ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, July 15, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ƴan Bindiga Sun Kashe Wani Fasto, Sun Sace Masu Ibada A Jihar Ekiti

by Abubakar Sulaiman
3 months ago
Fasto

Mazauna garin Eda Oniyo da ke Jihar Ekiti, shalkwatar ƙaramar hukumar Ilejemeje, sun shiga cikin fargaba bayan wasu ‘yan bindiga sun kai hari kan al’ummar yankin, inda suka kashe mutum guda tare da sace wasu da dama.

Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne a yammacin ranar Talata, lokacin da ake gudanar da wani taron wa’azi a fili wanda wata coci ta shirya a yankin da misalin ƙarfe 7 na yamma.

An ce ‘yan bindigar sun riƙa harbe-harbe ba kakkautawa, inda suka kashe faston wanda shi ne baƙon da aka gayyata, sannan suka sace wasu daga cikin masu ibadar a yayin harin.

ADVERTISEMENT

Wata majiya daga yankin ta bayyana cewa maharan, waɗanda ke ɗauke da muggan makamai, sun aikata abin da suka ga dama kafin su tsere da mutanen da suka sace zuwa cikin wani daji da ke kusa.

Wani jagoran al’umma, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya shaida wa manema labarai a Ado-Ekiti cewa daga cikin waɗanda aka sace akwai tsofaffi da yara.

LABARAI MASU NASABA

NDLEA Ta Cafke Ƴar Shekara 67 Da Hodar Iblis Da Aka Ɓoye A Cikin Ayaba

Gwamnatin Kaduna Ta Yaba Wa ONSA Kan Shirin Horon Masu Tsaron Daji ‘Forest Guards’

A cewarsa, “Da yammacin yau, kafin ƙarfe bakwai kaɗan, ‘yan bindiga sun kai hari kan wani taron coci a Eda Oniyo. Sun harbe fasto tare da bude wuta kan masu ibada, suka kuma sace da dama ciki har da tsofaffi da yara, suka tafi da su cikin daji. Yawan maharan ya girgiza al’umma, kuma iyalai na ci gaba da neman ‘yan uwansu da suka ɓace.”

Shugaban ƙaramar hukumar Ilejemeje, Hon. Pius Alaba, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce rahotanni daga faston da ke kula da cocin sun nuna cewa sama da masu ibada 50 ne suka halarci taron, inda da dama daga cikinsu suka samu tserewa zuwa cikin daji.

Ya ƙara da cewa gawar faston baƙon, wanda aka ce daga wata jiha makwabta ya zo, an kai ta ɗakin ajiye gawa.

Fasto
Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    Gwamnatin Tarayya Za Ta Ƙaddamar Da Tsarin Daƙile Rugujewar Gine-Gine
  • Abubakar Sulaiman
    Kotu Ta Hana INEC Amincewa Da Tarukan ADC Ƙarƙashin Jagorancin David Mark
  • Abubakar Sulaiman
    Mahara Sun Kashe Mutane 9 Ƴan Gida Ɗaya, Har Da Jariri Ɗan Wata 2 A Filato
  • Abubakar Sulaiman
    FIFA Na Nazarin Faɗaɗa Gasar Kofin Duniya Zuwa Ƙasashe 64

MASU ALAKA

Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya
Tsaro

NDLEA Ta Cafke Ƴar Shekara 67 Da Hodar Iblis Da Aka Ɓoye A Cikin Ayaba

July 11, 2026
Gwamnatin Kaduna Ta Yaba Wa ONSA Kan Shirin Horon Masu Tsaron Daji ‘Forest Guards’
Tsaro

Gwamnatin Kaduna Ta Yaba Wa ONSA Kan Shirin Horon Masu Tsaron Daji ‘Forest Guards’

July 9, 2026
Sojoji Sun Kama Mai Kai Wa Ƴan Ta’adda Kayan Aiki A Zamfara
Tsaro

Sojoji Sun Kama Mai Kai Wa Ƴan Ta’adda Kayan Aiki A Zamfara

June 25, 2026
Next Post
Masu Ruwa Da Tsaki Sun Buƙaci Ƙara Zuba Jari A Binciken Noma

Masu Ruwa Da Tsaki Sun Buƙaci Ƙara Zuba Jari A Binciken Noma

LABARAI MASU NASABA

Sakamakon Binciken Masana Na Kasar Da Ake Fitarwa Kyauta Yana Kara Jan Hankalin Duniya

Sakamakon Binciken Masana Na Kasar Da Ake Fitarwa Kyauta Yana Kara Jan Hankalin Duniya

July 14, 2026
Cinikin Waje Ta Kasar Sin Na Bunkasa Cikin Sauri Da Kwanciyar Hankali A Rabin Farko Na Shekara Ta 2026

Cinikin Waje Ta Kasar Sin Na Bunkasa Cikin Sauri Da Kwanciyar Hankali A Rabin Farko Na Shekara Ta 2026

July 14, 2026
An Yi Tir Da Kalaman Wasu Sassan Ketare Game Da Yayata Batun Cika Shekaru Goma Da Fitar Da Abin Da Aka Kira “Hukuncin Tekun Kudancin Sin”

An Yi Tir Da Kalaman Wasu Sassan Ketare Game Da Yayata Batun Cika Shekaru Goma Da Fitar Da Abin Da Aka Kira “Hukuncin Tekun Kudancin Sin”

July 14, 2026
Nijeriya Za Ta Zama Ƙasa Mai Zaman Lafiya, Ba Za A Ƙara Samun Kashe-kashen Jama’a Ba – Oluremi Tinubu

Nijeriya Za Ta Zama Ƙasa Mai Zaman Lafiya, Ba Za A Ƙara Samun Kashe-kashen Jama’a Ba – Oluremi Tinubu

July 14, 2026
Sin Ta Tsara Bunkasa Darajar Cinikayyar Kayayyaki Zuwa Yuan Tiriliyan 60 Yayin Shirin Raya Kasa Na Shekarar 2026 Zuwa 2030

Sin Ta Tsara Bunkasa Darajar Cinikayyar Kayayyaki Zuwa Yuan Tiriliyan 60 Yayin Shirin Raya Kasa Na Shekarar 2026 Zuwa 2030

July 14, 2026
Katsina: Kotu Ta Yanke Wa Hauwa’u Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya Kan Taimaka Wa ’Yan Bindiga

Kotu Ta Tsare Shugaban Makaranta Da Malami Kan Zargin Lalata Da Ɗaliba Mai Shekara 6 A Gombe

July 14, 2026
An Bankado Muguwar Aniyar Japan Ta Haifar Da Tashin Hankali A Tekun Kudancin Sin

An Bankado Muguwar Aniyar Japan Ta Haifar Da Tashin Hankali A Tekun Kudancin Sin

July 14, 2026
Layin Dogo Tsakanin Tanzaniya Da Zambiya Ya Zama Shaidar Abota Tsakanin Sin Da Afirka

Layin Dogo Tsakanin Tanzaniya Da Zambiya Ya Zama Shaidar Abota Tsakanin Sin Da Afirka

July 14, 2026
Nijeriya da Masar Sun Ƙulla Haɗin Gwiwa Domin Yaƙi da Miyagun Ƙwayoyi

Nijeriya da Masar Sun Ƙulla Haɗin Gwiwa Domin Yaƙi da Miyagun Ƙwayoyi

July 14, 2026
CMG Ya Gudanar Da Babban Taron Masu Kirkirar Manyan Shirye-Shirye Da Fina-Finai

CMG Ya Gudanar Da Babban Taron Masu Kirkirar Manyan Shirye-Shirye Da Fina-Finai

July 14, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.