ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, September 11, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ƴan Majalisar ADC Sun Soki Shirin Shugaba Tinubu Na Karɓo Bashin $516m

by Abubakar Sulaiman
5 months ago

Ƙungiyar ‘yan majalisar jam’iyyar ADC ta yi kakkausar suka ga matakin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu na neman amincewar Majalisar Dattawa domin karɓo sabon bashi a ƙasar waje na dala miliyan 516,333,070 don aikin titin Sokoto–Badagry. Bukatar ta fito ne cikin wasiƙar da aka karanta a zauren majalisar ranar Alhamis, inda aka nemi izini bisa tanadin dokar Debt Management Office ta 2011.

Shugaban ƙungiyar, Hon. Uko Ndukwe Nkole, tare da shugabannin yankuna, sun bayyana cewa wannan mataki abin damuwa ne, suna zargin gwamnati da mayar da karɓo bashi wata hanya ta yau da kullum ba tare da la’akari da ɗorewa da jin daɗin al’umma ba. Sun kuma ce duk da muhimmancin ayyukan more rayuwa, ya kamata a fayyace tsadar aiki da sharuɗɗan bashin.

A cewarsu, gwamnatin ba ta gabatar da ingantaccen tsari na biyan bashin ko hujjoji masu gamsarwa kan yadda ake sarrafa basussukan ba. Sun ce Nijeriya na fuskantar nauyin bashi mai yawa, inda biyan bashi ke cin kaso mai tsoka na kuɗaɗen shiga, amma duk da haka ana ci gaba da ƙara zurfafa cikin matsalar tattalin arziƙi.

ADVERTISEMENT

Ƙungiyar ta buƙaci Majalisar Dattawa da kada ta zama ƴar amshin shatan, ya kamata tana neman cikakken bayani kan aiki, da tsarin kashe kuɗi da yadda za a biya bashin.

Haka kuma ta shawarci gwamnati da ta mai da hankali kan manufofin da za su bunƙasa tattalin arziƙi, samar da ayyukan yi da rage asarar kuɗaɗen shiga, tana gargaɗin cewa al’umma za su nemi jin bahasi kan duk wani mataki da zai jefa ƙasar cikin matsalar tattalin arziƙi.

LABARAI MASU NASABA

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

Rashin Mulki Ke Firgita Atiku – Kakakin APC Na Kaduna

Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    Sojoji Sun Ceto Mutane 13 Da ’Yan Bindiga Suka Yi Garkuwa Da Su
  • Abubakar Sulaiman
    Taron BRICS: Shettima Zai Jagoranci Tawagar Nijeriya Zuwa Indiya
  • Abubakar Sulaiman
    Idan Atiku Ya Janye, Za Mu Kula Da Shi Bayan Mun Yi Nasara – Kwankwaso
  • Abubakar Sulaiman
    ASUU Ta Yi Barazanar Shiga Yajin Aiki Na Ƙasa Gaba Ɗaya

MASU ALAKA

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu
Manyan Labarai

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

September 9, 2026
Rashin Mulki Ke Firgita Atiku – Kakakin APC Na Kaduna
Siyasa

Rashin Mulki Ke Firgita Atiku – Kakakin APC Na Kaduna

September 9, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027
Siyasa

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Next Post
Sin Ta Bukaci Amurka Ta Daina Karfafa Abin Da Take Kira “Huldar Diplomassiya” Tsakaninta Da Taiwan

Sin Ta Bukaci Amurka Ta Daina Karfafa Abin Da Take Kira “Huldar Diplomassiya” Tsakaninta Da Taiwan

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Ceto Mutane 13 Da ’Yan Bindiga Suka Yi Garkuwa Da Su

September 11, 2026
Taron BRICS: Shettima Zai Jagoranci Tawagar Nijeriya Zuwa Indiya

Taron BRICS: Shettima Zai Jagoranci Tawagar Nijeriya Zuwa Indiya

September 11, 2026
Mutfwang Ya Buƙaci Sojoji Su Ƙara Ƙaimi A Aikinsu

Gwamnan Shekara na 2026 Gwamna Caleb Manasseh Mutfwang

September 11, 2026

Idan Atiku Ya Janye, Za Mu Kula Da Shi Bayan Mun Yi Nasara – Kwankwaso

September 11, 2026

ASUU Ta Yi Barazanar Shiga Yajin Aiki Na Ƙasa Gaba Ɗaya

September 11, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwarzon Gwamnan Shekarar 2026 Kwamared Nasir Idris

September 11, 2026

Dalilin Da Ya Sa Ba Zan Janye Wa Atiku Ba A Zaɓen 2027 – Peter Obi

September 11, 2026
Farashin Siminti Zai Ragu Idan Farashin Kayan Aiki Ya Sauka – BUA

Gwarzon Shekarar 2026 Abdulsamad Rabiu

September 11, 2026
Cutar Kwalara Na Ci Gaba Da Yi Wa ‘Yan Nijeriya Kisan Mummuƙe

Buƙatar Ɗaukar Matakan Daƙile Yaɗuwar Cutar Mashaƙo A Nijeriya

September 11, 2026
Ding Xuexiang Ya Halarci Taron Kolin CIFTIS Tare Da Ganawa Da Manyan Jami’an Kasashen Waje

Ding Xuexiang Ya Halarci Taron Kolin CIFTIS Tare Da Ganawa Da Manyan Jami’an Kasashen Waje

September 10, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.