ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ɗan Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar Ya Koma APC

by Abubakar Sulaiman
8 months ago
Atiku

Abubakar Atiku Abubakar, ɗan tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, ya sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC mai mulki, inda ya bayyana aniyarsa ta yin aiki domin sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a shekarar 2027.

Ɗan Atikun, Wanda aka fi sani da “Abba”, an tarɓe shi a ranar Alhamis a Majalisar Tarayya da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, tare da manyan shugabannin APC daga shiyyar Arewa maso Gabas.

  • Atiku Ya Fara Neman Mulki Tun Ina NYSC – Datti Baba-Ahmed
  • Barau Ya Gargaɗi Gwamna Abba Kan Siyasantar Da Batun Tsaro A Kano

Da yake sanar da sauya sheƙarsa, Abba ya ce ya yi murabus daga jam’iyyar PDP, ya kuma yanke shawarar shiga APC bisa abin da ya kira kyakkyawan jagoranci da tsare-tsaren gwamnatin Shugaba Tinubu. Ya ce zai yi aiki tare da Sanata Barau domin tabbatar da wa’adin mulki na biyu ga Tinubu a 2027, tare da umartar dukkan mambobin ƙungiyarsa su shiga APC su goyi bayan Ajandar “Renewed Hope”.

ADVERTISEMENT

Ya kuma bayyana cewa ƙungiyarsa ta siyasa da ya kafa a 2022, wato Haske Atiku Organisation, za ta sauya suna nan take zuwa Haske Bola Tinubu Organisation, alamar cikakken daidaituwar manufofin APC gabanin zaɓen 2027. Shugaban APC na ƙasa mai kula da Arewa maso Gabas, Comrade Mustapha Salihu, ya bayyana wannan sauyin sheƙa a matsayin alama mai nuni da  tabbatar ƙasa kyawawan manufofin APC.

A nasa jawabin, Sanata Barau Jibrin ya taya Abba murna bisa matakin da ya kira jarumta da hikima, yana mai cewa ya yanke wannan shawara ne bisa aƙida da imani da manufofin Shugaba Tinubu. Ya ƙara da cewa Abba, wanda ya kasance yana bibiyar siyasar Nijeriya daga Amurka, ya dawo ne domin ba da gudummawa wajen gina makomar ƙasa.

LABARAI MASU NASABA

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi

A ƙarshe, wakilan ƙungiyarsa daga Kano sun tabbatar da cewa za su ƙara zage damtse wajen tallata APC da tabbatar da nasararta a zaɓen 2027.

Atiku
Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    Iyalin El-Rufai Sun Bai Ministan Tsaro Wa’adin Kwana 7 Kan Zargin Rikicin Kudancin Kaduna
  • Abubakar Sulaiman
    Atiku Ya Zargi Gwamnatin Tarayya Da Cin Bashi Kamar Mashayin Da Kuɗi Ya Ƙarewa
  • Abubakar Sulaiman
    Boko Haram Ta Kai Hari Adamawa, Ana Fargabar Mutuwar Mutane 11
  • Abubakar Sulaiman
    Ƴan Bindiga Sun Kai Hari Sokoto, Sun Kashe Mutane 7, Sun Yi Garkuwa Da 12

MASU ALAKA

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027
Siyasa

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi
Manyan Labarai

2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi

September 8, 2026
Atiku
Siyasa

Muna Da Yan Takarar Gwamna A Jihohi 28 Don Shiga Zaben 2027

September 6, 2026
Next Post
Binciken Jin Ra’ayin Jama’a Na Cgtn: Duniya Na Maraba Da Shawarar Sin a Bangaren Inganta Tsarin Shugabancin Duniya

Binciken Jin Ra'ayin Jama'a Na Cgtn: Duniya Na Maraba Da Shawarar Sin a Bangaren Inganta Tsarin Shugabancin Duniya

LABARAI MASU NASABA

Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.