Shugaban kasar Sin, Xi Jinping, ya isa birnin Bishkek a yau Lahadi domin halartar taron kolin Kungiyar Hadin Gwiwa ta Shanghai (SCO) na shekarar 2026, da kuma gudanar da ziyarar aiki a kasar Kyrgyzstan. Shugaban kasar Kyrgyzstan, Sadyr Japarov, da uwargidansa sun tarbi shugaba Xi Jinping da uwargidansa, Peng Liyuan, a filin jirgin saman kasa da kasa na Manas, a yau Lahadi. Shugaba Xi ya gabatar da sako a rubuce, a madadin gwamnati da al'ummar kasar Sin, inda ya mika kyakkyawar gaisuwa da fatan alheri ga shugaba Sadyr Japarov da al'ummar kasar Kyrgyzstan. Xi ya bayyana cewa, dangantakar abota tsakanin Sin da Kyrgyzstan tana da dogon tarihi da zamani mai alfanu, kuma tsaunukan Tianshan sun shaida musayar zumunta mai danko tsakanin al'ummomin biyu a tsawon dubban shekaru. Kazalika, tun bayan kulla huldar diflomasiyya shekaru 34 da suka gabata, dangantakar Sin da Kyrgyzstan ta tsallaka siradin sauye-sauyen siyasar duniya, tare da samun ci gaba mai inganci ba tare da tangarda ba, har ta kai matsayin hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare na matakin koli a sabon zamani. Shugaba Xi ya kara da cewa, a yayin wannan ziyara, zan yi cikakkiyar tattaunawa da shugaba Japarov kan dangantakar Sin da Kyrgyzstan, da hadin gwiwa a fannoni daban-daban, da kuma batutuwan kasa da kasa da na shiyya-shiyya kan muradun juna, domin tsara sabon shirin gina al'ummar Sin da Kyrgyzstan mai kyakkyawar makoma ta bai-daya. Ina fatan halartar taron kolin kungiyar SCO da za a gudanar a Bishkek, tare da yin aiki da dukkan bangarori don karfafa samun ci gaba mai dorewa ga Kungiyar Hadin Gwiwa ta Shanghai. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Read moreDetailsA yayin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ke halartar taron koli...
Read moreDetailsAna ci gaba da aiwatar da shirin tallafin da Sin ta ware...
Read moreDetailsDa safiyar ranar 26 ga watan nan da muke ciki, an samu abkuwar mummunan ibtila’in zabtarewar kasa a bangaren kasar Nepal mai makwabtaka da kasar Sin, lamarin da ya janyo babbar hasarar rayuka gami da bacewar wasu mutane da dama a gundumar Gyirong ta birnin Xigaze na jihar Xizang mai cin gashin kanta ta kasar Sin, wato yankin kan iyakokin Sin da Nepal. A yau Lahadi kuma an yi wani taron manema labarai a Gyirong dangane da ibtila’in, inda aka bayyana cewa, bayan abkuwarsa, an dauki matakan shawo kansa ba tare da bata lokaci ba a Xizang, inda aka kafa babban sashin kula da ayyukan ba da agajin gaggawa gami da wani sashin kula da agajin gaggawa da ke can yankin da ibtila’in ya ritsa da shi. Ma’aikatar kudi, da ma’aikatar shawo kan al’amuran ba-zata ta kasar Sin, sun ware kudin Sin Yuan miliyan 120, kana, kwamitin samar da ci gaba da yin gyare-gyare a gida na kasar ya ware Yuan miliyan 100, a wani kokari na tallafa wa ayyukan ba da agaji da ceto da kuma farfado da yankin da ibtila’in ya shafa. Kawo yanzu, an riga an tura ma’aikata 2141 na bangarori daban-daban domin bayar da agajin gaggawa a wurin, ciki har da na rundunar ’yantar da jama’ar kasar Sin, da ’yan sanda masu dauke da makamai, da tawagar ’yan kwana-kwana masu kai dauki da sauransu, gami da motocin agaji guda 269, hade da na’urorin kai dauki 3922. Zuwa karfe 6 na yammacin ranar 29 ga watan muke ciki, yawan mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon ibtila’in ya kai 16, yayin da wasu 546 suka bace. (Murtala Zhang)
Read moreDetailsA yayin da shugaban kasar Sin Xi Jinping zai kai ziyarar aiki...
Read moreDetailsJirage mara matuka na shawagi a sama domin nazarin yanayi, yayin da...
Read moreDetailsMasu bincike na kasar Sin sun kammala gwajin sadarwa tsakanin duniyar dan...
Read moreDetailsDaga ranar 31 ga watan Agustan da muke ciki zuwa ranar 1...
Read moreDetailsKasar Sin ta mika aikin gyara da fadada asibitin Masaka na Rwanda ga hukumomin kasar, yayin wani biki da ya gudana jiya Juma’a a babban birnin Kigali. Aikin wanda Sin ta bayar da tallafin gudanar da shi, shi ne aikin tallafi mafi girma da gwamnatin Sin ta gudanar a Rwanda, kuma wani muhimmin aiki na inganta rayuwa da ke karkashin shawarar Ziri Daya da Hanya Daya. Biyo bayan gyara da fadada asibitin, girmansa ya karu daga murabba’in mita 6,398 zuwa murabba’in mita 56,957, yayin da adadin gadaje ya karu sosai daga 127 zuwa 837. An kuma samu karuwar adadin marasa lafiya da asibitin zai iya karba a kullum zuwa 2,000. Da yake jawabi yayin bikin, ministan lafiya na kasar Sabin Nsanzimana, ya ce wannan wani gagagrumin ci gaba ne ga kasar da kuma bangaren kiwon lafiya. Ya ce suna sa ran wannan asibiti zai zama alama ta ingantacciyar kiwon lafiya da za su iya samarwa a Rwanda da nahiyar Afrika. Kuma suna sa ran ci gaba da hada hannu da Sin don ganin hadin gwiwar ta fadada a bangaren kiwon lafiya. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
Read moreDetailsKafin ziyarar aiki a Masar da shugaban Sin Xi Jinping zai yi,...
Read moreDetails© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.
© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.