Yau Alhamis da rana, firaministan kasar Sin Li Qiang ya isa garin Gyirong da ke yankin Xizang mai cin gashin kansa na kudu maso yammacin kasar Sin, bayan mummunar zaftarewar laka ta afkawa garin da jiya safiyar Laraba, agogon kasar Sin. Li, wanda kuma memba ne na zaunannen kwamitin ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, ya tafi wurin ne bisa umarnin Xi Jinping, babban sakataren kwamitin tsakiya na jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, don ya jagoranci wata tawagar manyan jami'ai daga mabambantan hukumomi masu ruwa da tsaki, zuwa yankin da bala'in ya shafa. Wadannan jami'ai za su sanya ido kan ayyukan ceto da agaji, sannan za su ziyarci wurare daban daban don ganawa da ma'aikatan ceto da masu ba da agaji, da kuma mutanen da bala'in ya ritsa da su. (Bello Wang)
Read moreDetailsYau 26 ga watan Agusta, ofishin yada labarai na majalisar gudanarwa ta...
Read moreDetailsYayin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ke gab da halartar taron...
Read moreDetailsGasar wasannin motsa jiki ta mutum-mutumin inji masu siffar dan Adam ta duniya karo na...
Read moreDetailsBisa shirin ci gaban kasa da kyautata jin dadin zamantakewar al’umma na...
Read moreDetailsKakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ya sanar da cewa, daga ranar...
Read moreDetailsYau Laraba, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin, Lin Jian ya jagoranci wani...
Read moreDetailsShugaban kasar Sin Xi Jinping, ya bayar da umarnin a yi dukkan...
Read moreDetailsA yau Talata ne kasar Sin ta yi nasarar harba sabbin taurarin...
Read moreDetailsAbin da ci gaban Sin ya kawo ba barazana ba ce, sai...
Read moreDetails© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.
© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.