ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

2027: An Fara Fafutukar Neman Ikon Samun Tikitin Takarar Shugaban Ƙasa A ADC

by Leadership Hausa
8 months ago
2027

A halin yanzu dai jam’iyyar haɗaka ta ADC tana cikin wani mawuyacin hali kasancewarta
jam’iyyar da ta samu ƙarɓuwa, wanda ta samu shigowar mayan ƴan adawa gabanin zaɓen
shekarar 2027.

A cikin yanayin sauyin mulki mai matuƙar muhimmanci wanda aka yi masa laƙabi da mai sauya
zaɓe, Peter Obi a ƙarshe ya bayyana cikakken zama mamba na jam’iyyar ADC a ranar 31 ga
Disamba, 2025, wanda ya sauya akalar jam’iyyar zuwa samun nasara ko akasin haka a
matsayinta ta babbar jam’iyyar adawa. Ya bayyana haka ne a Inugu yayin wani taro na
musamman da masu ruwa da tsaki daga kudu maso gabas suka shirya a tsakanin ƴaƴan
jam’iyyar PDP da na LP da kuma na APGA.

  • 2027: Datti Baba-Ahmed Ya Ayana Neman Takarar Shugaban Ƙasa
  • Kasar Sin Ba Ta Amince Kasashen Dake Da Huldar Diplomasiyya Da Ita Su Cimma Yarjejeniya A Hukumance Da Yankin Taiwan Ba

A cikin ƴan watannin da suka gabata, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP a 2023, ya
kasance cikin shakkar bayyana matsayinsa game da zama mamba a ADC. Bayanin nasa a
hukumance ya kawo ƙarshen jita-jita game da aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban ƙasa
zaɓen 2027.

ADVERTISEMENT

Tare da haɗin gwiwar manyan ƴan siyasa irin su tsohon mataimakin shugaban
ƙasa, Atiku Abubakar da Peter Obi da Rotimi Amaechi da Nasir El-Rufai, waɗanda ke da
mabiya masu yawa a yankuna daban-daban a ƙasa baki ɗaya, jam’iyyar ta ƙara samun ƙarfin
iko a halin yanzu. Ta zama wata jam’iyyar da a yanzu haka an fara fafatukar neman ikon
mallakar tikitin takarar shugaban ƙasa tun gabanin jam’iyyar ta ayyan ranar gudanar da zaɓen
fid da gwani.

Al’amarin na nuna yadda jam’iyyar ta tsinci kanta a ciki na cika burin waɗannan
manyan ƴan siyasa da ke da manufar tsayawa takarar shugaban ƙasa.
Yayin da ake ƙoƙarin fara fitar da jaddawalin zaɓen fid da gwani daga wurin kwamitin
gudanarwa na jam’iyyar, Atiku ya bayyana cewa ba zai janye wa wani ɗan takara ba.

LABARAI MASU NASABA

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi

Ko da yake zai cika shekaru 80 a wannan watan Nuwamba, Atiku ya dage kan aniyarsa ta zama
shugaban ƙasa, saboda yana ganin ya kafa hanyoyin kare ƙuri’u a rumfunan zaɓe.
A ɓangare ɗaya kuma, magoya bayan Peter Obi na kallon cewa samun yarjejeniya da za ta kai
ga Atiku ya jaye aniyarsa ta tsayawa takara.

Suna kira da a gudanar da zaɓen fid da gwani a buɗe, inda suke ganin shaharar Obi za ta kai tilasta wa jam’iyyar yin abin da suke so.
Sai dai kuma, a ɓangarorin El-Rufai da Amaechi sun nuna shakku game da lamarin. Suna jin
tsoron gudanar da zaɓen fid da gwani a buɗe ta yadda wanda ya samu ƙuri’u mai yawa zai
samu tikiti, sun fi son a yi yarjejeiya don samun daidaiton buƙatun Arewa da Kudu.
Yanzu haka dai ana tabka muhawara tsakanin masu ruwa da tsaki kan wane zaɓi ne zai
tabbatar da tsari ba tare da rigima ba.

