ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sojoji Sun Ceto Mata Da Yara 6 Daga Hannun ‘Yan Boko Haram A Jihar Borno

by Muhammad
4 months ago

Sojojin rundunar haɗin gwiwa ta Arewa maso Gabas, Operation HADIN KAI (OPHK), sun sake samun wata babbar nasara bayan ceto fararen hula shida da aka sace, tare da haɗa su da iyalansu a ƙauyen Ngoshe, ƙaramar hukumar Gwoza a Jihar Borno.

A wata sanarwa da jami’in yaɗa labarai na OPHK, Lt. Col. Sani Uba, ya fitar ga manema labarai a Maiduguri ranar Asabar, ya ce wannan nasara ta biyo bayan ci gaba da kai hare-haren soji, ciki har da farmakin jiragen sama da aka kai kan maɓoyar ‘yan ta’adda a tsaunukan Mandara.

Ya bayyana cewa bisa sahihan bayanan sirri, sojojin OPHK yayin dawowa daga wani samame da suka kai cikin dare a safiyar Juma’a, 1 ga Mayu, 2026, sun tare tare da ceto mata da yara shida a yankin Amuda—wani wuri da babu kowa tsakanin Ngoshe da Gava a ƙaramar hukumar Gwoza, wanda aka san da zama hanyar zirga-zirgar ‘yan ta’adda.

ADVERTISEMENT

An bayyana sunayen waɗanda aka ceto da suka hada da Zainab Idris (Mai shekaru 18), Fatima Abubakar (Mai shekaru 17), Maimuna Abdulrashid (Mai shekaru 24), Muhammad Idris (Mai shekara 1), Sadiq Abdullahi (Mai shekara 7), da Fatima Abdulrashid (Mai shekara 5).

Binciken farko ya nuna cewa su na daga cikin mutanen da aka sace a harin da ‘yan ta’adda suka kai Ngoshe a ranar 3 ga Maris, 2026, inda aka tsare su a wani sansanin ‘yan ta’adda a Gava kafin su samu damar tserewa.

LABARAI MASU NASABA

NDLEA Ta Cafke Ƴar Shekara 67 Da Hodar Iblis Da Aka Ɓoye A Cikin Ayaba

Gwamnatin Kaduna Ta Yaba Wa ONSA Kan Shirin Horon Masu Tsaron Daji ‘Forest Guards’

A lokacin aikin ceton, sojojin sun fuskanci harbin daga ‘yan ta’adda da ke ƙoƙarin bin waɗanda suka tsere. Sai dai sojojin sun mayar da martani cikin gaggawa, inda suka fafata na ɗan lokaci, lamarin da ya tilasta wa ‘yan ta’addan ja da baya zuwa cikin tsaunuka.

Sanarwar ta ƙara da cewa wannan nasara na da alaƙa da matsin lamba da ake ci gaba da yi wa ‘yan ta’adda, wanda ya raunana haɗin kansu tare da jefa su cikin ruɗani. Rahotannin sirri sun nuna cewa ‘yan ta’addan na cikin matsananciyar damuwa da firgici sakamakon asarar da suke yi da kuma tserewar waɗanda suka sace, ciki har da wata yarinya mai shekara 16 da aka tilasta mata aure da wani kwamandansu.

Bayan ceton, an ba waɗanda aka ceto agajin gaggawa tare da duba lafiyarsu a wani asibitin soji, kafin a miƙa su ga shugabannin al’umma.

Da misalin ƙarfe 2:00 na rana a ranar, an haɗa su da iyalansu ta hannun Wali na Ngoshe, Alhaji Shuaibu Dabawa, a wani yanayi mai cike da motsin zuciya wanda al’umma suka halarta.

Rundunar Sojojin Nijeriya ta tabbatar da ƙudirin ta na ci gaba da kare al’umma, ceto waɗanda aka sace, da kuma kawar da ‘yan ta’adda a dukkan yankunan Arewa maso Gabas.

Ta kuma ce ƙwarin gwiwar sojoji da ƙwarewarsu na nan daram, yayin da ake ci gaba da gudanar da ayyukan da ƙarfi. An kuma buƙaci al’umma da su ci gaba da bayar da sahihan bayanai domin taimaka wa ayyukan tsaro, don tabbatar da zaman lafiya da ci gaban yankin.

Babban hafsan rundunar soji ya yaba wa sojojin bisa jajircewarsu, tare da ƙarfafa musu gwiwa su ci gaba da kai hare-hare domin mamaye fagen daga.

Muhammad
+ postsBio
  • Muhammad
    Yadda Na Tsira Daga Cutar Mashaƙo A Katsina: “Na Fara Da Tsartuwar Jini Tare Da Yawu”
  • Muhammad
    An Naɗa Yusuf Nasidi Nasir A Matsayin Talban Barayan Kano
  • Muhammad
    Wani Kamfani Ya Tallafa Wa Masu Sana’ar Shayi A Kano
  • Muhammad
    Kosan Waka Ya Rasu, Gwamnan Kano Ya Jajanta Wa Iyalansa

MASU ALAKA

Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya
Tsaro

NDLEA Ta Cafke Ƴar Shekara 67 Da Hodar Iblis Da Aka Ɓoye A Cikin Ayaba

July 11, 2026
Gwamnatin Kaduna Ta Yaba Wa ONSA Kan Shirin Horon Masu Tsaron Daji ‘Forest Guards’
Tsaro

Gwamnatin Kaduna Ta Yaba Wa ONSA Kan Shirin Horon Masu Tsaron Daji ‘Forest Guards’

July 9, 2026
Sojoji Sun Kama Mai Kai Wa Ƴan Ta’adda Kayan Aiki A Zamfara
Tsaro

Sojoji Sun Kama Mai Kai Wa Ƴan Ta’adda Kayan Aiki A Zamfara

June 25, 2026
Next Post
Tawagar Likitocin Sin A Nijar Ta Bayar Da Horo Na Farko Kan Agajin Gaggawa Da Ya Kai Ingancin Na Kasa Da Kasa

Tawagar Likitocin Sin A Nijar Ta Bayar Da Horo Na Farko Kan Agajin Gaggawa Da Ya Kai Ingancin Na Kasa Da Kasa

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.