɓa Yi Wa Tinubu Alƙawarin Zan Koma APC Ba – Wike

September 16, 2026
Siyasa

An Gudanar Da Sallar Zana’idar Tsohon Gwamnan Gongola

September 13, 2026
jam'iyyu
Siyasa

An Buƙaci Ƴan Takara Su Sanya Tsare-tsaren Yaƙi Da Ɗumamar Yanayi A Jaddawalin Kamfen Ɗinsu

September 12, 2026
Next Post
Kuri’un Jin Ra’ayin Jama’a Na CGTN Sun Shaida Kamfanonin Kasa Da Kasa Sun Fi Son Zuwa Kasar Sin Don Aiwatar Da Harkokinsu

Kuri’un Jin Ra’ayin Jama’a Na CGTN Sun Shaida Kamfanonin Kasa Da Kasa Sun Fi Son Zuwa Kasar Sin Don Aiwatar Da Harkokinsu

LABARAI MASU NASABA

Matatar Dangote Za Ta Ƙara Yawan Ma’aikata Da Samar Da Mai

Matatar Dangote Za Ta Ƙara Yawan Ma’aikata Da Samar Da Mai

September 18, 2026
Tinubu Ya Nemi Jihohi Su Dakatar Da Karbar Haraji A Kan Masu Safarar Kayan Abinci

Tinubu Ya Ba Da Umarnin Binciken Mutuwar Masu Haƙar Ma’adinai A Neja

September 18, 2026
Gwamnatin Neja Ta Sanya Dokar Hana Fita Bayan Zanga-Zanga Ta Ɓarke A Minna

Gwamnatin Neja Ta Sanya Dokar Hana Fita Bayan Zanga-Zanga Ta Ɓarke A Minna

September 18, 2026
ICPC Ta Yi Wa Dan Takarar APC A Ekiti Titsiye Kan Zargin Badakalar Kuɗi

ICPC Ta Yi Wa Dan Takarar APC A Ekiti Titsiye Kan Zargin Badakalar Kuɗi

September 18, 2026
Gyaran Kundin Tsarin Mulki: Abubuwa 12 Da Ya Kamata A Sani Kan Abin Da Aka Aika Wa Majalisun Jihohi

Gyaran Kundin Tsarin Mulki: Abubuwa 12 Da Ya Kamata A Sani Kan Abin Da Aka Aika Wa Majalisun Jihohi

September 18, 2026
Saudiyya Ta Yi Biris Da Bukatar Nijeriya Ta Ƙarin Kujerun Hajjin 2027

Saudiyya Ta Yi Biris Da Bukatar Nijeriya Ta Ƙarin Kujerun Hajjin 2027

September 18, 2026
Dalilanmu Na Neman NDLEA Ta Binciki Bello El-Rufai Kan Zargin Amfani Da Hodar Iblis

Dalilanmu Na Neman NDLEA Ta Binciki Bello El-Rufai Kan Zargin Amfani Da Hodar Iblis

September 18, 2026
Shettima Ya Yi Karin Haske Kan Maganar Gwamnonin Arewa 6

Shettima Ya Yi Karin Haske Kan Maganar Gwamnonin Arewa 6

September 18, 2026
Cinikin Shige Da Fice Mai Dorewa Ba Tare Da Gurbatta Muhalli Ba Na Kasar Sin Yana Sahun Gaba A Duniya

Cinikin Shige Da Fice Mai Dorewa Ba Tare Da Gurbatta Muhalli Ba Na Kasar Sin Yana Sahun Gaba A Duniya

September 17, 2026
U-20: Nijeriya Ta Doke Ingila Da Ci 3-0, Ta Kai Zagayen Kwata-fainal

U-20: Nijeriya Ta Doke Ingila Da Ci 3-0, Ta Kai Zagayen Kwata-fainal

September 17, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.