Tunji Shelle, a ra’ayinsa, yana ganin cewa zaɓin wakilai ne zai fi dacewa da buƙatun jam’iyya. Ya ci gaba da lissafa wasu muhimman abubuwa da za su yanke shawara kan wanda zai samu tikitin.
Ya ce, “Dukkaninsu (Atiku da Obi) sun yarda cewa duk wanda ya samu tikitin za a goyi
bayansa. Kowa zai rungumi wannan mutum. Abin da zai faru shi ne, wakilai za su fito su jefa ƙuri’a. Dukkaninsu sun yarda da dimokuraɗiyya, za su shiga zaɓen fid da kuma duk wanda ya
samu nasara zai samu goyo baya.

“Shugabanci nagari ne zai tabbatar da yanayin mai kyau wajen amincewa da junansu. Ba na
son a yi tunanin janyewa juna. Idan dai ba sa yarda su janye wa juna ba, tabbas za a yi zaɓen
fitar da gwani kuma duk wanda ya ci zai kasance ɗan takaran shugaban ƙasa. Dole ne wani ya
amince da rashin nasara a ƙarshe. Burina shi ne su kasace sun yi aiki tare. Daidaita buƙatun
ƙasa ta fi na mutum ɗaya.”

A halin yanzu, shugabancin Daɓid Mark na fuskantar wani yanayi na shari’a, saboda rikicin cikin
gida da ƙalubale a kotu. Wasu mambobin jam’iyya sun kai kara kotun tarayya a Abuja, suna
ƙalubalantar sahihancin shugabancin wucin gadi na jam’iyyar, suna nuni cewa an saɓa wa
kundin tsarin mulki wajen yin naɗin.

Masu ƙara suna nuna jayayya da naɗin Mark da Aregbesola, da Abdullahi domin naɗinsu ya
saɓa wa tsarin mulkin jam’iyyar. Suna nema kotu ta soke naɗin da hana hukumar zaɓe mai
zaman kanta ta ƙasa (INEC) yarda da jami’an wucin gadi. Rigimar ta nuna matsaloli masu zurfi
a cikin jam’iyyar, inda wasu mambobi ke adawa da burin takarar shugabancin ƙasa na Atiku
Abubakar a jam’iyar.

Duk da cewa INEC ta amince da jagorancin Daɓid Mark a hukumance, wasu ɓangarori a cikin
jam’iyyar, ciki har da masu goyon bayan tsohon shugaban Ralph Nwosu, sun ƙalubalanci
halarcin sabon kwamitin gudanarwa na jam’iyyar da ke goyon bayan haɗin gwiwa. Kowace
hukunci da shugabanci ke yanke a halin yanzu ana duba ta sosai don ganin ko tana karkata
zuwa ga Atiku ko Obi.

A yanayin siyasa a halin yanzu, ADC na cikin wani mawuyacin hali. Duk da cewa jam’iyyar ta
samu nasarar samun haɗin gwiwar mayan ƴan siyasa da ke adawa da Shugaban ƙasa Bola
Ahmed Tinubu, rashin iya kawo ƙarshen rarrabuwar kai da ke tsakanin ɓangaren magoya baya
Atiku da kuma Obi iya jefa jam’iyyar cikin haɗari.

2027
Leadership Hausa
Website |  + postsBio
  • Leadership Hausa
    Karuwar Farin Jinin Gwamna Umaru Bago A Siyasar Jihar Neja
  • Leadership Hausa
    Kyakkyawan Tsarin Laken Asiri Zai Dakile Shirin Magudin Zabe A Nijeriya —Mohammed
  • Leadership Hausa
    Batun Dawo Da Tallafin Mai Da Atiku Ya Yi Na Ci Gaba Da Tayar Da Kura
  • Leadership Hausa
    Batun Guguwar Kakar Yakin Neman Zabukan 2027 A Nijeriya

MASU ALAKA

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027
Siyasa

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi
Manyan Labarai

2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi

September 8, 2026
2027
Siyasa

Muna Da Yan Takarar Gwamna A Jihohi 28 Don Shiga Zaben 2027

September 6, 2026
Next Post
2027

Ana Ci Gaba Da Allah-wadai Da Harin Da Aka Kai Wa Kasuwar Hausawa A Edo

LABARAI MASU NASABA

Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.