Ministan Wutar Lantarki, Adebayo Adelabu, ya samu amincewar Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu, kan shirin yin murabus daga muƙaminsa domin neman kujerar gwamna a jihar Oyo, kuma ana sa ran zai ajiye aiki nan ba da jimawa ba.
Mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai, Tunji Bolaji, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba.
- Sin Ta Nuna Rashin Jin Dadinta Ga Italiya Da Tarayyar Turai Kan Ziyarar Jami’ar DPP
- Sin Tana Son Cin Moriya Tare Da Sassan Duniya A Fannin Kirkire-kirkire
- Sin Da Indiya Na Shirye-shiryen Ganawar Xi Da Modi
- Hadin Gwiwar Hada-Hadar Ba Da Hidima Tsakanin Sin Da Afirka Na Karfafa Karfin Afirka
- Dalilan Da Ya Sa Jam’iyyun Siyasa Suka Jinkirta Ƙaddamar Da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen
Bolaji ya ce lokacin murabus ɗin na nuna yadda ministan ke son kammala muhimman ayyuka a ɓangaren lantarki kafin barin ofis, ciki har da ƙoƙarin daidaita samar da wuta bayan raguwar da aka samu sakamakon ƙarancin iskar gas, gyaran bututun mai da kuma bashin da ake bin masu samar da gas.
Ya ƙara da cewa yayin ganawarsa da Shugaba Tinubu a Fadar Shugaban Ƙasar da ke Abuja ranar Talata, Adelabu ya gabatar da cikakken rahoto kan ayyukan da ya gudanar cikin shekaru biyu da rabi, ciki har da ƙoƙarin inganta samar da wutar lantarki, ƙarfafa hanyoyin isar da ita da kuma aiwatar da gyare-gyare a ɓangaren.
Haka kuma ya gabatar da manufofi kamar National Integrated Electricity Policy (NIEP) da tsare-tsaren aiwatar da ita, wanda ke nufin tabbatar da ɗorewar ɓangaren lantarki, da faɗaɗa samun wuta da kuma inganta tsarin gaba ɗaya. Shugaba Tinubu ya yaba da ƙoƙarin ministan da nasarorin da aka samu, musamman wajen kafa tubalin manufofi domin sauya fasalin ɓangaren wutar lantarki.














