Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunan Murtala Sule Garo ga Majalisar Dokokin Jihar domin tantancewa da amincewa da shi a matsayin sabon mataimakin gwamna. An bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da Sakataren yaɗa labaran gwamnan, Mustapha Muhammad, ya fitar a daren ranar Talata.
Sanarwar ta ce naɗin ya yi daidai da sashi na 191(3) na Kundin Tsarin Mulki na 1999 (wanda aka gyara), wanda ke bai wa gwamna damar naɗa mataimaki idan gurbi ya samu. Rahotanni sun nuna cewa kujerar ta samu ne bayan murabus ɗin Comrade Abdussalam Gwarzo a ranar 27 ga Maris, 2026.
- Sojoji Sun Ceto Fasinjoji Uku Da ‘Yan Bindiga Suka Harba A Filato
- Xi Zai Halarci Taron BRICS Karo Na 18 A Indiya
- Rodri Ya Nemi Afuwar Valencia Dangane Da Kalaman Da Yayi Akanta
- Za A Gudanar Da Taron Koli Na Shugabannin Harkokin Masana’antu Da Cinikayya Na APEC Na 2026 A Shenzhen
- Amurka Ta Bai Wa Nijeriya Sabbin Kayan Yaƙi Domin Yaƙi Da Ta’addanci
Haka kuma sanarwar ta bayyana cewa bayan tuntuɓa mai zurfi da masu ruwa da tsaki, gwamnan ya buƙaci majalisar da ta amince da naɗin Garo domin cike gurbin. An ce matakin na daga cikin ƙoƙarin tabbatar da ci gaba da tafiyar da gwamnati cikin tsari.
Garo mai shekaru 48 gogaggen ɗan siyasa ne wanda ya shafe sama da shekaru ashirin yana riƙe mukamai daban-daban na gwamnati da jam’iyya.
Ya taɓa zama sakataren tsare-tsare na jam’iyyarsa, mai ba gwamna shawara, shugaban ƙaramar hukumar Kabo, sannan ya riƙe muƙamin shugaban ALGON a Kano da kuma kwamishinan ƙananan hukumomi da masarautu, tare da kasancewa ɗan takarar mataimakin gwamna na APC a zaben 2023.














